Mun lalata makami mai linzami na Houthi da aka harba zuwa Riyadh
Asalin hoton, Getty Images
Ƙasar Saudiyya ta sanar da cewa ta dakatar tare da lalata wani makami mai linzami na ƙungiyar Houthi.
Kakakin rundunar kawancen sojojin da Saudiyya ke jagoranta, Turki al-Maliki, ya ce an harba makamin ne zuwa babban birnin ƙasar, Riyadh.
Tun da farko, wakilan kamfanin dillancin labarai na AFP sun ruwaito cewa sun ji karar fashewa sau biyu a birnin Riyadh.
Bayan fitar da gargaɗin haɗari, Hukumar Kariya ta Farar Hula ta Saudiyya ta sanar bayan 'yan mintoci kaɗan cewa "An kawar da haɗarin."
Najeriya ta tabbatar da ɓullar Ebola a Abuja babban birnin ƙasar
Najeriya ta tabbatar da samun mutum ɗaya da ya kamu da cutar
Ebola a Babban Birnin Tarayya, Abuja, lamarin da ya sa hukumomin lafiya suka
fara bibiyar mutanen da suka yi hulɗa da mara lafiyar domin hana yaɗuwar cutar.
A cikin wata sanarwa da Ministan Lafiya,
Ali Pate, ya fitar a ranar Talata, ya ce an gano mutane 44 da suka yi kusanci
da mara lafiyar, kuma ana sa ido a kansu a matsayin wani ɓangare na matakan
dakile yaɗuwar cutar.
Matar da aka tabbatar ta kamu da cutar ta iso Najeriya ne
daga ƙasar Uganda, inda aka kwantar da ita a wani asibiti mai zaman kansa a
Abuja kafin gwaje-gwaje su tabbatar tana ɗauke da cutar Ebola. A halin yanzu tana killace kuma tana karɓar
kulawar likitoci.
Rahotanni sun nuna cewa Najeriya ita ce ƙasa ta farko a
Yammacin Afirka da ta tabbatar da bullar cutar da ke da alaƙa da annobar
Ebola da aka ayyana a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC) da Uganda a watan
Mayu.
Tun bayan ɓarkewar annobar, cutar ta bazu zuwa wasu ƙasashe.
A ranar Talata, Kenya ta ce ta samu
mutane tara da suka kamu da cutar, a cewar ma'aikatar lafiyar ƙasar.
Hakan ya
sa Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta shawarci 'yan ƙasar ta da su sake yin
nazari kafin tafiya zuwa Kenya saboda haɗarin kiwon lafiya.
A cewar hukumomin lafiya, Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo na
ci gaba da kasancewa cibiyar wannan annoba, inda aka samu sama da mutane 9,400
da suka kamu da cutar da kuma fiye da mutum 4,500 da suka mutu zuwa tsakiyar
watan Oktoba.
An ce cutar ta bazu zuwa larduna takwas na ƙasar, kuma ana ci
gaba da gwagwarmayar dakile yaɗuwarta.
A Uganda kuwa, an ayyana kawo ƙarshen annobar a watan Agusta
bayan an sallami mara lafiya na ƙarshe daga asibiti a watan Yuli.
Tun farkon annobar, Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta ƙarfafa sa ido kan cututtuka tare da fitar da shawarwari
ga matafiya. Hukumar ta ce matafiya daga ƙasashen da ake fama da Ebola na iya
fuskantar ƙarin tantancewa, ciki har da cike takardar bayanan lafiya.
Hukumar ta kuma bukaci matafiya su kasance cikin lura tare
da gaggauta neman kulawar likita idan suka fara nuna alamomin cutar, waɗanda
suka haɗa da zazzaɓi, ciwon kai, gajiya mai tsanani, amai da gudawa.
Gwamna Uba Sani ya yi alƙawarin tallafa wa Ahmed Zakka da Iyalinsa
Asalin hoton, Senator Uba Sani/Faceebook
Gwamnan Jihar Kaduna ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da tallafa wa Malam Ahmed Abubakar Zakka, matarsa Nafisah da 'yarsu Fatima bayan samun 'yancinsu, inda ya tabbatar da cewa za a samar musu da gida tare da ɗaukar nauyin dukkan kuɗaɗen jinyarsu.
A wata ziyara da ya kai musu a gidan kulawa na Gwamnatin Jihar Kaduna, gwamnan ya ce iyalan na ci gaba da samun kulawar lafiya bayan an sallame su daga asibiti, kuma ya nuna gamsuwa da yadda lafiyarsu ke ƙara inganta.
Ya bayyana cewa abin da ya faru da iyalan wata alama ce ta irin raɗaɗin da rashin tsaro ke haifarwa ga al'umma, yana mai jaddada cewa gwamnati na da alhakin kare rayuka da tabbatar da zaman lafiya a dukkan sassan jihar.
Gwamnan ya ce gwamnatin jihar ba za ta tsaya ga wannan ziyara kaɗai ba, domin za ta samar wa iyalan gida, ta biya dukkan kuɗaɗen magani, sannan ta tabbatar suna samun kulawar ƙwararru kan lafiyar kwakwalwa da walwala domin taimaka musu su farfaɗo tare da sake gina rayuwarsu.
Ya ƙara da cewa samun 'yancin nasu ya ƙara wa gwamnati ƙarfin gwiwa wajen yaƙi da 'yan bindiga da sauran masu aikata laifuka, ta hanyar ƙara haɗin gwiwa da hukumomin tsaro da kuma kusantar al'ummomi.
Gwamnan ya kuma yabawa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu saboda nuna damuwa da kuma sa ido kan lamarin, tare da yaba wa Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Malam Nuhu Ribadu, da sauran hukumomin tsaro saboda rawar da suka taka wajen tabbatar da dawowar iyalan gida cikin aminci.
A nasa ɓangaren, Malam Ahmed Abubakar Zakka ya gode wa Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Kaduna da kuma jami'an tsaro saboda ƙoƙarinsu da kulawar da suka nuna masa da iyalinsa a lokacin da suke fuskantar wannan ƙalubale.
Ya ce yana jin daɗin kulawar da ake ba shi, kuma yana da kwarin gwiwar cewa zai ci gaba da samun sauƙi har zuwa cikakkiyar murmurewa.
Gwamnatin Kaduna ta ce lafiyar iyalan da kuma cikakkiyar farfaɗowarsu za su ci gaba da kasancewa cikin manyan abubuwan da za ta bai wa fifiko a watanni masu zuwa.
Iran ta bukaci MDD ta dakatar da barazanar Amurka da Isra'ila cikin gaggawa
Asalin hoton, Getty Images
A cikin wata wasiƙa da ta aika wa Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD), gwamnatin Iran ta yi Allah wadai da barazanar Amurka ta amfani da abin da ake kira "Uwar Bamabamai" (Mother of All Bombs), tare da kira ga MDD da ta ɗauki matakin gaggawa domin dakatar da barazanar da Amurka da Isra'ila ke yi.
Wasiƙar, wadda Gholamhossein Darzi, jakada kuma wakilin Iran a hedikwatar MDD da ke New York, ya sanya wa hannu, an aike ta ne ga Sakatare Janar na MDD da kuma shugaban Kwamitin Tsaro na wannan lokaci.
A cikin wasiƙar, wakilin Iran ya bukaci jami'an MDD biyu da su "Yi kira cikin gaggawa ga Amurka da gwamnatin Isra'ila da su dakatar da barazanarsu da ta saɓa wa doka, tare da cika wajibansu bisa Kundin Tsarin Mulkin Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma ƙa'idojin dokokin ƙasa da ƙasa."
Wannan matakin ya biyo bayan wani rahoto da tashar CNN ta wallafa a makon da ya gabata, inda ta ce ta tattauna da wasu jami'an Amurka da suka bayyana cewa rundunar sojin ƙasar ta shirya sabbin tsare-tsaren kai hari kan Iran.
Rahoton ya ce daga cikin zaɓuɓɓukan da ake nazari akwai yiwuwar amfani da bam ɗin da aka fi sani da "Mother of All Bombs", idan Shugaban Amurka Donald Trump ya bayar da umarnin sake fara ayyukan soji.
Iran ta bayyana cewa irin waɗannan kalamai da shirye-shiryen soja suna ƙara tsananta tashin hankali a yankin, kuma tana ganin sun saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa da manufar zaman lafiya da tsaro ta duniya.
APC ta musanta zargin shirin kashe Atiku
Asalin hoton, Getty Images
Jami'yyar APC mai mulki a Najeriya ta musanta zargin cewa akwai wani shiri na kashe tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Action Democratic Congress (ADC) a zaɓen shekarar 2027, Atiku Abubakar.
Mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen jamiyyar APC, Dele Alake, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar, yayin da yake mayar da martani kan wani zargi da wani ɗan jam'iyyar ADC, Timi Frank, ya yi.
Jam'iyyar APC ta musanta kai-tsaye cewa Shugaba Bola Tinubu ko Fadar Shugaban Ƙasa ko kuma APC'n na da hannu a duk wani shirin cutar da Atiku Abubakar ko wani jigon jam’iyyun adawa.
Sanarwar ta kuma musanta rahotannin da ke cewa an janye jami’an tsaron da ke kare tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar, inda ya tabbatar da cewa Atiku na ci gaba da samun cikakkiyar kariya daga rundunar ’yan sandan Najeriya da kuma Hukumar Tsaro ta DSS.
Dele Alake ya kuma ce zargin kisan ba komai bane illa 'ƙulle-ƙullen siyasa irin ta jamiyyun adawa', inda ya ce an yi hakan ne domin a zafafa siyasar ƙasar da kuma jawo hankalin ƙasashen duniya ta hanyar amfani da kafafen sada zumunta.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa a kwanan nan ne ma Shugaba Tinubu ya umarci hukumomin tsaro da su ƙarfafa matakan tsaron da ake bai wa dukkan ’yan takarar shugaban ƙasa da mataimakin shugaban ƙasa da gwamnoni da mataimakin gwamna gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Mai magana da yawun kwamitin ya kuma jaddada cewa duk wata barazana ga rayuwar ɗan ƙasar abu ne mai haɗari da ke buƙatar a ɗauki mataki ba tare da la’akari da siyasa ba, tare da kira ga Frank da ya gabatar da duk wata hujja da yake da ita ga hukumomin tsaro domin gudanar da bincike cikin gaggawa.
'Na amince da taron shugabannin Amurka, Rasha da China, amma ba don batun Ukraine ba'
Asalin hoton, Getty Images
Bayan rahotannin kafafen yaɗa labarai na Amurka cewa shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya ba da shawarar a gudanar da taro tsakanin shugabannin Rasha, Amurka da China domin tattauna makomar yaƙin Ukraine, shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya amince da irin wannan taro.
Sai dai Trump ya jaddada cewa babban abin da za a mayar da hankali a kai a taron shi ne rage makaman nukiliya, ba batun Ukraine ba.
Shugaban na Amurka ya kuma ce matsayar Rasha kan rikicin Ukraine ta kasance “abin da za a iya amincewa da ita.”
Rahoton da jaridar Wall Street Journal ta wallafa game da shawarar Putin ya janyo damuwa a ƙasashen Turai, tare da suka daga gwamnatin Kyiv ta Ukraine.
Har ila yau, Trump ya sake sukar shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, yana mai cewa watakila lokaci ya yi da wani daban zai wakilci Kyiv a tattaunawar sulhu.
Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa da muhawara tsakanin ƙasashen yammacin duniya game da hanyoyin kawo ƙarshen yaƙin da ya shafe shekaru ana yi a Ukraine.
'Yan gudun hijira daga yaƙin Yemen sun zarta 250,000 - MDD
Asalin hoton, Getty Images
Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanar a ranar Talata cewa fiye da mutane 250,000 sun tsere daga gidajensu sakamakon sabbin faɗace-faɗacen da suka sake ɓarkewa a Yemen.
Ƙungiyar ta nuna matuƙar damuwa kan halin da mutanen da suka nemi mafaka a birnin Taiz da kewaye ke ciki, tana mai gargadin cewa hanyoyin isa waɗannan yankuna sun kasance kusan a rufe gaba ɗaya.
Babban Kwamishinan Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da haƙƙin bil'adama, Volker Türk, ya ce ta hanyar rufe hanya ɗaya tilo da ke haɗa Taiz da Aden, mayaƙan Houthi sun hana kai agajin jin ƙai da kuma isar da muhimman kayayyaki ga al'ummar yankin, lamarin da ke jefa fararen hula cikin babban haɗari.
Ya yi kira ga mayaƙan Houthi da su gaggauta ba da damar shigar da kayan agaji zuwa Taiz.
Mista Türk ya kuma bayyana cewa an tabbatar da mutuwar fararen hula 32, ciki har da ƙananan yara 14 da mata 9 a sassan lardin.
Ya jaddada cewa halin da ake ciki a Taiz ya fi tayar da hankali, ganin cewa kusan rabin mutanen da rikicin ya raba da muhallansu a baya-bayan nan sun nemi mafaka ne a cikin birnin.
Mai shiga tsakanin Iran da Amurka Asim Munir ya isa Tehran
Asalin hoton, Getty Images
Babban kwamandan rundunar sojin Pakistan, Field Marshal Asim Munir, wanda kuma ke taka rawar shiga tsakani tsakanin Iran da Amurka, ya isa birnin Tehran tare da Ministan Harkokin Cikin Gida na Pakistan, Mohsin Naqvi.
Wannan ita ce ziyara ta hukuma ta biyar da kwamandan sojin Pakistan ya kai Tehran tun bayan fara tsagaita wuta.
A ziyararsa da ta gabata a ranar 2 ga Satumba, ya gana da:
Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian
Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Koli, Mohsen Rezaei
Kakakin Majalisar Dokoki, Mohammad Baqer Qalibaf
Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi
Ministan Harkokin Cikin Gida, Eskandar Momeni
Sa'a guda kafin isowar Mista Munir, kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmail Baghaei, ya bayyana a wani taron manema labarai cewa babban abin da za a mayar da hankali a tattaunawar shi ne "Ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu da kuma bunƙasa haɗin gwiwar da ke tsakaninsu."
Ana sa ran tattaunawar za ta mayar da hankali kan alaƙar Iran da Pakistan, haɗin kai a fannonin tsaro da tattalin arziki, da kuma sauran batutuwan da suka shafi yankin.
MDD ta buƙaci a bada damar shigar da kayan agaji Yemen
Asalin hoton, Getty Images
Babban kwamishinan Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da haƙƙin ɗan Adam, Volker Türk, ya yi kira da a ba da damar shigar da kayan agaji zuwa birnin Taiz na ƙasar Yemen, wanda mayakan Houthi da Iran ke marawa baya suka yi wa ƙawanya tsawon makonni.
A cikin wata sanarwa, Mista Türk ya yi gargadin cewa rayukan fararen hula na fuskantar babban haɗari, yayin da abinci, da man fetur da sauran muhimman kayayyaki ke ƙarewa cikin sauri.
A makon da ya gabata, Hukumar Abinci ta Duniya ta yi gargaɗin cewa wata mummunar matsalar jin ƙai na gab da afkawa birnin Taiz, wanda shi ne birni na uku mafi girma a Yemen.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce sama da mutane dubu dari biyu da hamsin ne suka bar gidajensu tun bayan da sabon rikici ya sake ɓarkewa a watan Agusta tsakanin sojojin gwamnati masu samun goyon bayan Saudiyya da kuma mayakan Houthi.
Birtaniya za ta tura jiragen yaƙi Saudiyya domin kare ta daga hare-haren Houthi
Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Birtaniya ta ce za ta tura jiragen yaƙin na RAF Typhoon zuwa Saudiyya domin taimakawa wajen kare ƙasar daga hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa da ƙungiyar Houthi ke kaiwa.
Gwamnatin ta ce wannan mataki zai taimaka wajen kare biranen Saudiyya da muhimman gine-ginen gwmanati daga hare-haren ƙungiyar wadda Iran ke mara wa baya ke kaiwa.
Firaministan Birtaniya, Andy Burnham, ne ya amince da wannan mataki bayan ƙaruwar hare-haren da 'yan Houthi suka kai, musamman a baya-bayan nan kan birnin Riyadh, da kuma wasu cibiyoyin makamashi da ke gabar tekun ƙasar.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, sakataren tsaro na Birtaniya, Wes Streeting, ya ce: “Waɗannan jirage za su yi aikin kariya ne kawai, kuma ba za su kai hare-haren ramuwar gayya kan 'yan Houthi ba.”
Ƙungiyar Houthis na yaƙi da gwamnatin Yemen da ƙasashen duniya suka amince da ita, wadda Saudiyya ke mara wa baya.
A shekarar 2014 ne Houthi suka ƙwace iko da babban birnin Yemen, Sanaa, bayan sun kori gwamnatin da ke kan mulki a lokacin.
Za a ci gaba da tattaunawar zaman lafiya tsakanin Amurka da Iran
Asalin hoton, Getty Images
Babban hafsan sojin Pakistan, kuma babban mai shiga tsakanin Iran da Amurka, Fil Marshal Asim Munir, ya isa birnin Tehran domin ci gaba da tattaunawa.
Wannan ita ce ziyara karo na biyar da ya kai Iran tun bayan kafa kwarya-kwaryar yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Yuni.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta ce babban abin da za a mayar da hankali a kai a tattaunawar shi ne ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu da kuma haɗin gwiwa a fannoni daban-daban.
Ƙoƙarin diflomasiyya na samar da mafita ta dindindin ga yaƙin dai na fuskantar cikas, inda tattaunawar ta tsaya cik kan muhimman batutuwa da suka haɗa da makomar mashigar Hormuz.
A ranar Talata, farashin manyan kwangilolin man fetur na Amurka da kuma ma’aunin farashin mai na duniya ya yi tashin gwauron zabi a kasuwanni.
Iran ta ce ta tarwatsa jiragen ruwa biyu da suka keta mashigar Hormuz
Asalin hoton, Reuters
Rundunar juyin juya halin Iran ta ce wasu jiragen ruwan dakon kaya biyu tarwatse bayan taka nakiya a mashigar Hormuz.
IRGC ta bayyana jiragen da ''waɗanda suka karya doka''.
A cikin wata sanarwa, rundunar ta ce jiragen sun taka nakiyoyin da rundunar ruwanta ta dasa a cikin ruwa.
Rundunar ruwan ta IRGC ta kuma yi gargaɗin cewa "ƙetare hanyar da aka girke bam-baman ruwa a cikinta babban laifi ne, kuma ba zai haifar da komai ba face lalata kadarorin waɗanda suka karya dokar."
Sai dai hukumomi masu zaman kansu da ke sanya ido kan tsaron zirga-zirgar jiragen ruwa, ciki har da Hukumar Kula da Tsaron Jiragen Ruwa ta Kasuwanci ta Birtaniya (UKMTO), ba su tabbatar da aukuwar fashewar ba a nasu bincike.
Duk da haka, tsanantar rikicin da ke tsakanin 'yan tawayen Houthi da Saudiyya, da kuma ci gaba da kai hare-hare kan jiragen ruwa a mashigar Hormuz, sun janyo hauhawar farashin mai a kasuwannin duniya.
A safiyar yau, farashin gangar danyen mai na Brent ya haura dala 111 a karon farko cikin watanni biyar yayin fara harkokin ciniki.
Ƙasurguman Kachalloli biyu da suka mutu a faɗan ƴanbindiga a Zamfara
Asalin hoton, OTHERS
Rahotanni daga Jihar Zamfara da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya na cewa wani mummunan faɗa da ya ɓarke tsakanin ƙungiyoyin ƴanbinga ya yi sanadin kashe wasu daga cikin manyan jagororinsu.
Mannir Fura Girke ɗan jarida ne mai bincike kan ayyukkan ƴan fashin daji a arewacin Najeriya ya shaidawa BBC cewa faɗan ya samo asali ne sakamakon ɗaukar fansa.
''A kwanakin baya ne wasu ƴanbindiga ƙarƙashin jagorancin Kachalla Dogo Baldu suka kai hari dabar Kachalla Alhaji Mu'azu a dajin Dausayi da ke jihar Katsina, inda suka kashe shi tare da yaransa bakwai'', in ji Fura Girke.
Mai binciken kan ayyukan ƴanbindiga ya ce Kachalla Alhaji Mu'azu ɗaya ne daga cikin manyan yaran ƙasurgumin ɗan fashin dajin nan Ado Aleiro, wanda ya yi kaurin suna a ayyukan fashin daji.
''To bayan kwanaki da wannan kisa ne sai ɓangaren Ado Aleiro suka ƙudiri aniyar ɗaukar fansa kan Dogo Baldu da yaransa'', in ji shi.
Ya ci gaba da cewa wannan ne ya sa ɓangaren Ado Aleiro da yaran sa suka kai hari gidan Dogo baldu da ke ƙauyen Mai Galma a jihar Zamfara, suka kuma kashe shi tare da yaransa uku.
Za a fara tattaunawa domin sasanta Zelensky da Trump a Norway
Asalin hoton, Getty Images
Wakilin musamman na Amurka, Steve Witkoff, ya isa Norway domin tattaunawa da shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, a daidai lokacin da dangantaka tsakanin shugaban na Ukraine da shugaban Amurka, Donald Trump, ke ci gaba da tsami.
Firaministan Norway, Jonas Gahr Støre, ya ce Zelensky ne ya nemi Norway da makwabciyarta Finland su shirya taron da zai haɗa Ukraine da Amurka da kuma ƙawayenta na Turai.
Kafin taron, Ministan Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya yi watsi da zarge-zargen cewa Ukrainawa na mutuwa saboda Amurka na hana Kyiv bayanan sirri na soja.
Kalaman nasa na zuwa ne bayan mai ba wa rundunar sojin Ukraine shawara kan harkokin fasaha, Serhii Beskrestnov, ya shaida wa BBC cewa rashin samun gargaɗin hare-hare daga Amurka a kai a kai na janyo asarar rayuka.
Dangantaka tsakanin Kyiv da Washington ta yi tsami a ƴan makonnin nan, har shugaban Amurka Donald Trump ya ce lokaci ya yi da Ukraine za ta samu sabon shugaba, ko kuma wani daban ya jagoranci tattaunawa a madadinta.
Sai dai Firaministan Norway ya ce manufar taron Oslo ita ce mayar da dangantakar bangarorin kan hanya mai kyau da kuma taimakawa wajen kaiwa ga ƙarshen yaƙin ta hanyar diflomasiyya domin samar da zaman lafiya mai ɗorewa da adalci.
Zelensky ya ce shi ma ya yi tattaunawa mai amfani da Rubio kan buƙatar samun gargaɗin hare-hare da wuri, makaman kariya daga makamai masu linzami, da kuma sabis na intanet na Starlink.
A shirye muke mu mayar da martani kan duk wani harin Amurka
Asalin hoton, RAHBAR.IR
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghaei, ya ce ƙasarsa ba za ta bar duk wani hari da aka kai mata ba tare da mayar da martani ba.
Kalaman nasa na zuwa ne bayan rahotannin da ke cewa Amurka ta aika wa Iran saƙo tana gargaɗinta kada ta mayar da martani idan an kai hari kan cibiyar Koh-e-Kalang.
Da yake magana kan batun, Baghaei ya ce Iran ta riga ta nuna a aikace cewa ba ta barin hare-haren da ake kai mata ba tare da mayar da martani ba. Ya ƙara da cewa ko da martanin Iran bai fi ƙarfin harin da aka kai mata ba, to za ta tabbatar da cewa ta rama abin da aka yi mata.
Jami’in na Iran ya kuma yi watsi da ikirarin cewa Amurka za ta iya kai hari kan Koh-e-Kalang ba tare da fuskantar martani daga Tehran ba. A cewarsa, wannan hasashe ne kawai, yana mai cewa "zamanin barazana ya wuce."
Kalaman Baghaei na zuwa ne bayan da shugaban Amurka, Donald Trump, ya sake yin barazanar kai hari kan cibiyar Koh-e-Kalang. Cibiyar tana kusa da wurin sarrafa makamashin nukiliya na Natanz, kuma Iran ta ce ana amfani da ita wajen ƙerawa da haɗa sabbin na’urorin haɗa makamai.
DSS ta gurfanar da mutum biyar kan zargin sace ƴan NYSC a Imo
Asalin hoton, CHANNELS
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta Najeriya (DSS) ta gurfanar da wasu mutum biyar da ake zargi da hannu a sace wasu masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) 20 da wani farar hula a jihar Imo.
An gurfanar da waɗanda ake zargin a babbar kotun jihar Imo da ke Owerri bayan kama su a wasu samame da jami'an tsaro suka gudanar bisa bayanan sirri a jihohin Rivers da Abia.
An sace matasan masu yi wa ƙasa hidimar da farar hular ne a ranar 1 ga Oktoban 2026 a kusa da Umunoha da ke ƙaramar hukumar Mbaitoli, yayin da suke kan hanyarsu daga Ibadan zuwa sansanonin horaswa na NYSC a jihohin Abia da Akwa Ibom.
Lamarin da ya sa jami'an tsaro suka kaddamar da wani samame, inda aka ceto mutanen 21 a ranar 7 ga Oktoba daga dajin Amakohia-Ubi da ke ƙaramar hukumar Owerri ta Yamma.
Daga baya DSS ta ce ta kama mutum biyar tsakanin 10 da 14 ga Oktoba a Port Harcourt da Aba, waɗanda yanzu haka suke fuskantar shari'a.
Me ya janyo rikici tsakanin Kwankwaso da ADC?
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon
Yayin da ake ta tattaunawa kan yiwuwar haɗakar manyan ƴan'adawa gabanin zaɓen 2027, rikici tsakanin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na NDC da kuma jam'iyyar ADC na ci gaba da aza ayar tambaya kan fatan haɗewar.
Mun yi bayani game da wannan lamari.
Ethiopia ta gargaɗi Eritrea kan goyon bayan ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai
Asalin hoton, Getty Images
Firaministan Habasha, Abiy Ahmed, ya yi gargaɗi Eritrea cewa za ta fuskanci mummunan sakamako idan ta ci gaba da goyon bayan ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai a Habasha. A wata hira da ya yi da gidan talabijin na gwamnati cikin harshen Tigrinya, ya ce Eritrea wata hanya da da maƙiyan Habasha ke amfani da ita.
Kalaman nasa na zuwa ne a lokacin da dangantakar Habasha da Eritrea ke ci gaba da tsami. Habasha na zargin Eritrea da tallafa wa ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai da kuma hannu a rikicin arewacin ƙasar, zarge-zargen da Eritrea ke musantawa.
A ranar 1 ga Oktoban 2026, Habasha ta sanar da rufe ofishin jakadancinta da ke Asmara tare da korar jami'an diflomasiyyar Eritrea 10.
Eritrea ta mayar da martani da irin wannan mataki, inda ta sanar da katse hulɗar diflomasiyya da Habasha. Hakan ya ƙara fito da girman rikicin da ke tsakanin ƙasashen biyu.
A hirarsa ta baya-bayan nan, Abiy Ahmed ya ce ƙasashen da ke mara wa Eritrea baya ba za su iya kare ta daga matakan da za su iya ɗauka ba.
Ya kuma zargi gwamnatin Eritrea da yin watsi da ci gaba da gina cibiyoyi, yana mai cewa hakan ne ya haddasa matsalolin tattalin arziki da ƙasar ke fuskanta.
Sai dai Eritrea ba ta yi martani kan waɗannan sabbin kalamai ba.
Ba na goyon bayan sake zaɓen Netanyahu - Vance
Asalin hoton, Getty Images
Mataimakin shugaban Amurka, J.D. Vance, ya ƙi bayyana ko yana goyon bayan Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, gabanin zaɓen ƙasar, duk da cewa Shugaba Donald Trump ya nuna goyon bayansa gare shi.
A wata hira da kafar yaɗa labarai ta intanet, Vance ya ce ba ya son tsoma baki a zaɓen Isra'ila. Ya ce hankalinsa ya fi karkata kan siyasar Amurka da kuma zaɓukan tsakiyar wa'adin mulki da ke tafe.
Vance, wanda ya taba ziyartar Budapest a lokacin zaɓen Hungary inda ya nuna goyon baya ga Viktor Orbán, ya ce yana goyon bayan ƴan takarar Amurka ne, ba na wasu ƙasashe ba.
Ya ce, "Ba na adawa da sake zaɓen Netanyahu, amma kuma ba na goyon bayan sake zaɓensa. Ba na son tsoma baki a zaɓen Isra'ila."
Ana sa ran za a gudanar da zaɓen Isra'ila a mako mai zuwa. Wannan shi ne zaɓe na farko da ƙasar za ta yi tun bayan harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga Oktoba.
Jihohi 7 da Tinubu zai fi fuskantar ƙalubale a zaɓen 2027
Asalin hoton, Getty Images
Yayin da zaɓen shugaban Najeriya na shekarar 2027 ke ƙara matsowa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu na fuskantar ƙalubalen siyasa a wasu jihohi da ka iya zama masa tarnaki, yayin da yake neman samun nasara domin yin wa'adi na biyu a zaɓen mai zuwa.
Ko da yake jam'iyyar APC mai mulki ta ƙara faɗaɗa tasirinta a siyasar ƙasar, wasu jihohi na iya zama ƙalubale ga Tinubu, musamman idan aka yi la'akari da tarihin siyasarsu, matsalolin da suke fuskanta da dai sauransu.
Wani rahoto na Cibiyar Nazarin Zaɓe ta International Republican Institute (IRI) ya bayyana cewa matsin tattalin arziki, rashin tsaro da rashin amincewar jama'a ga 'yan siyasa na daga cikin manyan abubuwan da za su iya tantance yadda zaɓen 2027 zai kasance.
Farfesa Abubakar Kari, masanin harkokin siyasa kuma malami a Jami'ar Abuja da ke Najeriya, ya yi tsokaci kan waɗannan jihohi da kuma dalilan da za su iya sa Shugaba Tinubu ya fuskanci ƙalubale a cikinsu.