Babu sulhu tsakanin mu da Boko Haram - Sojojin Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojin Najeriya ta ce babu batun tsagaita wuta tsakaninta da ƙungiyoyin masu ikirarin jihadi na Boko Haram da ISWAP.
Hare-haren da Boko Haram da ISWAP ke kai wa kan sansanonin soja a arewa maso gabashin Najeriya sun ƙaru a 'yan makonnin nan duk da shafe shekaru ana gudanar da ayyukan soja da nufin daƙile tayar da kayar bayan da ya shafe shekaru 17 yana gudana a yankin.
Da yake jawabi a wani taron bayani kan harkokin leƙen asiri a babban birnin tarayya Abuja, kakakin rundunar sojin Najeriya, Manjo Janar Samaila Uba, ya ce nasarorin da aka samu a baya-bayan nan, ciki har da kashe masu tayar da ƙayar baya da kama waɗanda ake zargi da kuma kuɓutar da mutanen da aka yi garkuwa da su.
Sojojin sun ce jami'an tsaro na ci gaba da matsa wa ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai lamba.
"Ina so na bayyana ƙarara cewa babu maganar tsagaita wuta ko kaɗan... idan aka yi la'akari da nasarorin da aka samu a dukkan ayyukanmu, a bayyane yake cewa ba mu sassautawa," in ji Uba.
Ya kuma ce Najeriya na tattaunawa da ƙasashen makwabta na yankin Sahel da suka fice daga ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka ta ECOWAS kan haɗin gwiwar tsaro da harkokin diflomasiyya


