Gwaji ya nuna cewa ba a samu sababbin waɗanda suka kamu da Ebola a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kula da cututtuka masu yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta ce gwaje-gwajen ɗakin gwaji da aka gudanar kan samfurorin mutum biyu da ake zargin sun kamu da cutar Ebola a jihar Adamawa sun nuna sakamakon da ke tabbatar da cewa babu wanda ya kamu da cutar a jihar.
Sanarwar da hukumar ta fitar a daren Asabar ta biyo bayan wani gargaɗi da ta bayar tun farko game da gano wasu mutane biyu da ake zargin suna ɗauke da cutar a Yola, babban birnin jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Babban daraktan NCDC, Dkta Jide Idris, ya ce hukumomin lafiya na jihar sun samu rahoto a ranar Juma’a bayan gano wasu mutane biyu da ke nuna alamomin da suka yi kama da na Ebola. Wannan ya sa aka killace su tare da fara daukar matakan da suka dace.
“An tattara samfurori domin gudanar da gwaje-gwajen ɗakin gwaji don gano haƙiƙanin cutar da ke damun su. Abin farin ciki, sakamakon gwaje-gwajen sau biyu da aka yi ya nuna cewa ba su ɗauke da cutar Ebola,” in ji Dokta Jide.
A halin yanzu, hukumomi na kira ga jama’a da su guji yaɗa jita-jita ko hasashe marasa tushe game da yaɗuwar cutar.















