Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mutanen da suka samu kyautuka a bikin Ballan d'Or na 2026
Masoya ƙwallon ƙafa a faɗin duniya na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu kan kyaututtukan ballan d'or da aka bayar jiya a birnin Landan.
An gudanar da bikin ne karon farko a wajen Faransa, domin karrama Stanley Matthews, mutumin da ya fara lashe kyauta, wanda ɗan asalin Ingila ne.
Kyaftin ɗin tawagar Ingila Harry Kane ne ya lashe kyautar gwarzon ɗan kwallon na wannan shekara, yayin da abokan takararsa, Kylian Mbappe da Lamine Yamal suka zo na biyu da na uku.
Sai dai akwai kyautuka daban-daban da kaa bai wa waɗanda suka yi fice a harkar kwallon kafa a wannan shekara.
A wannan mukala za mu duba jerin mutanne da suka samu kyautuka a bikin da aka gudanar ranar Litinin.
Harry Kane
Kyaftin ɗin tawagar Ingila kuma fitaccen ɗan wasan gaba na ƙungiyar Bayern Munich, Harry Kane, ne ya lashe kyautar Ballon d'Or.
Ɗan wasan mai shekara 33 ya zama dan Ingila na farko da ya samu nasarar lashe kyautar cikin shekara 25.
Kane ya lashe kofuna uku a kakar da ta gabata da Bayern Munich, tare da zura ƙwallaye fiye da 70 a kakar wasan da ta gabata.
Ya jagoranci Ingila zuwa matakin wasan kusa da ƙarshe a gasar Kofin Duniya tare da zura ƙwallaye shida a gasar.
Alexia Putellas
Ita ce ta lashe kyautar ballan d'Or ɓangaren mata.
Idan aka yi la'akari da nasarorin kulob da kuma bajintar da Alexia Putellas ta nuna, da wuya a nemi abin da ya fi nasarorin da ta samu, bayan ta jagoranci Barcelona a matsayin kyaftin zuwa lashe manyan kofuna huɗu na nahiyar Turai a kakar wasa ta 2025-26.
A kakar, Barcelona ta lashe Liga F da Copa de la Reina da Spanish Super Cup, da kuma Champions League.
Putellas ta kuma zama ta biyu cikin fitattun ƴan wasan Barcelona da suka fi zura ƙwallaye a tarihin kulob ɗin, bayan da ta ci kwallaye biyu a wasan daf da na kusa da na ƙarshe na gasar Champions League a watan Mayu.
Hakan ya taimaka mata wajen samun kyautar gwarzuwar gasar.
Lamine Yamal - Gwarzon matshin ɗan wasa
Matshin ɗan wasan Sifaniya da Barcelona, Lamine Yamal ne ya samu kyautar matashin da ya fi kowa bajinta na ballan d'Or.
Yamal ya taimaka wa Sifaniya lashe Kofin Duniya, sannan ya taimaka wa Barcelona lashe manyan kofuna biyu a kasar wasan da ya gabata.
Wannan shi ne karo na uku a jare ɗan wasan na lashe wannan kyauta.
A jawabin da ya gabatar bayan lashe kyautar ya ce ya yi wa abokin wasansa Cubarsi fatan lashe kyautar, amma kuma hi ne ya rabauta da ita.
Vicky López - Gwarzuwar matashiyar ƴarwasa
Matshiyar yar wasan Barcelona, Vicky López ce ta samu nasarar lashe kyautar gwarzuwar matashiyar ƴar wasa.
López ta taka rawar gani a kakar wasan da ta gbata, bayan ta taimaka wa Barcelona lashe manyan kofuna hudu.
Bukayo Saka - mafi ayyukan taimako
Ɗan wasan Ingila, Bukayo Saka ne ya samu kyautar ɗan wasa mafi ayyukan taimakon marasa karfi na ballon d'Or.
Yayin da yake jawabi bayan karɓar kyautar, ɗan wasan na Arsenal ya ce "Ina aiki sosai tare da iyalina da kuma wata ƙungiyar agaji mai suna BigShoe''.
''Muna ƙoƙarin yin duk mai yiwuwa domin taimaka wa yara da ba su samu damar da mu muka samu ba," in ji shi.
Unai Simon - Mai tsaron raga mafi ƙwazo (maza)
Mai tsaron ragar Sifaniya da Athletic Bilbao, Unai Simón ne ya samu nasarar lashe wannan kyauta.
Simon ya taimaka wa Sifaniya lashe Kofin Duniya, inda ya kasance golan da aka zura wa ƙwallo kaɗan.
Yayin karbar kyautar Simon ya gode wa tawgaar Sifaniya, wadda ya ce ta taimaka masa wajen samun nasarar.
Cata Coll - Mai tsaron raga mafi kwazo (mata)
A ɓangaren mata kuwa, mai tsaron ragar ƙungiyar mata ta Barcelona, Cata Coll ce ta samu wannan kyauta.
Cata Coll ta kafa tarihi bayan bajintar taimaka wa ƙungiyar mata ta FC Barcelona lashe manyan kofuna huɗu a kakar wasa guda.
Nasarar ta zo ne bayan rawar gani da ta taka wajen taimaka wa Barcelona ta mamaye manyan gasa a kakar wasan.
Luis de la Fuente - Kocin maza mafi bajinta
Kocin Sifaniya, Luis de la Fuente ne ya samu kyautar gwarzon koci na ballon d'Or.
Ya samu wannan kyauta ne bayan jagorantar tawagar Sifaniya wajen lashe Gasar Kofin duniya na 2026 da aka yi a ƙasashen Amurka, Mexico da Canada.
Pere Romeu - Kocin mata mafi ƙwazo
Kocin tawagar mata da Barcelona, Pere Romeu ne ya samu kyautar kocin mata mafi bajinta na ballon d'Or.
Romeu ya taimaka wa tawagar matan Barcelona lashe manyan kofuna huɗu a kakar wasan da ta gabata.
Sauran kyautuka
Ɗan wasan gaba mafi hazaƙa - Kane
Yar wasan gaba mafi haaƙa - Charlyn Corral
Ƙungiyar mafi ƙwazo - PSG
Ƙungiyar mata mafi kwazo - Barcelona.