Akalla mutum 15 sun mutu bayan motar sojoji ta taka nakiya a Borno

Asalin hoton, Getty Images
Aƙalla mutane 15 ne suka mutu, ciki har da sojojin Najeriya 10 da mambobi biyar na rundunar sa-kai ta fararen hula (CJTF), bayan da wata motar sojoji ta taka nakiya a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Lamarin ya faru ne ranar Asabar yayin da sojojin wata bataliya da ke Gamboru ke sintiri a kan hanyar da ta haɗa Gamboru da Ngala kusa da iyakar Najeriya da Kamaru.
Rahotanni sun nuna cewa nakiyar da motar ta taka ana zargin mayaƙan Boko Haram ne suka binne ta a kan hanyar. Fashewar ta kashe sojoji takwas nan take.
Bayan fashewar, wasu mahara sun buɗe wuta kan wata mota ta biyu da ke cikin ayarin, inda suka kashe ƙarin sojoji biyu da kuma mambobi biyar na rundunar CJTF, wadda ke taimakawa sojoji a yaƙi da ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi.
An kuma kai sojoji shida da suka jikkata zuwa Asibitin Sojoji na Maimalari da ke Maiduguri domin samun kulawar likitoci.
Har zuwa lokacin da aka haɗa wannan rahoto, rundunar sojin Najeriya ba ta fitar da wata sanarwa mai alaka da bayanan harin ba.
Babu kuma wata ƙungiya mai zaman kanta da ta tabbatar da adadin mamatan da aka ruwaito.
Masana tsaro na ganin harin na nuna cewa ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP na ci gaba da kasancewa barazana a yankin duk da hare-haren da sojojin Najeriya ke kai musu.
Tashin hankalin da ya fara a arewa maso gabashin Najeriya tun shekarar 2009 ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane tare da raba miliyoyin mutane da muhallansu a Najeriya da yankin Tafkin Chadi.































