Manchester United na harin Howe, Arsenal na zawarcin Baena

Eddie Howe
Bayanan hoto, Eddie Howe
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Daraktan bayar da shawarwari na Manchester United Jason Wilcox ya nuna cewar, ya fi son su ɗauko tsohon mai horar da ƴan wasan Newcastle United Eddie Howe, inda har suka sallami Michael Carrick. (Talksport)

Haka kuma Manchester United na sake duba yiwuwar ko zata ɗauko Julian Nagelsmann idan suka yi hannun riga da Carrick, biyo bayan da tsohon mai horara da ƴan wasan Bayern Munich ɗin ke nuna son komawa United ɗin. (Telegraph - subscription required)

Har ila yau dai mai horra da ƴan wasan Aston Villa Unai Emery shi ma na cikin waɗan da Manchester United ke fatan ganin ya maye gurbin Carrick. (i news)

Manchester United ta fara tattaunwa da tsohon mai horar da ƴan wasan Chelsea da Tottenham Antonio Conte don ganin ya koma gasar Firimiya. (La Repubblica - in Italian)

Manchester United na son ganin ta ajiye tarihi wajen biyan kuɗaɗe masu yawa wajen ganin sun ɗauko Fabian Hurzeler daga Brighton a matsayin wanda zai maye gurbin Carrick. (Telegraph - subscription required)

Sai dai kuma , Hurzeler ba shi da sha'awar komawa Manchester United ɗin, idan har kwantaraginsa da Brighton ɗin ya ƙare. (Talksport)

Arsenal na zawarcin ɗan wasan Atletico Madrid Alex Baena, inda ta ke son ɗaukar sa a watan Janairu. (FootballTransfers)

Arsenal na sa ido kan ɗan wasan Monza Gustavo Varela, yayin da Napoli da Benfica su ma ke harin ɗan wasan. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Bayer Leverkusen na son Gleison Bremer idan ya yanke shawarar barin Juventus a watan Janairu. (Gazzetta dello Sport - in Italian)