KAI TSAYE , Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 09/11/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin, 09/11/2026

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Shugaba Tinubu
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Ƴar Arewan da ke buga wa Najeriya ƙwallo
  • waya
  • Gwamna Adeleke na Accord
  • Jihohi masu talauci
  • Buba Galadima
  • Dattijuwa

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Sabuwar rundunar killace Iran ta ƙasa ta fara aiki - Trump

    Najeriya

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce wata sabuwar runduna ta musamman da aka kafa domin killace iyakokin ƙasar Iran ta ƙasa ta fara aiki gaba ɗaya.

    An ƙirƙiri rundunar ne domin datse hanyoyin shiga Iran da sojojin Amurka ke zargin ana amfani da su wajen safarar makamai da sauran haramtattun kayayyaki.

    Tun da farko, Amurka ta riga ta ƙaƙaba wa Iran wani shamakin ruwa, wanda ta ce ya taƙaita yawan kuɗin da Tehran ke samu daga fitar da ɗanyen man fetur zuwa dala biliyan 25.

    Sai dai Iran ta ce sabon matakin ba zai yi nasara ba, kuma ba zai haifar da durƙushewar tattalin arzikin ƙasar ba.

  2. Sallama

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Litinin.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniyar ke ciki.

    Kuna iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta.