Shugabannin duniya na maraba da nasarar Demokrats
Ba abin mamaki ba ne ganin cewa wasu shugabannin ƙasashen da Donald Trump ya taɓa suka ko nuna adawa da su na maraba da gagarumar nasarar da jam'iyyar Democrat ta samu a zaɓen rabin wa'adi.
- Firaministan Sifaniya, mai ra'ayin sassauci, Pedro Sanchez, ya ce Amurkawa sun zaɓi kawar da ƙiyayya, musun sauyin yanayi da kuma fifita masu gata a cikin al'umma.
- Shi ma takwaransa Jonas Støre, firaministan ƙasar Norway, wadda Trump ya soko a makonnin baya saboda ba ta ba shi lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel ba, ya ce wasu sabbin muryoyi na tasowa a Amurka waɗanda suka fi dacewa da manufofin birnin Oslo.
- Shugaban ƙasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, wanda Trump ya zarga da aikata kisan kare dangi kan fararen fata, ya ce zaɓukan za su kawo sabon zamani a dangantakar ƙasashen duniya.
- A wani ɓangaren kuma, mataimakiyar shugabar Majalisar Tarayyar Turai, Christel Schaldemose, ta ce tana da fata cikin taka-tsantsan cewa sakamakon zaɓen na iya haifar da ƙarin goyon baya ga Ukraine.