'Yandambe da gasar kyau ta zabiya cikin ƙayatattun hotunan Afirka na mako

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Ƙayatattun hotunan Afirka da na ƴan nahiyar a wasu sassan duniya na wannan makon

Wasu 'yandambe ne a nan suke gwambzawa
Bayanan hoto, A ranar Juma'a ne aka gwabza dambe a gasar African Warrior Dambe World Series, a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja - wasan dambe yana da daɗaɗɗen tarihi a arewacin Najeriya da ma sauran maƙwabtanta irin su Nijar
Dandambe a tsaye
Bayanan hoto, A wannan rana ta Juma'a ne dai a Abuja, Faisal Ibrahim da ake yi wa laƙabi da Dan Yellow Tula yake nuna jaruntarsa ko da wanda zai tare shi su gwambza
Masu wasan linƙaya a ruwa
Bayanan hoto, Yayin da ake shirin shiga yanayin zafi mai tsanani nan wasu matasa ne suke wanka a teku a babban birnin Tunisia, Tunis ranar Talata.
Wata yarinya da balan-balan
Bayanan hoto, Wasu yara kenan a Abuja suna zabar balan-balan a wajen wasa na Magic Land.
Wasu mata a wajen shakatawa da wasa na Magic Land wanda aka buɗe wajen shekara 20 da ta wuce a Abuja
Bayanan hoto, Wasu mata a wajen shakatawa da wasa na Magic Land wanda aka buɗe wajen shekara 20 da ta wuce a Abuja
Masu shiga gasar kyau ta maza da mata zabiya ta Afirka a Zimbabwe na shiri a Zimbabwe ranar Asabar
Bayanan hoto, Masu shiga gasar kyau ta maza da mata zabiya ta Afirka a Zimbabwe na shiri a Zimbabwe ranar Asabar
'Yar wasan Tunisia kenan Ons Jabeur a rana ta farko ta babbar gasar tennis ta Ingila - Wimbledon a Birtaniya ranar Litinin.
Bayanan hoto, 'Yar wasan Tunisia kenan Ons Jabeur a rana ta farko ta babbar gasar tennis ta Ingila - Wimbledon a Birtaniya ranar Litinin
Wani mai sayar da kankana a wajen hajarsa
Bayanan hoto, Wani mai kankana kenan ya kasa yana jiran masu saye a garin Nakuru na Kenya ranar Laraba. Farashin kayan abinci na ci gaba da tashi yayin da kasar ke fama da tsadar rayuwa.
Mawaki Rema kenan ɗan Najeriya da tawagarsa lokacin da suka hallara a bikin kayan ado na Jacquemus a birnin Paris, Faransa.
Bayanan hoto, Mawaki Rema kenan dan Najeriya da tawagarsa lokacin da suka hallara a bikin kayan ado na Jacquemus a birnin Paris, Faransa, ranar Lahadi.
Wasu masu rakashewa kenan a bikin watan masu neman jinsi ɗaya (Pride Month) a Lagos suke cashewa a ranar Asabar
Bayanan hoto, Wasu masu raƙashewa kenan a bikin watan masu neman jinsi daya (Pride Month) a Lagos suke cashewa ranar Asabar
Fitacciyar mawakiyar Afirka ta Kudu, Thandiswa Mazwai, na wasa zauren kaɗe-kaɗe da sauran wasanni na Johannesburg Lyric Theatre, ranar Lahadi
Bayanan hoto, Fitacciyar mawaƙiyar Afirka ta Kudu, Thandiswa Mazwai, na wasa zauren kaɗe-kaɗe da sauran wasanni na Johannesburg Lyric Theatre, ranar Lahadi.
A ranar Litinin masu wasan sulun teku daga sassan duniya suka shiga gasar ƙwararru ta Ballito a gabar gabashi ta KwaZulu-Natal da ke Afirka ta Kudu.
Bayanan hoto, A ranar Litinin masu wasan sulun teku daga sassan duniya suka shiga gasar ƙwararru ta Ballito a gabar gabashi ta KwaZulu-Natal da ke Afirka ta Kudu.