Gasar wasan Polo da masu ninƙaya a cikin hotunan Afrika

An wallafa

Wasu daga cikin ƙayatattun hotunan Afrika na wannan mako daga 22-28 ga Satumba.

.
Bayanan hoto, A ranar Lahadi aka gudanar da gasar ninƙaya ta kilomita biyar tsakanin Dakar babban birnin ƙasar Sinigal da Tsibirin Goree.
.
Bayanan hoto, Ƴar Afirika ta Kudu mai goyon bayan wasan zari ruga.
.
Bayanan hoto, Mawaƙan Addinin Kirista na rera waƙoƙi a yayin bukin ranar Meskel a Ƙasar Habasha.
.
Bayanan hoto, Mabiya Addinin Kirista na gaisawa da juna cikin farin ciki a lokacin hutun bukin na Meskel a Habasha.
.
Bayanan hoto, Yadda girgizar ƙasa ta rusa birnin Tamazirt na ƙasar Moroko a farkon watan Satumba.
.
Bayanan hoto, A ranar litinin ruwan sama mai karfi tare da iska ya mamaye birnin Cape Town na ƙasar Afirika ta Kudu
.
Bayanan hoto, Magoya bayan ƴar takarar Majalisar Wakilai a ƙasar Eswatini yayin da suke cashewa ranar Laraba a Siphofaneni.
.
Bayanan hoto, Gangamin yaƙin neman zaɓen Nomalungelo Simelane ƴar fafutukar kafa mulkin dimukuraɗiyya bayan an haramtawa ƴan siyasa kafa jam'iyyu a ƙasar
.
Bayanan hoto, Ƙungiyar Wasan Polo ta Nairobi ta shirya wasan cin kofin Casino wanda za a fafata har tsawon kwanaki uku tsakanin ƙwararru.
.
Bayanan hoto, Wannan ce tsohuwar ƙungiyar ƴan wasan Polo a Gabashin Afirika, ana shirya gasa daban-daban kowacce shekara.
.
Bayanan hoto, Al'ummar birnin Kairouan na ƙasar Tunisiya sun yi dandazo a masallaci don gudanar da Maulidi.
.
Bayanan hoto, Wani Uba da ɗansa yayin da al'ummar Musulmi a ƙasar Masar suke gudanar da Mauludi a Cairo babban birnin ƙasar.
.
Bayanan hoto, Jama'a na ci gaba da zanga-zangar tsadar rayuwa da yawaitar cin hanci tsakanin wasu jami'an gwamnati a Ghana.