Kwamandojin ISWAP biyu da sojojin Najeriya suka ce sun kashe

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe ɗaya daga cikin manyan kwamandojin ƙungiyar Iswap a wata fafatawa da aka yi da dakarunta a jihar Borno.
Dakarun da ke aiki ƙarƙashin Shirin Operation Hadin Kai sun ce sun samu nasarar daƙile wani abu da suka bayyana a matsayin gagarumin samame daga ƴan ƙungiyar a cibiyoyinsu da ke Kukawa, kusa da Tafkin Chadi, a ƙarshen mako.
Sai dai babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da sahihancin batun.
Wannan ba shi ne karon farko da sojojin Najeriya ke sanar da kashe manyan jagororin ƙungiyar Iswap ba.
A watan Yulin 2026, rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe Abu Salim al-Barnawi, ɗaya daga cikin manyan shugabannin ƙungiyar ISWAP.
Rundunar sojin Najeriya ta ce lamarin ya faru ne a lokacin da aka daƙile hari kan wani sansanin soji, inda suka tabbatar da mutuwar Abu Salim tare da masu aikin ɗauka da yada bayanan ƙungiyar ta Iswap.
"Bayan arangamar, dakaru sun samu nasarar ƙwato makamai da alburusai da kuma kayan sadarwa," in ji wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar.
Sanarwar wannan kisa na kwamandan za ta iya zama wata babbar koma-baya ga ISWAP, wadda take cikin ƙungiyoyin masu ɗauke da bindiga waɗanda suka fi kai hare-hare a yankin Tafkin Chadi.
Sai dai a baya ƙungiyar ba ta nuna gajiyawa ba wajen maye gurbin jagororinta da da aka hallaka a fagen daga.
Wannan sanarwa da rundunar sojin Najeriya ta fitar na zuwa ne yayin da mayaƙa ke ci gaba da kai hare-hare lokaci zuwa lokaci a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
A watannin baya-bayan nan ƙungiyar ISWAP ta ƙara ƙaimi wajen kai hare-hare a sansanonin sojin Najeriya da kuma kan fararen hula a yankunan karkara a jihohin Borno da Yobe, inda suke kashe mutane da garkuwa da su da kuma yi wa jami'an tsaro ɓarna.
Duk da cewa rundunar sojin Najeriya na iƙirarin matsa wa ƙungiyoyi masu alaƙa da Boko Haram ƙaimi, har yanzu yankin Tafkin Chadi na fama da matsalar rashin tsaro, shekaru sama da 15 tun bayan ɓarkewar rikicin Boko Haram.
Mayaƙa na ci gaba da kai hari kan dakaru da fararen hula, musamman a yankunan da ke cikin daji a yankin na Tafkin Chadi mai iyaka da ƙasashen Nijar da Chadi da kuma Kamaru.
Wane jagoran ISWAP ne aka kashe?
Sanarwar da rundunar sojin Najeriya ta fitar ta hannun mai magana da yawunta Kyaftin Mohammed Goni ta ce cikin kwamandojin Iswap da aka kashe akwai Abu Hajara, wanda rundunar sojin ta bayyana a matsayin wakili a kwamitin shura na ƙungiyar ta ISWAP, wadda ita ce majalisar ƙoli ta tafiyar da al'aumran ƙungiyar.
Sai kuma kwamanda Abu Walid, wanda na kusa ne da jagoran ƙungiyar Ba Shuwa.
Rundunar sojin ta ce akwai kuwam wasu manyan mayaƙan ƙungiyar waɗanda aka kashe a lokacin artabun, inda rundunar sojin ta samu nasarar ƙwato makamai da alburusai da kuma na'urorin sadarwa.
BBC ba ta riga ta tantance sahihanci da kuma bayanan manyan mayaƙan Iswap ɗin da sanarwar ta ambata ba.
Sanarwar ta kuma tabbatar da wani samame da dakarun Najeriya suka kai a Buni Yadi da ke jihar Yobe mai maƙwaftaka da jihar Yobe, inda sojojin suka ce sun kashe mayaƙa 55, ciki har da wasu manyan kwamandoji.





















