Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE , Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Asabar 31/10/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Asabar 31/10/2026

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed

  1. INEC ta saka Pantami a takarar gwamnan Gombe, ta amince da shigar NDC a Kano

    Hukumar INEC ta wallafa jerin sunan ƴan takarar zaɓen 2027 na ƙarshe, inda a cikin jerin sunan ƴan takarar gwamna na jihohi, ta sanya sunan Farfesa Isa Ali Pantami a matsayin ɗan takarar gwamna jihar Gombe a jam'iyyar PDP.

    Da farko dai da hukumar ta fitar ta jerin sunayen, rashin ganin Pantami da Aminu Abdussalam gwarzo na NDC a jihar da wasu ya tayar da ƙura, lamarin da ya hankali matuƙa, har hukumar ta fito ta ce za ta duba ƙorafe-ƙorafen da aka miƙa mata.

    A cikin makon nan ne wasu jaridu a Najeriya suka ruwaito daga wasu majiyoyi cewa INEC ta kammala nazari, inda wasu jaridun suka ce an mayar da sunan ɗan takarar na NDC a Kano da na PDP a Gombe, yayin da wasu suka ruwaito majiyar da ke nuna cewa Pantami ne kawai aka mayar.

    Sai dai a jerin da hukumar ta fitar na ƙarshe, akwai Pantami, amma a game da takarar Kwamrade Abdulsalam na NDC a Kano, hukumar ta rubuta akwai hukuncin kotu a game da takarar, duk da cewa ta rubuta sunan NDC a cikin jerin.

    Hakan ke nufin tana sauraro kotu kafin ta kammala yanke hukunci ɗan takarar.

  2. Za a yi zanga-zangar tsadar rayuwa a ƙasashe turai a dama

    Ana sa ran ƙasashe da dama na Turai za su fuskanci tarzoma a ƙarshen makon nan, yayin da ake shirya zanga-zanga a birane da dama saboda tsadar rayuwa da kuma rashin ingancin ayyukan gwamnati.

    A Faransa, inda aka shafe makonnin baya ana fuskantar zanga-zangar da ta rikide zuwa tashin hankali, ministan harkokin cikin gida ya yi gargadin cewa akwai babbar barazanar rikice-rikicen tsaro.

    A Jamus kuma, ana sa ran dubban mutane za su fito zanga-zanga, inda shugabannin siyasa suka yi gargadin cewa masu tsattsauran ra'ayi na iya amfani da gangamin domin cimma manufofinsu.

    Ƴansanda a Sifaniya ma na shirin tunkarar yiwuwar barkewar tarzoma. A Italiya kuwa, dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a ranar Juma'a. break

  3. Amurka za ta sayar wa Ukraine makamai masu linzami

    Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce ta amince da sayar wa Ukraine makamai masu linzami na kariya da darajarsu ta haura dala biliyan biyu.

    Ƙasashen Canada da Jamus da kuma Norway ne suka biya kuɗin waɗannan makamai guda 500.

    Wakilin BBC ya ce shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce a wannan makon ƙasarsa ta shafe kusan wata guda tana jiran Amurka ta amince da samar da muhimman makamai masu linzami da take buƙata.

    Inda ya sha yin kira ga Washington din da ta hanzarta isar da makaman kafin lokacin hunturu ya yi tsanani. Sai dai ana fuskantar karancin irin wadannan makamai a duniya, sakamakon yadda Amurka ke amfani da su a yakinta da Iran.

  4. Idan Amurka ta sake kai mana hari, yaƙin zai faɗaɗa zuwa wasu yankuna - Iran

    Dangane da yiwuwar wani sabon hari da Amurka za ta kai wa Iran, kakakin rundunar sojin Iran, Mohammad Akraminia, ya ce idan hakan ta faru, fagen yaƙin zai faɗaɗa zuwa wasu yankuna.

    Ya rubuta a shafinsa na dandalin sada zumunta na X cewa: "Duba da mummunan tarihin shugaban Amurka na yin watsi da tattaunawar diflomasiyya, rundunar sojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, wadda ba ta yarda da maƙiyi kuma ba ta damu da ayyukansa ba, tana ci gaba da inganta shirinta na yaƙi a kowane lokaci."

    Ya ci gaba da cewa: "Idan shugaban Amurka ya sake tsunduma cikin wani sabon kasada a yankin ta hanyar barazana da kuma tunzurawa, babu shakka wutar yaƙi za ta bazu zuwa wasu yankuna, kuma makomar yain za ta bar hannunsa."

    Wɗannan kalamai na zuwa ne bayan da kamfanin dillancin labarai na Axios ya ruwaito, yana mai nakalto majiyoyin diflomasiyya, cewa masu shiga tsakani daga Qatar na ci gaba da tattaunawa domin cimma yarjejeniya kan sake farawa kai tsaye tattaunawa tsakanin Amurka da Iran.

    An ce za a ci gaba da waɗannan tattaunawa a birnin Doha ranar Asabar.

  5. Buɗewa

    Masu bibiyar shafin BBC Hausa kai-tsaye, Assalamu alaikum. A yau ma, kamar kullum, za mu kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Kuna kuma iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa kamar a Fesbuk da X da Instagram, sannan ku ziyarci shafinmu na YouTube domin kallon bidiyo.