Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ana jimamin faston da ya mutu a coci bayan kuros ya faɗo masa a kai
- Marubuci, Redacción
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Mundo
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 3
Wani fasto ɗan shekara 53 ya rasu bayan wani babban kuros na katako ya faɗo masa a kai yayin da yake jagorantar ibada a wata coci da ke birnin Guayaquil na ƙasar Ecuador.
Lamarin ya faru ne a Cocin Our Lady of Perpetual Help da ke tsakiyar birnin a ranar Asabar, lokacin da Fasto Patricio Alfredo Sánchez Molinari ke gudanar da ibada.
Rahotanni sun ce faston na tsaye a gaban jama'a yana jagorantar ibadar ne lokacin da kuros ɗin ya kuɓuce daga inda aka kafa shi, sannan ya faɗo kai tsaye a kansa.
Nan take faston ya faɗi ƙasa cikin mamakin masu ibadar da kuma waɗanda ke kallon ibadar kai tsaye a shafukan sada zumunta.
Da dare a ranar Asabar, babban cocin Katolika na Guayaquil ya tabbatar da rasuwarsa tare da miƙa godiya ga waɗanda suka aike da saƙonnin ta'aziyya da kuma addu'o'i.
Mutuwar faston ta jefa mabiya cocin da ma al'ummar yankin cikin alhini, inda mutane da dama suka bayyana kaɗuwarsu da baƙin cikinsu kan wannan lamari da ya faru ba zato ba tsammani.
A wata sanarwa da ya fitar, babban cocin Katolika na Guayaquil ya ce:
"Muna godiya da dukkan saƙonnin ta'aziyya da muka samu daga sassa daban-daban na duniya, musamman addu'o'in da ake yi domin Allah Ya jikan Fasto Patricio Sánchez."
A ranar Lahadi kuma, Archbishop na Guayaquil, Cardinal Luis Cabrera, ya jagoranci taron addu'a na musamman a cocin da lamarin ya faru domin karrama marigayin.
Shi ma Cabrera ya bayyana rasuwar faston a matsayin babban rashi ga cocin, yana mai kira ga mabiya da su ci gaba da yi masa addu'a.
Har yanzu hukumomi ba su bayyana abin da ya sa kuros ɗin ya kuɓuce daga inda aka kafa shi ya faɗo ba.
"Wata rana dukkanmu da muke a nan za mu mutu"
Kafin aukuwar lamarin, faston ya gabatar da wa'azi inda ya buƙaci mabiya cocinsa su yi tunani kan irin lokacin da suke ware wa ga Allah a rayuwarsu ta yau da kullum, tare da tambayar kansu ko suna ba Shi lokaci kamar yadda suke yi wa wasu abubuwa na ɗan lokaci kaɗan, kamar wayoyin hannu ko shirye-shiryen talabijin.
A wani ɓangare na wa'azin nasa, ya ce: "Ƴan'uwa, wata rana dukkanmu da muke a nan za mu mutu."
Ya kuma ƙara da cewa:
"Wani lokaci, lokacin da muke ɓatawa kan abubuwan da ba su da wata muhimmiyar ma'ana ba, ba ya kai lokacin da muke ware wa ga Allah. Lokaci mai amfani da muke ba Allah, da 'yan'uwanmu, da mazajenmu ko matanmu, da 'ya'yanmu da iyalanmu, shi ne mafi kyawun lokacin da aka yi amfani da shi."
Bayan kammala wa'azin, faston ya koma kan dandamali domin ci gaba da addu'o'in ibadar, amma a daidai wannan lokaci ne hatsarin ya faru, minti biyu bayan ya sauka daga mumbari.
"Fasto! Fasto!" Ihun da wata mata da ke wurin ta yi kenan. "A kira motar asibiti! Fasto! Fasto!"
Har zuwa lokacin da lamarin ya faru, hukumomi ko kuma babban cocin Katolika na Guayaquil ba su bayyana abin da ya sa babban kuros ɗin ya kuɓuce daga inda aka kafa shi ba.
A ranar Litinin kuma, kafafen yaɗa labarai na yankin sun nuna hotunan yadda ake aikin mayar da siffar Yesu Almasihu da ke kan kuros ɗin zuwa wurinta a cocin.