Babban jami’in gudanarwa na Manchester United, Omar Berrada da daraktan kwallon kafa, Jason Wilcox suna Carrington, domin tattauna makomar babban koci, Michael Carrick wanda ke fuskantar matsin lamba.
Shahararren tsohon ɗan wasan Red Devils ya fara aiki a bara a karo na biyu, inda ya mayar da kungiyar kan ganiya da samun gurbin Champions League tun bayan da ya maye gurbin Ruben Amorim da aka sallama.
A lokacin da ya karbi aikin rikon kwarya United tana can kasar teburi, amma tun daga Janairu ya saita komai ta dunga cin wasanni da ta kai ta kare a mataki na ukun teburi a gasar Premier League.
Nasarorin da Carrick ya samu ne suka sa aka ba shi sabon kwantiragi na shekaru biyu, domin ci gaba da zama kocin United, amma watanni biyar kacal tsakani, sai fuskantar barazanar sallama yake yi, bayan rashin nasarar a gida a hannun Bournemouth da ci 3-0 a Old Trafford ranar Lahadi.
An fahimci cewa tattaunawa kan batun kocin ta fara ne, bayan wannan rashin nasarar kuma ta ci gaba bayan da Berrada da Wilcox suka isa cibiyar horaswa ta Carrington a safiyar Litinin.
Eddie Howe da Julian Nagelsmann na daga cikin waɗanda ake ganin za su iya maye gurbin Carrick, wanda ya ja ragamar takwas ba tare da samun nasara ba, bayan shan kashi a hannun Bournemouth kwanaki kadan bayan rashin nasarar 4-1 da suka yi a hannun Como a Gasar Zakarun Turai.
United ta yi nasara biyu kacal cikin wasanni 12 da ta buga a dukkan fafatawa a wannan kakar, kuma maki bakwai da ta samu daga wasanni takwas shi ne mafi muni da ta taba fara kakar wasa tun bayan shekarar 1986.
Kungiyar tana matsayi na 16 a teburin Premier League, maki daya kacal tsakaninta da yankin faduwa daga gasar, kuma za ta je gidan Chelsea ranar Asabar. Daga nan kuma za ta shiga hutun wasannin kasa da kasa bayan karbar bakuncin Roma da Aston Villa.
Carrick ya kauce wa tambayoyi kan makomarsa bayan rashin nasarar da Bournemouth, amma ya yi kama da wanda ya fahimci abin da ke tafe yayin da yake daga hannu ga magoya baya tare da dafa kirjinsa lokacin da yake barin filin wasa, yayin da magoya bayan ke rera sunansa cikin goyon baya.
Fushin magoya bayan Old Trafford ya fi karkata ne ga iyalan Glazer da Sir Jim Ratcliffe da tsarin Ineos, ciki har da daraktan kwallon kafa na United, Wilcox.
An yi wa ’yan wasan ihu lokacin da aka tashi wasan Bournemouth, sannan aka sake yi musu ihun, yayin da suka bi Carrick zuwa dakin hutuwar ’yan wasa a ranar da kocin ya ajiye kyaftin Bruno Fernandes a benci.
Dan wasan mai shekaru 32 ya gaza kaiwa ganiyar da ya nuna a kakar da ta gabata lokacin da ya lashe kyaututtukan PFA da FWA, inda kyaftin din ya kalubalanci Carrick kan dabarun da ya yi amfani da su, bayan rashin nasarar a hannun Como a tsakiyar mako.