An tsige shugaban Paraguay

Asalin hoton, Getty Images
An tsige shugaban ƙasar Paraguay Santiago Pena sannan kuma an tsare shi a gida bayan durƙushewar wani banki ya haifar da matsalar da ta sanya sama da rabin al'ummar ƙasar sun kasa amfani da kuɗaɗensu na ajiya da ke cikin asusun banki.
A jiya Juma'a ne aka kama Pena jim kaɗan bayan ƴan majalisar dokokin ƙasar sun tsige shi da gagarumin rinjaye, tare da goyon bayan ƴan jam'iyyarsa.
Lamarin ya biyo bayan durƙushewar bankin Ueno Bank a farkon mako, wanda ke da alaƙa da kamfanonin da ake alaƙantawa da Peno.
Ya yi yunƙurin ajiye mulki a ranar Alhamis. To sai dai a maimakon amincewa da ajiye mulkin nasa, sanatocin sun yanke shawarar tsige shi tare da tuhumar shi da saɓa ƙa'idar aiki, wanda hakan ke nufin an tuɓe masa kariyar da ake bai wa tsofaffin shugabannin ƙasar.
Pena, wanda har a shekarar da ta gabata yake da hannun jari a kamfanin da ya mallaki bankin, ya musanta aikata ba-daidai ba.
Tuhume-tuhumen da suka kai ga tsige Shugaba Pena sun yi zargin cewa ya nuna son rai wajen gudanar da ayyukan kula da kamfanoni, ya karkatar da kuɗaɗen fansho sannan yana da hannu wajen yin rufa-rufa game da wasu ayyukan babban bankin ƙasar.














