Chelsea na zawarcin Ayari, Barcelona da Madrid na neman Manzambi

Asalin hoton, Getty Images
Chelsea ta bi sahun Galatasaray wajen zawarcin ɗan wasan tsakiya na Brighton, Yasin Ayari, ɗan ƙasar Sweden mai shekara 23. (Teamtalk)
Liverpool ba ta cikin gaggawar fara tattaunawar sabunta kwantiragin ɗan wasan tsakiya na Argentina, Alexis Mac Allister, duk da cewa ɗan wasan mai shekara 27 yana taka leda yadda ya kamata a kakar wasa ta bana.(Telegraph)
Barcelona da Real Madrid na daga cikin ƙungiyoyin da ke sanya ido kan ɗan wasan tsakiya na Switzerland, Johan Manzambi, bayan ɗan wasan mai shekara 21 ya fara kakar wasan bana da kyau a Aston Villa. (Football Insider)
Sunderland na shirin gabatar da sabon tayin ɗaukar ɗan wasan gefe na Sporting da Mozambique, Geny Catamo, mai shekara 25, a lokacin kasuwar musayar ƴan wasa ta watan Janairu. (Teamtalk)
Everton na sa ido kan ɗan wasan gaba na Dinamo Zagreb, Dion Beljo, ɗan ƙasar Croatia mai shekara 24, a matsayin ɗaya daga cikin zaɓin da suke da shi a kasuwar watan Janairu. (Football Insider)
Liverpool da wasu manyan ƙungiyoyin Turai, na sha'awar ɗaukar ɗan wasan tsakiya na Mexico, Gilberto Mora, mai shekara 18, daga ƙungiyar Tijuana. (Marca)
Arsenal na son dawo da kuɗin da ta kashe wajen ɗaukar ɗan wasan gaba na Sweden, Viktor Gyokeres, mai shekara 28—kuɗi da ya kai fam miliyan 55—inda ake ganin yarjejeniyar za ta fi yiwuwa a ƙarshen kakar wasa maimakon a watan Janairu.(Football Insider)
Ɗan wasan gaba na Brazil, Vinicius Jr, ya kusa komawa Arsenal a lokacin bazara, amma yanzu ɗan wasan mai shekara 26 yana fatan ci gaba da zama a Real Madrid har zuwa lokacin da zai yi ritaya daga ƙwallon ƙafa. (Mail)
Arsenal ce ke kan gaba wajen zawarcin ɗan wasan tsakiya na Turkiyya, Can Uzun, mai shekara 20, wanda ke buga wa Eintracht Frankfurt wasa. (The Daily Briefing)





























