Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ronaldo ya ci amanar Manchester United - Ten Hag
Tsohon kocin Manchester United, Erik ten Hag ya ce Cristiano Ronaldo "ya ci amanar ƙungiyar kuma ya ci amanata" a lokacin da ɗan ƙasar Holland ɗin ke jagorantar ƙungiyar a Old Trafford.
Ronaldo dan wasan Portugal ya yi zaman wa'adi na biyu a United lokacin da Ten Hag ya karɓi ragamar horar da ƙungiyar a bazarar shekarar 2022, amma ya bar ƙungiyar daga baya cikin yanayi mai cike da ce-ce-ku-ce.
"Ya ci amanar ƙungiyar, kuma ya ci amanata, domin mun tsara abubuwa tare da shi," in ji Ten Hag a wata hira da The Athletic.
"Na je Portugal domin in yi magana da shi game da abin da nake son cimmawa kafin in je United.
"Babu shakka yana ɗaya daga cikin fitattun 'yan wasan ƙwallo kafa a tarihin. Na girmama shi matuƙa. Sai dai a matsayina na koci dole ne in yanke hukuncin da nake ganin ya dace, kuma in ci gaba da riƙe 'yan wasan da nake yabawa."
Ten Hag ya cire Ronaldo daga cikin yan wasan da za su fuskanci a Chelsea a Premier League a watan Oktoban 2022, sakamakon ya ƙi shiga wasa a matsayin canji a karawar da suka yi da Tottenham kwanaki uku kafin hakan.
Ronaldo ya yi wata hira a watan Nuwamba inda ya ce yana jin United ta "ci amanarsa", ba ya girmama Ten Hag, kuma ana tursasa masa ya fice daga ƙungiyar kafin daga bisani bangarorin biyu suka yanke shawara a yanke alaka tsakanin United da tsohon dan wasan Real Madrid da Juventus.
Ronaldo yana da shekara 36 lokacin da ya koma Manchester United daga Juventus a shekarar 2021, lokacin Ole Gunnar Solskjaer ne yake kocin ƙungiyar.
A ƙarƙashin Ten Hag, Ronaldo ya zura ƙwallaye uku kacal a wasa 16 kafin ya bar kungiyar Old Trafford a kakar 2022-23.
Ten Hag ya yi wannan hirar a lokacin da aka dakatar da Ronaldo kwanaki 30 tare da cin tararsa euro 255 (£215) daga Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Portugal saboda ya bar sansanin tawagar a watan da ya gabata ba tare da izini ba.
Manchester United ta sallami Ten Hag a watan Oktoban 2024 bayan ya lashe Kofin Carabao a 2023 da kuma Kofin FA a 2024.
Da yake magana kan zamansa a Old Trafford, Ten Hag ya ƙara da cewa so ɗaukar Frenkie de Jong da Harry Kane da Declan Rice, sannan kuma bai amince da sayar da Scott McTominay zuwa Napoli a watan Agustan 2024 ba.
Yadda Manchester United ta ɗauki Ten Hag
Manchester United ta sanar da ɗaukar Erik ten Hag a watan Afrilun 2022, domin maye gurbin Ralf Rangnick, bayan ƙarshen kakar 2021-22. A lokacin, Ten Hag ya zo ne daga Ajax bayan ya yi suna sosai a Netherlands tare da lashe kofunan gida da kuma kai Ajax wasan kusa da na ƙarshe a Gasar Zakarun Turai ta UEFA a kakar 2018-19.
An ɗora masa nauyin dawo da Manchester United kan turbar nasara, bayan shekaru da dama na rashin tabbas tun bayan ritayar Sir Alex Ferguson. Magoya baya da mahukuntan ƙungiyar sun yi imanin cewa salon wasansa na mallakar ƙwallo da tsarin kai hare-hare da kuma haɓaka matasa zai taimaka wajen dawo da martabar kungiyar ɗin.
Ya fara jan ragamar Old Trafford da tagomashi duk da fuskantar kalubale
Duk da rashin nasara a wasanninsa biyu na farko a gasar Premier League, Ten Hag ya samu nasarar sauya yanayin ƙungiyar cikin kankanin lokaci. A kakar wasa ta farko, Manchester United ta kammala gasar Premier League a matsayi na uku tare da samun gurbin buga Gasar Zakarun Turai ta Champonpions League. Haka kuma ta lashe Kofin Carabao, wanda ya kawo ƙarshen shekara shida da ƙungiyar ta kwashe ba tare da lashe babban kofi ba.
Haka kuma United ta samu nasarori masu armashi a kan manyan ƙungiyoyi kamar Manchester City da Liverpool da Arsenal. Wannan ya sa mutane da dama suka yi imanin cewa ƙungiyar na fara komawa kan turbar da ta dace.
Rikicin Ronaldo da Ten Hag
Babban ƙalubalen farko da Ten Hag ya fuskanta shi ne batun Cristiano Ronaldo. A watan Oktoban 2022, Ronaldo ya ƙi shiga wasa a matsayin canji a karawar da United ta yi da Tottenham Hotspur. Bayan haka, Ten Hag ya cire shi daga yan wasan da za su buga da Chelsea a babbar gasar tamaula ta Ingila.
Daga bisani Ronaldo ya yi wata hira mai cike da ce-ce-ku-ce inda ya ce yana jin kamar an ci amanarsa a Manchester United, kuma ba ya girmama Ten Hag. Wannan kalaman ya haifar da barinsa United, bayan da suka cimma yarjejeniyar soke kwantiraginsa da ya rage a kungiyar Old Trafford.
Ten Hag ya ce Ronaldo bai shirya kansa yadda ya kamata don yin atisaye ba, kuma ba a samun abinda ake bukata daga gare shi. Ya kuma yi zargin cewa Ronaldo yana zuga wasu 'yan wasan su rage sa ƙwazo a lokacin atisayen.
Kalubalen da Ten Hag ya fuskanta a Manchester United
Bayan kakarsa ta farko mai kyau, Ten Hag ya shiga mawuyacin hali. Matsalolin raunin 'yan wasa da ya addabi ƙungiyar, musamman a bangaren tsaron baya. Hakan ya jawo United ta yi ta fama da fuskanatar koma baya a sakamakon wasannin da take bugawa a gasar Premier League da kuma Turai.
A kakar 2023-24 aka fitar da Manchester United daga Gasar Zakarun Turai tun a matakin rukuni, sannan ta kammala Premier League a matsayi na takwas, mafi muni a tarihinta tun bayan sauya fasalin gasar Premier League. Duk da haka, Ten Hag ya ceci kakar ne ta hanyar lashe Kofin FA bayan doke Manchester City a wasan ƙarshe.
Haka kuma, ya sha suka kan wasu saye-sayen 'yan wasa da yake yi, matsalar rashin zura ƙwallaye a raga da kuma rashin samun a sakamako akai-akai. A hirarsa ta baya-bayan nan, ya ce tun daga farkon aikinsa ya jaddada cewa ƙungiyar tana buƙatar sabon mai tsara wasa, ƙarfafa tsakiya da kuma ƙwararren mai cin ƙwallaye.
Wasanni da nasarorin da ya jagoranta
A lokacin da ya shafe kusan shekaru biyu da rabi yana jan ragamar Manchester United, Ten Hag ya jagoranci wasa 85 a Premier League. Daga ciki ya yi nasara a karawa 44, ya yi canjaras 14 sannan ya sha kashi 27. Kenan yana da kashi 52 cikin 100 a jerin nasarorin da ya yi.
Ya lashe Kofin Carabao a shekarar 2023 da kuma Kofin FA a shekarar 2024, nasarori biyu da suka sa ya zama ɗaya daga cikin kocin United bayan Ferguson da suka samu manyan kofuna.
Dalilan da Manchester United ta kori Ten Hag
Duk da lashe Kofin FA a ƙarshen kakar 2023-24, sakamakon da ƙungiyar ta riƙa samu a farkon kakar 2024-25 ya jefa Ten Hag cikin matsin lamba. Ƙungiyar ta kasa cin wasannin farko a kakar, kuma ta tsinci kanta a mataki na 14 a teburin Premier League lokacin da aka yanke shawarar sallamarsa.
A ranar 28 ga Oktoban 2024, Manchester United ta sanar da raba gari da Ten Hag. Kungiyar ta bayyana cewa ya bar ƙungiyar bayan shekaru biyu da rabi a kan aiki, duk da cewa ya taimaka wajen lashe kofuna biyu na cikin gida.
Kungiyar da ya horar bayan barin Manchester United
Bayan sallamarsa daga Manchester United a watan Oktoban 2024, Ten Hag ya koma Jamus inda aka naɗa shi a matsayin kocin Bayer Leverkusen kafin kakar wasa ta 2025-26. Sai dai zamansa a can bai daɗe ba, domin ya bar aikin bayan ɗan gajeren lokaci.
Ko da yake zaman Erik ten Hag a Manchester United ya haɗu da nasarori da ƙalubale, ba za a manta da cewa ya kawo ƙarshen jiran shekaru shida ba tare da daukar babban kofi ba.
Sai dai rikicin da ya yi da Cristiano Ronaldo da matsalolin raunin yan wasa da yawa da rashin samun sakamako akai-akai da matsin lamba a gasar Premier League sun taka rawa wajen kawo ƙarshen aikinsa a Old Trafford.