Zaɓaɓɓun hotunan abubuwan da suka faru a Afirka daga 26 ga Fabrairu zuwa 4 ga Maris 2021

An wallafa

Ga wasu zaɓaɓɓun hotunan wasu abubuwan da suka faru a Afirka daga 26 ga Fabrairu zuwa 4 ga Maris 2021:

A family watch a movie screening at the Sudanese European Film Festival.
Bayanan hoto, Wasu iyalai ƴan Sudan suna cikin nishaɗi a yayin da suke hanyar zuwa wani baje-kolin fina-finai a Khartoum ranar Lahadi.
Egyptian skateboarders look on at the start of the competition.
Bayanan hoto, Washe gari kuma a birnin Alƙahira wasu masu wasan zamiya sun shiga wata gasa ta Red Bull Mind a Masar.
Men from the Kenyan Maasai tribe jump in unison during the rites.
Bayanan hoto, A wannan ranar kuma a yankin Narok na Kenya, matsana ƙabilar Masai suna gudanar da wata al'ada don su zama moran - wato mazan da za su zama gwarazan al'ummar.
Girls stand on the rocks looking at a magazine.
Bayanan hoto, Yara masu talla na kallon mujalla a kusa da wata ƙorama yayin da suka dan tsaya hutawa a Dakar, babban birnin Senegal.
A supporter of opposition leader Ousmane Sonko hurls stones during clashes with security forces.
Bayanan hoto, A ranar Laraba a Dakar ɗin, magoya bayan ɗan hamayyar da ke takara da shugaban kasa Ousmane Sonko suna fito na fito da dakarun tsaro. An zargi Mr Sonko da aikata fyaɗe sannan aka ɗage masa kariyar da yake da ita ta ɗan majalisa. Sai dai ya musanta tuhumar.
A Sahrawi woman soldier holds a gun. She has henna-dyed patterns on her hands.
Bayanan hoto, A ranar Asabar wata soja ƴar ƙasar Saharawi ta yi lalle a hannunta tana yin fareti...
Sahrawi women perform a dance in the parade. They are fully clothed in red.
Bayanan hoto, Lamarin ya faru ne a wani sansanin ƴan gudun hijira a wajen garin Tindouf, da ke Algeria. Shekara 45 kenan da aka ayyana yankin Larabawa na Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Sahrawida ka fi sani da Western Sahara a matsayin mai cin gashin kanta...
Sahrawi women perform a dance in the parade. Their faces are painted white.
Bayanan hoto, Cikakkiyar mamba ce ta Ƙungiyar Tarayyar Afirka amma gwamnatocin ƙasashen duniya ba su amince da ita ba. Yawancin yankunanta suna ƙarƙashin ikon Moroko ne, wadda ke ikirarin suna cikin ikonta.
A man is seen riding a horse. Bother are wearing green, yellow and red colours for their symbolism.
Bayanan hoto, A ranar Talata a birnin Addis Ababa, wani mutum yana sukuwa a kan dokinsa a wajen bikin tunawa da yaƙin Adwa da aka yi a 1896, inda Habasha ta yi nasara a kan dakarun Italiya.
A giraffe crosses a road laced with an electric fences.
Bayanan hoto, Sannan kuma a ranar Laraba, motoci na jira cikin ƙosawa wani raƙumin dawa ya tsallaka titi kafin su wuce, a Kimana da ke Kenya.

Dukkan hotunan suna da haƙƙn mallaka.