Wasu daga cikin kayatattun hotunan Afrika na wannan mako

An wallafa

Wasu zaɓaɓɓun hotunan Afrika da wasu nahiyoyi na wannan mako

.
Bayanan hoto, Nan, mata ne ke bikin murnar zagayowar ranar samun yancin kai a Eriteria a ranar Laraba, wanda ya kawo karshen yaƙi tsakanin ƙasar da Habasha na tsawon shekara 30.
A woman in Abidjan, Ivory Coast, carries an impressive number of water bottles on her head on Tuesday.
Bayanan hoto, Wata mata a Abidjan, babban birnin Ivory Coast, ɗauke da gororin ruwa a kanta a ranar Talata.
MICHELE SPATARI/ AFP
Bayanan hoto, A can garin Hammanskraal da ke Afrika ta Kudu kuwa, wani mutum ne aka a saman tankar ruwa domin cika ta da ruwa a ranar Talata, yayin da aka gargaɗi mazauna garin da cewa kada su sha ruwan famfo bayan ɓarkewar cutar kwalara.
J. COUNTESS/ GETTY IMAGES
Bayanan hoto, Shugaba Isaias Afewerki na Eritrea cike da murna a bikin tunawa da samun ƴancin kan ƙasarsa. Ƙasar Habasha ta mamaye ƙasar a shekarar 1962, amma dakarunta sun sake kwace iko da babban birnin ƙasar a shekarar 1991, inda daga karshe suka kaɗa kuri'ar samun ‘yancin kai a shekarar 1993.
BENOIT DOPPAGNE/ AFP
Bayanan hoto, Nan, hoton wata mata ce 'yar ƙasar Senegal aka ɗauka a wurin buɗe wani katafaren kamfani haɗa siminti a Dakar.
SAMUEL ALABI/ AFP
Bayanan hoto, Mai martaba Sarkin Kano (a ɓangaren hagu) da Ooni na Ife a lokacin da suka halarci bikin buɗe katafaren matatar mai ta Aliko Dangote a birnin Legas tare kuma da shugaba Muhammadu Buhari.
MUHAMADOU BITTAYE/ AFP
Bayanan hoto, A can Senegal kuwa, masu zanga-zanga ne suka tare hanyar zuwa gidan madugun 'yan adawan ƙasar Ousmane Sonko, domin hana yunkurin kama shi a ranar Litinin. Ana tuhumar sa da laifin fyaɗe, abin da ya musanta.
HECTOR VIVAS/ GETTY IMAGES
Bayanan hoto, Wasu magoya bayan Masoyan kwallon kafa na ƙasar Senegal a Argentina, sun yi murna ga tawagarsu a wasan da suka fafata da Japan a gasar cin Kofin Duniya ta 'yan ƙasa da shekara 20 a ranar Lahadi - wanda Japan ta ci 1-0.
BRIAN LAWLESS/PA WIRE
Bayanan hoto, Ƴan Afrika ta Kudu Tina Sekete da Jane Dlamini cikin murmushi yayin da suke ɗaukar hoto a ranar Afrika ta Dublin a ranar Alhamis. Ma'aikatar Harkokin Waje ta Ireland tana shirya bukukuwa a kowace shekara a ranar 25 ga watan Mayu don bikin jama'a da al'adun nahiyar.
.
Bayanan hoto, Wasu mata kenan lokacin da suka halarci wani fareti a ranar Asabar a Algiers babban birnin ƙasar Aljeriya domin murnar cika shekaru 50 da kafa kungiyar Polisario. Kungiyar dai na fafutukar ƙwato 'yancin kan yankin yammacin Sahara. A halin yanzu Maroko tana iko da kusan kashi 80 na yankin kuma sauran na hannun Polisario.
.
Bayanan hoto, Nan, masu gadin gidan yari ne a Zimbabwe ke bakin aiki a gidan yari a Harare a ranar Juma'a, lokacin da hukumomi suka saki kusan kashi biyar na dukkan fursunoni karkashin umarnin afuwar da shugaban ƙasar ya bayar, da nufin rage cunkoso a gidajen yarin ƙasar.
.
Bayanan hoto, An haska wuta a mai kyalli a sararin samaniyar a birnin Rabat na ƙasar Maroko, a daidai lokacin da ake kawo karshen wani taro a Rabat, da ta kasance hedkwatar al'adun Afrika na tsawon shekara guda.
.
Bayanan hoto, A nan, maza ne daga yankin kudu da hamadar sahara ke jiran sauka daga wani jirgin ruwa a tsibirin Canary - bayan da jami'an tsaron gaɓar ruwan Sifaniya suka ɗauki bakin haure 138 da ke cikin kwale-kwalen a ranar Talata.