Za mu bi umarnin kotu kan takarar Atiku - INEC

Asalin hoton, INEC/Atiku
Shugaban hukumar zaɓen Najeriya INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya wajabta wa hukumar bin duk wani hukunci na ƙarshe da kotuna za su yanke dangane da cancantar, Atiku Abubakar, na tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Da yake magana a cibiyar Chatham House da ke birnin Landan a ranar Alhamis, Amupitan ya mayar da martani kan tambayoyin da aka yi masa game da ko har yanzu za a sanya sunan Atiku a cikin jerin 'yan takarar shugaban ƙasa a 2027.
A makon da ya gabata ne dai babbar kotun tarayya da ke Abuja ta soke shugabancin ADC tsagin David Mark tare da duka matakan da tsagin ya ɗauka ciki har da tsayar da Atiku takara.
Atiku dai ya ɗaukaka ƙara domin neman kotun ɗaukaka ƙara ta soke hukuncin babbar kotun tarayyar, wanda Amupitan ya ce idan ya gaza samun nasara wajibi kan INEC ta cire sunansa.
"Idan a ƙarshe ya gaza, a to, wajibi ne a kaina ƙarƙashin sashe na 285 na kundin tsarin mulkin Najeriya, in bi duk wani umarnin kotu, musamman idan hukuncin ya fito daga Kotun Ƙoli," in ji shi.
Ya jaddada cewa hukumar INEC ba ta da wani zaɓi illa aiwatar da hukuncin kotu, ba tare da la'akari da tasirin da hakan zai iya yi a fagen siyasa ba.
Duk da tabbatar da aniyar INEC na mutunta bin doka da oda, shugaban hukumar ya nuna damuwa kan yawaitar shari'o'in da ake shigarwa gaban kotuna kafin zaɓe, waɗanda ke barazana ga shirye-shiryen hukumar na gudanar da zaɓen Janairun 2027.
Ya bayyana cewa a halin yanzu hukumar na fuskantar shari'o'i sama da 300 da ke gaban kotuna, duk da cewa saura makonni kaɗan a gudanar da zaɓen.


