Yadda wata cutar shanu ta yi sanadin mutuwar mutum a karon farko a duniya

    • Marubuci, Maia Davies
    • Marubuci, Michelle Roberts
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, digital health editor
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 3

Mahukunta a ƙasar Faransa sun ce a karon farko masana kimiyya sun gano wani mutum da ya mutu a farkon wannan wata na Oktoba bayan kamuwa da wata cuta mai suna Shamonda da ake kira Shav a taƙaice.

Jami'an kiyyon lafiyar ƙasar sun bayyana cewa lamarin wani yanayi ne na musamman da kan shafi majiyyaci "mai matuƙar raunin garkuwar jiki".

Sun kuma jaddada cewa, a halin yanzu, babu wata barazana ga lafiyar jama'a sakamakon wannan lamari.

Shav cuta ce da ta fi shafar shanu, wadda ake iya yaɗa ta ta hanyar ƙananan ƙwari masu shan jini da aka sani da midges.

An kuma samu ɓullar cutar a tumaki da awaki da raƙuman yankin alpaca da kum dawaki.

Sai dai kafin yanzu, ba a taɓa samun rahoton kamuwa da cutar a jikin ɗan Adam ba.

Cibiyar Yaƙi da Cutuka masu Yɗuwa ta Turai ta (ECDC) ta ce tana sa ido kan lamarin, yayin da jami'ai ke ci gaba da gudanar da bincike domin gano yadda aka yi har ƙwayar cutar ta yaɗu zuwa jikin ɗan Adam.

Ana zargin cewa majiyyacin da ya kamu da cutar Shamonda ya kamu da ita ne sakamakon cizon wani ƙwaro mai yaɗa cutar a gabashin Faransa, a cewar ma'aikatun lafiya da noma na ƙasar a ranar Alhamis. A wannan yanki ne aka fara gano cutar a cikin dabbobi tun lokacin bazara.

Ma'aikatun sun bayyana cewa ana kula da majiyyacin, wanda ke fama da wata matsananciyar rashin lafiya, a wani asibiti da ke birnin Lyon. Sun ce majiyyacin ya fuskanci matsalolin jijiyoyin ƙwaƙwalwa, waɗanda binciken farko ya nuna cewa akwai yiwuwar suna da alaƙa da ƙwayar cutar.

Sanarwar ta jaddada cewa majiyyacin na da raunin garkuwar jiki, lamarin da ya sa ya fi fuskantar barazanar kamuwa da cututtuka.

"Har zuwa yanzu, ana ɗaukar ƙwayar cutar Shamonda a matsayin wadda ba ta yaɗuwa zuwa ga mutane," in ji sanarwar.

Ta ƙara da cewa, duk da cewa cutar ta daɗe tana yaɗuwa a Afirka da Asiya tsawon shekaru, ba a taɓa gano ta a jikin ɗan Adam ba kafin aukuwar wannan lamari.

Cutar Shamonda na iya shafar garken shanun da ke samar da madara, inda take haddasa zazzaɓi da gudawa da raguwar samar da madara bayan dabbobin sun kamu da ita ta hanyar cizon ƙwari.

Cibiyar Yaƙi da d Cutuka masu Yɗuwa ta Turai ta (ECDC) ta ce tana aiki tare da hukumomin Faransa da sauran abokan hulɗarta a ƙasashen na urai domin gudanar da bincike kan irin illar da wannan cuta ke da ga lafiyar jama'a.

A cewar cibiyar, an fara gano bullar cutar Shamonda a Turai ne a ƙarshen watan Yuli. Kuma tun daga lokacin, an gano cutar a dabbobin gona a ƙasashe da dama, ciki har da Ireland da Jamus da Italiya da Spain da kuma tsibirin Jersey.

An kuma sanar da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) game da wannan lamari.