Gasar Afcon da ziyarar shugabar Tanzania zuwa Indonesia cikin hotunan Afirka

An wallafa

Ƙayatattun zaɓaɓɓun hotunan Afirka da na 'yan nahiyar a wasu sassan duniya na wannan mako

.
Bayanan hoto, Magoya baya sun yi dandazo a filin wasan ƙwallon ƙafa na Laurent Pokou da ke ƙasar Ivory Coast ranar Lahadi don kallon yadda aka fafata tsakanin Morocco da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Congo a gasar cin kofin Afrika.
.
Bayanan hoto, Kashegari, Najeriya ta lallasa Guinea-Bissau a gasar inda ta tsallaka zuwa zagayen gaba a gasar
.
Bayanan hoto, A ranar Litin ne, 'yan wasan Dogon suka cashe lokacin rawar Ogobagna a Bamako babban birnin 'kasar Mali.
.
Bayanan hoto, An nuna kayan tarihin Masar yayin baje-kolin abubuwan al'ajabi ta hanyar amfani da haske a birnin Paris na ƙasar Faransa ranar Alhamis.
.
Bayanan hoto, Ma'aikata na ƙirƙirar mutum-mutumi a Arewacin ƙasar Masar, ranar Asabar.
.
Bayanan hoto, Hotuna a kasuwar kayan masana'antu da ke titin Buganda, a Kampala babban birnin Uganda.
.
Bayanan hoto, Mabiya na dakon lokacin fara bukin Timket a ƙasar Ethiopia ranar Asabar.
.
Bayanan hoto, Mabiya addinin Kirista na gudanar da bukukuwan tunawa da muhimman ranaku cikin kogin Jordan.
.
Bayanan hoto, Ranar Alhamis dakarun Indonesia sun yi wa shugabar ƙasar Tanzania gaisuwar girmamawa yayin da ta ziyarci shugaban ƙasar Joko Widodo