Yadda a baya ban yi APC ba yanzu ma ba zan yi ba - Lamido

Asalin hoton, Mansur Ahmed/FB
Tsohon gwamnan jihar Jigawa, kuma jigo a jam'iyyar hamayya ta PDP, Alhaji Sule Lamido ya nesanta kansa da kalaman da mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya yi a kansa.
A lokacin da yake jawabi a taron yaƙin nema a Dutse, babban birnin jihar ranar Talata, Kashim Shettima ya Sule Lamido na tare da APC.
''Wai ina ana magar Jigawa, su wane ne Jigawa?, ga mu nan muna tare da Saminu Turaki da Ali Sa'adu B/Kudu da Muhammad Badaru Abubakar, dukkansu tsoffin gwamnonin jihar, kai har Alhaji Sule Lamido yana tsare da mu'', in ji Shettima.
Kalaman sun haifar da ce-ce-ku-ce tsakanin ƴansiyasar ƙasar, inda wasu suka fara zargin cewa Sule Lamidon na yi wa APC aiki ne.
Sai jim kaɗan bayan kalaman mataimakin shugaban ƙasar, Sule Lamido ya barranta kansa da kalaman.
Cikin wata hira da ya yi da kafar yaɗa labarai da DC Hausa, Lamido ya ce ba abin da zai sa a yanzu ya yi APC.
''Yadda a baya ban yi APC ba, duk da kiraye-kirayen da manyan jam'iyyar suka yi min, ai yanzu ba babu wani dalilin da zai sa na yi APC''.
Lamido ya kuma danganta kalaman na Shettima da barkwancin da ke tsakanin al'umomin Fulani da Kanuri.

