Za a amince da kafa ƴansandan jihohi nan da watan Disamba - Majalisar dattawa

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawan Najeriya, Opeyemi Bamidele, ya bayar da tabbacin cewa za a kammala shirin kafa ƴansandan jihohi kafin ko a cikin watan Disamban 2026.
Da yake magana kan ƙudirin a ranar Alhamis, Bamidele, wanda kuma shi ne Mataimakin Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan yi wa Kundin Tsarin Mulki na 1999 gyaran fuska, ya bayyana muhimmancin wannan ci gaba na tarihi, kamar yadda jaridar DailyTrust ta ruwaito.
Ya ce amincewar majalisun jihohi kusan 30 ta cika sharaɗin buƙatar samun goyon bayan kashi biyu bisa uku na jihohin ƙasar kamar yadda Sashe na 9(2) na Kundin Tsarin Mulki na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) ya tanada.
Da yake bayyana matakai na gaba a majalisa, Shugaban masu rinjayen ya ce abin da ya rage yanzu matakai ne na gudanarwa amma masu matuƙar muhimmanci.
A cewarsa, Majalisar Dokoki ta Ƙasa za ta tattara rahotannin majalisun dokokin jihohin a hukumance, sannan majalisun biyu su amince da ƙudirin da rinjayen kuri'u, kafin a miƙa shi ga Shugaban Ƙasa domin sanya hannu.
Ana sa ran kammala wannan tsari kafin ko zuwa watan Disamban 2026.

















