Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala Umarah a Saudiyya

Asalin hoton, Bola Tinubu/X
Shugabna Najeriya, Bola Tinubu ya koma ƙasar bayan kammala ziyarar Umara zuwa Saudiyya.
Jirgin shugaban ƙasar ya sauka a filin jirgin saman Abuja, babban birnin ƙasar ranar Laraba da daddare.
A makon da ya gabata ne shugaban Najeriya ya tafi ziyarar ibadar zuwa Saudiyya.
A lokacin ziyarar shugaban ya samu damar shiga ɗakin Ka'abar.

