’Yan bindiga sun kashe Sheikh Yahaya Masussuka - ‘Yansanda

Asalin hoton, Sheikh Yahya Masussuka/FB
Rundunar ‘yansandan Najeriya reshen jihar Katsina ta tabbatar da kisan sanannen malamin addinin Musulunci Sheikh Yahya Masussuka a gidansa da ke yankin Dutsen-Ma.
A wata tattaunawa da BBC, baturen ‘yansanda reshen Dutsen-Ma ya bayyana cewa wasu ‘yan bindiga ne suka kashe mashahurin malamin da yammacin Litinin a kofar gidansa.
CSP Auwalu Gwadabe ya ce malamin ya rasu ne sanadiyyar raunuka na harbin bindiga bayan an kai shi asibiti.
Haka nan sakataren malamin, Dr Mustapha Haruna ya tabbatar da rasuwar Masussuka a babban asibitin Dutsen-Ma
Kafin kisan nasa, Sheikh Masussuka na daga cikin malaman addinin Musulunci wadanda koyarwarsu ke haifar da cece-ku-ce a arewacin Najeriya da kasashe masu makwaftaka.
Malaman Musulunci da dama na sukar shi saboda akidarsa ta rashin yarda da hadisan Annabi Muhammad, inda yake danganta duk wata koyarwarsa ga Alqur’ani.
Za mu kawo muku karin bayani…





















