Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Real Madrid na harin Calafiori, Tottenham na son Romero
Real Madrid na son ganin ta siyo É—an wasan Arsenal da Italiya Riccardo Calafiori, da ya taka leda a hannun Jose Mourinho a Roma. (Sky Sports)
Tottenham na duba yiwuwar siyo dan wasan Juventus da Brazil Gleison Bremer, don maye gurbin dan wasan ƙungiyar Cristian Romero, da kuma ƙara inganta tsaron bayan kungiyar. (Tuttosport - in Italian)
Manchester United ba su da ra'ayin É—auko Romero daga Tottenham , amma suna son É—aukar É—an wasan Newcastle Lewis Hall. (Teamtalk)
Daya daga cikin mamallakan ƙungiyar Sir Jim Ratcliffe na son amincewa da buƙatar ɗan wasan Nottengham Forest Elliot Anderson domin ganin sun kawo shi Manchester United. (Mirror)
Manchester City ce kan gaba cikin ƙungiyoyin da ke son ɗaukar Anderson duk da yunƙurin United na ganin sun shammace ta wajen siye ɗan wasan. (Star - subscription required)
Sabon mai horar da Æ´an wasan Real Madrid Jose Mourinho na harin É—an wasan West Ham Mateus Fernandes da ke son komawa Chelsea. (AS - in Spanish)
Manchester United har ila yau na duba yiwuwar siyar da Fernandes ga West Ham, kan Fam miliyan 80, sai dai United din ba gaggawa suke ba wajen siyar da Fernandes . (Sky Sports)
Manchester United na duba yiwuwar bayar da wani mamaki na ɗauko mai tsaron ragar Leeds Karl Darlow, da kwantaraginsa ta ƙare da ƙungiyar, a wannan kaka, yayin da mai tsaron ragar United ɗin ke shuirin barin Old trafford ɗin. (Talksport)
Fulham na harin É—an wasan Najeriya Samuel Chukwueze daga AC Milan sakamakon tsawon lokacin da ya dauka a mastyin É—an wasan Aro a Craven Cottage, sai dai suna ci gaba da tattaunawa wajen biyan kuÉ—i kaÉ—an. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Atletico Madrid na sa ran siyen É—an wasan Manchester City Bernando Silva maimakon Barcelona ko Real Madirid saboda za su iya bai wa É—an wasan na Portugal isasshen lokacin taka leda. (Marca - in Spanish)
Fulham na duba yiwuwar É—auko mai hororar da Æ´an wasan Ipswich Kieran McKenna, wanda ke kan gaba a jerin waÉ—an da suke son É—auka don maye gurbin Marco Silva. (Talksport)
Leicester na tattaunawa da tsohuwar ƙungiyar mai horar da ƴan wasan Southampton da Rangers Russell Martin kan yiwuwar komawarsa ƙungiyar sakamakon rasa gurbin buga Firimiya, inda suka koma buga League One. (Leicester Mercury)