Me INEC ta ce kan mayar da sunayen Pantami da Gwarzo?

Pantami da Gwarzo
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

A ranar Alhamis ne hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta tabbatar da warware ƙorafe-ƙorafen da wasu jam'iyyun da ƴantakarar gwamna suka shigar mata, inda yanzu suke da damar shiga takarar 2027.

Sai dai har yanzu INEC ba ta fitar da jerin sunayen ƴantarar da ta tantance ɗin ba, kuma ba ta tuntuɓi ƴantakarar ba, kamar yadda wasu daga cikinsu suka shaida wa BBC.

Tun da farko a ranar 10 ga watan Oktoban da muke ciki ne hukumar INEC ta fitar da jerin sunayen ƴantakarar gwamna a faɗin jihohin ƙasar, inda wasu jam'iyyun suka koka kan rashin ganin sunayen ƴantakararsu na kujeru daban-daban.

Cikin wata sanarwa da hukumar zaɓen ta fitar a ranar Alhamis ta ce ta samu ƙorafe-ƙorafe fiye da 60 tun bayan fitar da sunayen ƴantakara gwamna.

Me INEC ta ce a sanawar?

Cikin sanarwar da shugaban sashen yaɗa labarai da wayar da kan masu zaɓe, Mohammed Kudu Haruna ya fitar ya ce bayan nazarin ƙorafe-ƙorafen da jam'iyyun suka shigar da kuma hukunce-hukuncen da kotuna suka yanke, hukumar ta samu hujjar saka wasu sunayen.

''Yayin da muka yi watsi da ƙorafe-ƙorafen da muka gaza samun gamsassun hujjoji a kansu'', in ji shi.

INEC ta kuma ce ta cire wasu sunayen da aka saka tun da farko bayan gano an yi kuskuren saka su.

''A taƙaice dai mun samu ƙorafi 69 kan haka, daga jam'iyyu 12 a faɗin jihohi 26 kan takarar gwamna, inda muka warware ƙorafi 41 tare da yin watsi da 26'', a cewar hukumar zaɓen.

INEC ta ce nan ba da jimawa ba za a shigar da sunayen jam'iyyu da ƴantakarar da abin ya shafa a ofisohinta na jihohin da abin da ya shafa.

Me INEC ta ce kan takarar Pantami da Gwarzo

A sanarwar da hukumar zaɓen ta fitar, ba ta fito ƙarara ta bayyana sunayen mutanen da ta ce ta mayar da su ba.

Haka kuma ba ta bayyana sunayen ƴantakarar da aka tabbatar da cire sunayensu daga cikin waɗanda za su yi takara ba.

Abin da kawai ta ce shine ta samu nasarar warware ƙorafe-ƙorafen wasu ƴantakara 41.

Hukumar zaɓen ta kuma ce nan ba da jimawa ba za a shigar da sunayen jam'iyyu da ƴantakarar da abin ya shafa a ofisohinta na jihohin da abin da ya shafa.

Mun dai yi ƙoƙarin tuntuɓar hukumar zaɓen don jin sunayen yantakatar da suka samu nasarar shiga masu yin takara a 2027, amma

Abin da ɓangarorin biyu suka ce

Pantami
Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ɓangarorin biyu sun ce har yanzu hukumar INEC ba ta tuntuɓe su kan batun mayar da sunayen ƴantakarar tasu ba.

Kakakin jam'iyyar PDP na jihar Gombe, Abdulkadir Ahmad Dukku ya shaida wa BBC cewa har zuwa lokacin haɗa wannan labari a safoyar Juma'a INEC ba ta tuntuɓe su domin sanar da su matsayarta kan ɗantakarsu a hukumance ba.

''Zuwa yanzu INEC ba ta tuntuɓe mu ba, amma dai ta ce mana nan ba ta jimawa ba sahen shari'a na hukumar zai fitar da cikakkun sunayen ƴantakarar da ya wanke ɗin'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa tun bayan sanarwar ya tuntuɓi shalwatar jam'iyyar ta ƙasa domin jin ko INEC ɗin ta ba su sanarwa a hukumance game da hakan, amma kuma ba su samu hakan ba.

A nasa ɓangare shi ma ɗantakarar gwamnan jihar Kano na jam'iyyar NDC, Aminu Abdussalam Gwarzo bai samu saƙon INEC a hukumance ba da ke nuna cewa an mayar da sunansa.

A hirarsa da BBC kakiakin Kwankwasiyya na Najeriya, Habibu Sale Mailemo ya ce zuwa yanzu suna jiran INEC ɗin ta fitar da sunayen ƴantakarar kuma suna da fatan ganin sunan ɗantakararsu.

''INEC ta ce ba ta da masatala da mu ta fuskar cancanta, ko rashin sunan ɗantakararmu a rajistar ƴan jam'iyya'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa har yanzu babu wata takarda daga INEC a hukumance da ke nuna mayar da sunayen ƴantakarsu.

''Ai dama INEC sake nazarin ƙorafe-korafe ta yi, ta faɗi matsayarta, sannan ta ce za ta fitar da sunayen a ofisoshinsu, kuma za mu ci gaba da bibiyar shafukansu don ganin ko za su fitar da sunayen'', in ji shi.