Wasan zamiya da bikin baje koli cikin hotunan Afirka

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Wasu daga cikin zaɓaɓɓun hotunan Afirka da na ƴan nahiyar a wasu sassan duniya cikin makon da ya gabata.

 bikin Halloween a birnin Johannesburg
Bayanan hoto, A ranar Asabar ne aka gunadar da gasar masu ado ta musamman a wani taron tallafa wa al'umma lokacin bikin Halloween a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu.
Ɗan tserenƘasar Habasha Yomif Kejelcha
Bayanan hoto, Ɗan tseren ƙasar Habasha, Yomif Kejelcha ya baje a ƙasa bayan da ya karya tarihin da ya kafa a gasar Valencia ta Sifaniya.
Lagos fashion Week
Bayanan hoto, An ƙaddamar da bikin baje kolin tufafin ƙawa na mako guda a Legas ranar Alhamis
...
Bayanan hoto, Wata tana shan kwalliya kafin a gabatar da ita a bikin ranar Juma'a
Lagos Fashion Week
Bayanan hoto, Mahalarta bikin sun yi ado irin tasu ta musamman
Bikin cika shekaru 70 da samun ƴancin kai a Algeriya
Bayanan hoto, A ranar Laraba a birnin Algiers, masu rawa sun gudanar da wani wasan kwaikwayo don bikin cika shekara 70 da samun ƴancin kai daga Faransa.
Masu zanga-zanga a Afirka ta Kudu
Bayanan hoto, Masu zanga-zanga a Afirka ta Kudu a ranar Talata sun yi kira ga hukumomi su gurfanar da wasu manyan jami’an kiwon lafiya biyu kan mutuwar majinyata 144 da suka mutu a cikin mawuyacin hali, a wani lamari da aka fi sani da bala’in Life Esidimeni.
.
Bayanan hoto, Masu zanga-zanga a Birtaniya sun buƙaci kawo ƙarshen yaƙin basasa a Sudan tare da yin allawadai da goyon bayan da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ke ba ƙungiyar RSF. Haɗaɗɗiyar Daular Larabawar ta musanta hannu amma hukumomi daban-daban ciki har da Majalisar Dinkin Duniya sun bankaɗo hujjoji da ke nuni da akasin hakan.
Masu Zanga Zanga a Lisbon
Bayanan hoto, Wani ɗan sanda ya harbe wani dan cirani ɗan ƙasar Cape Verde a kan titin Lisbon na ƙasar Portugal, lamarin da ya fusata mazauna yankin suna kira da a yi adalci.
..
Bayanan hoto, Ɗan Ivory Coast Roger Bango, (dama) ya gabatar da wannan rigar da aka yi da cakula a bikin baje kolin cakula na Paris na shekarar 2024 a Faransa ranar Talata.
filin wasan zamiya a babban birnin Senegal
Bayanan hoto, Wannan filin wasan zamiyan a babban birnin Senegal, Dakar, ya kasance kasaitacce wurin shaƙatawa tun lokacin da aka buɗe shi shekara biyu da suka gabata.
Wasan zamiya
Bayanan hoto, Yara masu wasan zamiya na shirya nuna bajintarsu
Masu yawon buɗe ido a ƙasar Masar
Bayanan hoto, Masu yawon buɗe ido da ke ninƙaya a gaɓar tekun ƙasar Masar ranar Talata