Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 26/10/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 26/10/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Aisha Aliyu Jaafar Aminu Kutama

  1. Switzerland ta ce babu barazana ga mutanen ƙasar bayan an kai mai Ebola daga Najeriya

    Gwamnatin Switzerland ta bayyana cewa babu wata barazana ga mutanenta bayan an ɗauke wata mara lafiya da ta kamu da nau’in cutar Bundibugyo Ebola daga Najeriya zuwa wani asibiti a Geneva domin ci gaba da jinya.

    A ranar Litinin ne gwamnatin ta ce kamfanin agajin gaggawa na sama na Switzerland, Swiss Air-Rescue, ya kai mara lafiyar, wadda yanzu take samun kulawa ta musamman a asibitin Geneva University Hospitals (HUG).

    Mijin mara lafiyar, wanda ake ɗauka a matsayin wanda ya yi kusanci da ita, an killace shi a asibitin Zurich University Hospital (USZ), kuma dukkaninsu ƴan ƙasar ne.

    Wannan mataki ya biyo bayan sanarwar da Nijeriya ta fitar a ranar Litinin cewa an mayar da mara lafiyar zuwa Switzerland domin samun ƙarin kulawa.

    Gwamnatin Switzerland ta ce jigilar mara lafiyar da kuma kula da ita a asibiti an yi su ne bisa ƙa’idojin lafiya na ƙasa da na ƙasa da ƙasa domin hana yaɗuwar ƙwayar cutar.

  2. Sakamakon zaɓen Isra’ila ba zai sauya mana komai ba - Iran

    Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana cewa sakamakon zaɓen majalisar dokokin Isra’ila, inda Firaminista Benjamin Netanyahu ke fuskantar ƙalubale mai zafi ba zai kawo wani sauyi ga matsayar Tehran ba.

    Mai magana da yawun ma’aikatar, Esmaeil Baqaei ya ce a taron manema labarai na mako-mako cewa, “Ba shi da wani bambanci a gare mu ko wa zai jagoranci wannan gwamnati da ta jawo tashin hankali da zubar da jini a yankinmu.”

    Za a gudanar da zaɓen ‘yan majalisar dokokin Isra’ila ne a ranar Talata, yayin da ake ci gaba da samun barazanar sake barkewar rikici tsakanin Isra’ila, Amurka da Iran bayan yakin da ya fara tun karshen watan Fabrairu.

    A baya Netanyahu ya sha bayyana cewa hanya guda da za a kawar da barazanar Iran ita ce "hamɓarar da gwamnatin ƙasar," har ma ya ce ya umarci jami’an leken asiri na Mossad da sojojin Isra’ila su yi aiki domin kifar da gwamnatin Iran.

    Sai dai Iran ta yi watsi da waɗannan kalamai, yana mai kiran su da “barazana maras amfani” da kuma “alamar rashin mafita.”

  3. Ƙungiyar Izala ta nesanta kanta da bidiyon ‘yan agajin da ke kalaman ‘tunzura jama’a’

    Ƙungiyar Jama'atu Izalatul Bidi'ah Wa'iƙamatus-Sunnah (JIBWIS), wadda aka fi sani da Izala, ta yi Allah wadai da wani faifan bidiyo da aka hangi wasu matsa 'yan agajin na rera wasu kalamai na "tunzura jama'a",

    Ƙungiyar ta ce ba ta amince da kalaman da aka ji a ciki ba.

    Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya buƙaci hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), rundunar 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro su gudanar da bincike cikin gaggawa, domin gano waɗanda ke da hannu a lamarin tare da hukunta duk wanda aka samu da laifi bisa doka.

    A cikin sanarwar da ɗaya daga cikin jami'an yaɗa labaran ƙungiyar, Ibrahim Shehu Giwa, ya fitar a ranar Litinin, 26 ga Oktoba, 2026, Sheikh Bala Lau ya ce: " Muna kira ga jami'an tsaro na DSS da 'yan sanda su kama wanda ya yi bidiyon, sanye da kayan agaji, yana wasu jawabai cewa a ba su AK-47, su je Enugu ranar Lahadi, lokacin motsa jiki, domin kai hari.

    Ya kuma ce kasancewar mutum sanye da kakin aikin 'yan agajin JIBWIS ko kuma bayyana tare da mambobinta ba yana tabbatar da cewa yana magana ko aiki ne da izinin ƙungiyar ba.

    "Ko da yake an gan shi sanye da kakin aikin 'yan agajinmu, kuma an gan shi a cikinmu, hakan ba yana nufin cewa ba turo shi aka yi domin ya ɓata wa ƙungiyar suna ba."

  4. NAHCON ta horas da masu aikin jigilar aikin Hajji

    Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta fara wani shirin horo na kwana biyu domin ƙara wa kamfanonin jigilar aikin Hajji da Umrah masu lasisi ƙwarewa a jihohin Kano da Legas.

    Wata sanarwa da Shugaban Sashen Yaɗa Labarai da Wallafe-wallafe na hukumar, Shafii Sani Mohammed ya fitar ta ce Shugaban NAHCON, Amabasada Ismaila Abba Yusuf ya bayyana cewa shirin zai taimaka wajen shirya masu gudanar da ayyukan Hajji a Najeriya domin sauye-sauyen da ke faruwa a harkar Hajji ta duniya sakamakon sauye-sauyen da ke ƙarƙashin shirin Vision 2030 na Saudiyya da kuma sabon tsarin kasuwanci tsakanin kamfanoni (B2B).

    Ya kuma bayyana cewa NAHCON ta samu amincewar gwamnatin Saudiyya kan wani tsari na sauyi a matakai na tsawon shekaru uku, wanda zai fara da kaso 30 cikin 100 na shiga hannun kamfanoni masu zaman kansu daga shekarar 2027. Wannan zai ba Najeriya damar ƙarfafa tsarin kula da dokoki da kuma shirya masu gudanar da ayyukan Hajji domin ɗaukar ƙarin nauyi.

  5. Kotu ta yi watsi da buƙatar El-Rufai game da tuhumarsa

    Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da buƙatar da Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufaʼi ya gabatar na cewa babu isasshiyar hujjar da za ta sa ya kare kansa a shari’ar da ake yi masa kan zargin sauraron tattaunawar waya ba bisa ƙa’ida ba.

    Kotun ta ce masu gabatar da ƙara sun gabatar da isassun hujjoji da suka sa ya zama dole a kira wanda ake tuhuma domin ya kare kansa. Saboda haka, kotun ta umarci El-Rufaʼi da ya fara gabatar da bayanan kariyarsa a watan Nuwamba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

    Ana tuhumar El-Rufai ne a ƙarƙashin sabbin tuhume-tuhume guda biyar da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta shigar, bisa zargin cewa ya yi kutse tare da sauraron tattaunawar wayoyi da ke da alaƙa da Nuhu Ribadu ba bisa ƙa’ida ba.

    A watan Fabrairun 2026 ne yayin wata hira a shirin Prime Time na Arise Television, tsohon gwamnan na Kaduna ya yi iƙirarin cewa wani ya sa ido kan wayar Nuhu Ribadu, wanda hakan ya ba shi damar jin yadda Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ke umartar jami’an tsaro su kama shi.

    Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta amince da matsayin masu gabatar da ƙara, tare da umartar El-Rufai ya buɗe kariyarsa, kuma ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 25 ga Nuwamba.

  6. Majalisar Kano ta amince da mutum shida don naɗa su a matsayin kwamishinoni

    Majalisar Dokokin Jihar Kano ta tantance mutane shida da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya miƙa mata domin naɗa su a matsayin kwamishinoni a gwamnatinsa.

    Waɗanda aka tantance sun haɗa da Ibrahim Namadi Dala da Mukhtari Ishaq Yakasai da kuma Farfesa Sani Lawan Malumfashi. Sauran sun haɗa da Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa da Idris Garba Mustapha, sai kuma Salisu Yushaʼu Soja.

    Tun a ranar Laraba, 21 ga Oktoba, Kakakin Majalisar, Jibril Ismail Falgore ya karanta wasiƙar gwamnan da ke neman majalisar ta tantance tare da amincewa da naɗin waɗannan mutane.

    Naɗin na cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na cike guraben kwamishinoni da suka kasance babu kowa a cikinsu sakamakon sauye-sauyen siyasa da suka faru a jihar.

  7. Masar za ta aika dakaru Saudiyya domin taimaka mata yaƙi da ƴan Houthi

    Majalisar dokokin Masar ta amince da tura tallafin soji zuwa Saudiyya domin taimaka mata wajen kare kanta daga hare-haren 'yan tawayen Houthi.

    Matakin, wanda ya biyo bayan buƙatar da Shugaban Masar, Abdel Fattah al-Sisi, ya gabatar, na iya sanya Masar shiga kai tsaye cikin rikicin yankin, wanda ake yi tsakanin masarautar Saudiyya da 'yan tawayen Houthi na Yemen masu samun goyon bayan Iran, waɗanda hare-haren da suke ci gaba da kai wa ke barazana ga mashigar Bab el-Mandeb, wata muhimmiyar hanya ruwa.

    Yayin wata ziyara da ya kai Alkahira, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya ce yana da matukar muhimmanci a dakatar ta'azzarar rikici a Gabas ta Tsakiya, musamman a daidai lokacin da Amurka da Iran ke ci gaba da yi wa juna barazana.

  8. Kotu ta yanke wa Chris Brown hukuncin ɗauri saboda tayar da rikici a gidan rawa

    Wata kotu a Landan ta yankewa shahararren mawakin Amurka, Chris Brown, hukuncin daurin watanni takwas na je ka gyara halinka, sakamakon wata hatsaniya da ta faru a wani gidan rawa a shekarar 2023.

    Brown ya amsa laifin tayar da rikici.

    Hotunan kyamarorin tsaro (CCTV) sun nuna mawakin yana bugun tsohon abokinsa, Abe Diaw, a kai da kwalbar giya.

    Abe Diaw ya samu raunuka a kai da gwiwa, lamarin da ya sa aka kai shi asibiti domin yi masa magani.

  9. Ƴan Houthi sun yi iƙirarin kai hari tashoshin tura mai na Saudiyya da filin jirgin saman Riyadh

    'Yan tawayen Houthi na Yemen sun ce sun kai hare-hare kan tashoshin tura man fetur na bututun mai na Gabas na Saudiyya da kuma filin jirgin saman Riyadh.

    Wannan ba shi ne karon farko da aka kai hari kan wannan bututun mai da tashoshin tura man nasa ba.

    Har yanzu jami'an Saudiyya ba su ce uffan ba game da wannan labari, amma a watan da ya gabata hare-haren Houthi kan filayen jiragen sam da tashoshin jiragen ruwa da cibiyoyin mai na Saudiyya sun ƙaru.

    Ƙawancen tsaron ƙasashen da Saudiyya ke jagoranta, wanda ke yaki da 'yan tawayen Houthi masu alaƙa da Iran, a baya ya ce ya kai hare-hare kan wurare biyu da ake harba makamai masu linzami masu dogon zango daga cikinsu a birnin Sana'a, babban birnin Yemen.

    A cewar kawancen, an harba makami mai linzami daga ɗaya daga cikin waɗannan wurare zuwa Riyadh, amma an yi nasarar kakkabe shi kafin ya kai ga inda aka nufa.

    Bututun mai na Gabas maso Yamma na Saudiyya, wanda tsawonsa ya kai kusan kilomita 1,200, ya ratsa gaba ɗaya yankin Larabawa.

    Wannan muhimmin bututun mai da kamfanin Aramco ke gudanarwa na taka muhimmiyar rawa wajen jigilar man Saudiyya ba tare da ya bi ta mashigar Hormuz ba.

  10. Ƴanbindiga sun hallaka mutum aƙalla 40 a Ethiopia

    Akalla mutane 40 ne suka rasa rayukansu yayin wani hari da aka kai kan wasu ƙauyuka a tsakiyar ƙasar Habasha.

    Shaidun gani da ido sun ce wasu ‘yan bindiga sun isa gundumar Shirka da yammacin ranar Asabar, inda suka fara harbe-harbe kan mutane a cikin gidajensu kafin daga bisani su banka musu wuta.

    An dai sha kai hare-hare kan Kiristoci a yankin, sai dai har yanzu ba a tabbatar ko sabon harin yana da nasaba da addini ba.

    Gundumar Shirka tana cikin Jihar Oromia ta Habasha, inda mayaka ke ci gaba da fafatawa da gwamnatin tarayya a wani rikici da ya dauki tsawon lokaci.

    Majiyoyi daga coci sun ce an binne waɗanda aka kashe a harin na ranar Asabar a wani babban kabari, ciki har da yara biyar.

  11. FBI ta kama ƴan Najeriya 9 da take zargi da gudanar da ayyukan damfara

    Hukumar Binciken Manyan Laifuffuka ta Amurka (FBI) ta ce ta kama mutane tara da ake zargi da hannu a cibiyoyin damfara da ke Najeriya.

    A cikin wata sanarwa da Daraktan FBI, Kash Patel, ya fitar ranar Litinin, ya ce an kuma gano kimanin dala miliyan 11 da ake shirin ƙwacewa a ƙasashe daban-daban.

    Ya kuma ce an ƙwace kwamfutoci da wayoyi 53.

    A cewar Patel, waɗanda ake zargi da gudanar da waɗannan cibiyoyin damfara a Najeriya, suna yaudarar mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, suna sace musu kuɗaɗensu, kuma suna aiki ne a ƙasashe daban-daban, a cewar sa ''suna tunanin sun fi ƙarfin hukumomi''.

    Ya kuma ce za su ci gaba da yaƙi da ƙungiyoyin damfara na ƙasa da ƙasa da ke sace wa Amurkawa biliyoyin daloli.

    Patel ya miƙa godiyarsa ga hukumomin tsaro na Najeriya da kuma abokan hulɗarsu a birnin London saboda haɗin kan da suka bayar wajen gudanar da binciken.

  12. Za a gudanar da taron tattauna tsaron Gabas Ta Tsakiya

    Mahukuntan Iran da Saudiyya sun ce za a gudanar da tattaunawa kan tsaron yankin Gabas Ta Tsakiya, a Tehran ranar Litinin.

    Ana sa ran jami'an Iran za su gana da manyan wakilai daga Pakistan, Saudiyya da Turkiyya.

    Ƙasashen uku sun rattaɓa hannu kan Yarjejeniyar Makka a watan Agusta, inda suka bayyana cewa duk wani hari kan ɗaya daga cikinsu za a ɗauke shi a matsayin hari kan su duka.

    Wannan ce za ta kasance tattaunawa ta farko tsakanin Iran da sabuwar kawancen da aka kafa, wanda aka fara gwada karfinsa cikin gaggawa, yayin da rikicin da ke tsakanin Saudiyya da 'yan tawayen Houthi da Iran ke marawa baya a Yemen ya kara tsananta.

    Har yanzu Turkiyya da Pakistan ba su tabbatar a hukumance cewa za su halarci tattaunawar ba.

  13. Isra'ila ta musanta samun saɓani tsakanin Netanyahu da sojin ƙasar

    Ministan Tsaron Isra'ila, Israel Katz, ya musanta rahotannin da ke cewa akwai sabani tsakanin Firaminista Benjamin Netanyahu da sojojin kasar kan zarge-zargen cewa Netanyahu na son kai hari kan Iran kafin zaben ranar Talata.

    Haka kuma ofishin Firaministan ya musanta rahotannin da ke cewa Netanyahu ya gaza yin nasara a ƙoƙarinsa na matsa wa Shugaba Donald Trump lamba ya kaddamar da sabbin hare-hare kan Iran.

    Babban abokin hamayyar Netanyahu, tsohon hafsan hafsoshin rundunar sojin Isra'ila Gadi Eisenkot, ya zargi Firaministan da amfani da yi wa Iran barazana wajen cimma muradun siyasa, sannan ya ce ya gaza cimma manufofin yakin da ya sanya a gaba.

  14. An fitar da matar da ta kai cutar Ebola Najeriya daga ƙasar

    An fitar da matar nan ta farko da aka tabbatar na ɗauke da cutar Ebola a Najeriya daga asar zuwa Switzerland domin ci gaba da jinyarta.

    Ministan Lafiya na Najeriya, Ali Pate, ne ya tabbatar da hakan.

    Yana mai cewa an fiytar da matar ne daga kasar bisa amincewarsa, inda ya ƙara da cewa mijinta, wanda har yanzu bai nuna alamun kamuwa da cutar ba, ya yi mata rakiya.

    A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, yayin da ya ke martani kan wani bidiyo da aka wallafa na yadda ake shiga da matar jirgin sama, ministan ya ce marar lafiyar ta samu sauƙi sosai kafin a kai ta Switzerland.

    Sai dai Pate ya ce hakan ba yana nuna cewa marar lafiyar ta samu sauƙin da ba za ta iya yaɗa cutar ba, inda ya ce har yanzu ana ci gaba da bin tsauraran ƙa'idojin kariyar lafiyar jama'a.

  15. Za a killace duk ɗan Uganda da ya koma ƙasar bayan tafiya zuwa Kongo na makonni 3

    Uganda ta ce za a killace duk wani ɗan ƙasar da ya koma ƙasar bayan yin tafiya zuwa Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC) na tsawon kwanaki 21, yayin da ta ke ƙara tsaurara matakan kariya daga cutar Ebola.

    Ministan Lafiya na Uganda, Chris Baryomunsi, ya ce a halin yanzu babu cutar Ebola a ƙasar, bayan da aka sanar da kawo ƙarshen bullar cutar a watan Yuli.

    Sai dai masana harkokin lafiya sun nuna damuwa bayan wasu mutum biyu da suka bi ta Uganda kwanan nan sun kamu da cutar bayan gwajin da aka yi musu a ƙasashen Kenya da Najeriya.

    Uganda ta kuma ce tana bincike kan matar da ta kamu da cutar da ke Najeriya.

    Matar mai shekaru 42 ta shiga Abuja ne bayan dawowa daga Uganda ta Addis Ababa a ranar 3 ga Oktoba, a cewar Hukumar Yaki da Cututtuka ta Najeriya (NCDC).

  16. Ana iya kawo ƙarshen rashin tsaron arewacin Najeriya cikin kwanaki 45 - KACRAN

    Ƙungiyar makiyaya ta Najeriya KACRAN ta ce za a iya kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro da ta addabi yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya cikin kwanaki 45, idan gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohin yankunan suka ba da cikakken goyon baya ga wani shirin sulhu da ta gabatar.

    Cikin wata sanarwar da da shugaban kungiyar na ƙasar, Mohammed Khalil Bello ya fitar ya ce shirin ƙungiyar ya tanadi makonni biyu na farko domin tuntuɓa da tattaunawa da masu ruwa da tsaki, kafin a shafe wata guda ana aiwatar da matakan samar da zaman lafiya.

    Ta ce akwai isassun shugabanni da masana harkokin tsaro daga Arewa da za su iya taka rawa wajen ganin an magance matsalar.

    KACRAN ta kuma jaddada cewa zaman lafiyar Arewa na da muhimmanci ga tattalin arzikin Najeriya, ganin cewa yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya na daga cikin cibiyoyin samar da abinci a ƙasar.

    Ta ce rashin tsaro na ci gaba da yin barazana ga noma, kiwo da sauran harkokin tattalin arziki.

    Ƙungiyar ta yi nuni da abin da ta kira nasarar amfani da tattaunawa wajen rage rikice-rikice a jihohin Kaduna da Katsina, tana mai kira ga sauran gwamnonin yankunan da su rungumi irin wannan hanya wajen warware matsalolin tsaro.

    Sai dai ƙungiyar ta yi gargaɗi cewa kafa ƙungiyoyin sa-kai a kan tushen ƙabilanci ka iya ƙara rikita matsalar tsaro.

    KACRAN ta kuma buƙaci gwamnati ta amince da shirin zaman lafiyar da ta gabatar, tare da ɗaukar matakai kan duk waɗanda suka ƙi bin duk wata yarjejeniyar sulhu da aka cimma.

  17. Adadin mutanen da suka mutu a harin ƴanbindiga a Taraba ya kusa 50

    'Yan sanda a jihar Tarabar Najeriya sun ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon harin da 'yan fashin daji suka kai wani kauye a jihar ya ƙaru zuwa 48.

    Ƴanbindiga sun kai hari hari ƙauyen Binnari da ke ƙaramar hukumar Karim Lamido jim kaɗan bayan sallar Juma'a, suna harbin kan mai uwa da wabi, tare da sace kayayyakin abinci da kuma ƙona shaguna da babura.

    Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Victor Mshelizah, ya shaida wa BBC cewa adadin ya ƙaru ne biyo bayan gano ƙarin gawawwaki 23 a jiya Lahadi.

    Ya ce binciken 'yan sanda ya nuna cewa wasu daga cikin waɗanda harin ya rutsa da su sun nutse ne a ruwa yayin da suke ƙoƙarin tserewa maharan, yayin da aka kashe wasu a cikin dazukan da ke kusa da yankin.

    Mazauna ƙauyen sun ce maharan sun shiga ƙauyen ne daga jihar Filato da ke makwabtaka da jihar ɗauke da muggan makamai.

    Ƙungiyar kare haƙƙin biladama ta Amnesty International ta zargi hukumomi da gaza kare alummomin ƙauyuka daga hare hare ƴan bindiga.

    Zuwa yanzu dai babu ƙungiyar da ta ɗauki alhakin harin, sai dai jihar ta Taraba da sauran jihohin Najeriya na ci gaba da fama da hare haren ƴan bindiga da sace mutane domin karɓar kuɗin fansa.

  18. Ƙungiyar ɗalibai masu zanga-zangar neman sauyi ta lashe babban zaɓen ƙasar Serbia

    A wani sakamako da ya bai wa mutane da dama mamaki, wata ƙungiyar ɗalibai masu zanga-zangar neman sauyi ce ta lashe babban zaɓen ƙasar Serbia, inda ta doke tsohon shugaban ƙasar Aleksandar Vucic, wanda ya shafe shekaru 14 yana mulki.

    Bayan da Mista Vucic ya amince da shan kaye, dubban magoya bayan 'yan dawa sun fito kan titunan birnin Belgrade suna ta shagulgula.

    Yawan waɗanda suka fito kaɗa ƙuri'a ya kai kusan kashi 70 cikin 100, wanda ya zamo mafi yawa a cikin gwamman shekaru.

    Wakilin BBC da ke Belgrade ya ce har yanzu ba a san cikakkun bayanai a kan yadda ƙungiyar ɗaliban ta tsara ayyukanta ba, haka kuma ba a san wanene zai zama sabon firaministan ƙasar ko manufofin da sabuwar gwamnati za ta bi ba.

  19. Luiz Inacio Lula da Silva ya lashe zaɓen Brazil da ƙuri'u miliyan 4

    Luiz Inacio Lula da Silva, ya samu gagarumar nasara a zaɓen shugaban ƙasar Brazil, inda ya doke abokin hamayyarsa mai ra'ayin riƙau, Flavio Bolsonaro, da sama da ƙuri'u miliyan huɗu.

    Jagoran mai shekaru 80, ya shaida wa magoya bayansa da suka tarbe shi da murna cewa 'yan Brazil sun kaɗa kuri'a ne domin "tabbatar da ɗorewar dimokraɗiyya".

    Sai dai Mista Bolsonaro ya ƙi amincewa da sakamakon zaɓen, yana mai cewa lauyoyinsa za su nemi a soke shi.

    Ya ce matakin wata kotu na tsawaita lokacin kaɗa ƙuri'a da sa'o'i biyu da kuma sakamakon tangardar sufuri ba abu ne da za a amince da shi ba.

    Wakiliyar BBC ta ce tun bayan da aka dawo da mulkin dimokradiyya a Brazil a 1989, babu wani ɗan takara da ya samu nasara a zagayen farko sannan ya gaza samun nasara a zagaye na biyu a zaɓe.

  20. Buɗewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Litini, inda za mu cigaba da kawo muku labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Kuna iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta kamar Fesbuk da X da Instagram, sannan ku ziyarci shafinmu na YouTube domin kallon bidiyo.