KAI TSAYE , Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Talata 10/11/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Talata 10/11/2026

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. China ta kai wani sabon matsayi a tarihin kasuwanci

    Xi Jinping

    Sabbin alƙaluman gwamnati sun nuna cewa China na dab da kafa wani sabon tarihin cinikayya a wannan shekarar, inda ƙasar ta samu rarar kasuwancin da ya kai dala tiriliyan ɗaya zuwa watan Oktoba.

    Wannan na zuwa ne sakamakon ƙaruwar buƙatar kayayyakin da ke da alaƙa da fasahar ƙirƙirarriyar basira ta AI a kasuwannin ƙasashen waje.

    Haka kuma, fitar da kayayyakin China zuwa Amurka ya ƙaru da kusan kashi ɗaya bisa uku a watan da ya gabata.

    Sai dai waɗannan alƙaluma na iya ƙara fin hakan saboda kasuwanci da ke tsakanin China da abokan hulɗarta.

  2. Da alama yaƙin Iran ya kusa zuwa ƙarshe - Trump

    ..

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ba lallai ba ne Amurka ta sake kai hare-hare kan Iran.

    Da yake magana a Fadar White House bayan jam’iyyarsa ta sha mummunar kaye a zaɓen tsakiyar wa’adi, Trump ya bayyana cewa Iran ta riga ta zama ƙasa da aka raunana sosai ta fuskar ƙarfin soji, yana mai cewa akwai kyakkyawan yanayi na cimma yarjejeniya da za ta kawo ƙarshen yaƙin.

    Ba wannan ne karon farko da Donald Trump ke cewa an raunana Iran ta fuskar ƙarfin soji ba, tare da bayyana cewa yana sa ran yaƙin zai kawo ƙarshe nan ba da jimawa ba.

    Sai dai a wannan karon, yanayin da Trump ke ciki ya bambanta da yadda al'amura suke a baya.

    A ɓangare guda kuma, Trump ya sake nuna goyon bayansa ga Sakataren Tsaronsa, Pete Hegseth, bayan wani ɗan majalisar dokoki daga jam’iyyar Republican, Thomas Massie, ya gabatar da ƙudirin tsige shi.

  3. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Talata.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da ake ciki.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa