Man United na zawarcin Ait Nouri, Barcelona na harin Hincapie

Rayan Ait-Nouri
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester United na duba yiwuwar ɗaukar matakin da zai ba kowa mamaki na sayen ɗan wasan baya na Manchester City, Rayan Ait-Nouri mai shekara 25; kuma batun sharuɗɗan kwangilar ɗan wasan na Algeria ba za su kawo cikas ga yiwuwar cimma yarjejeniya ba. (Florian Plettenberg)

Ɗan wasan baya na Arsenal ɗan ƙasar Ecuador, Piero Hincapie, mai shekara 24, yana cikin jerin ƴan wasan baya da daraktan wasanni na Barcelona, ​​Deco, ke son ɗauka. (Sport)

Mataimakin kocin tawagar Ingila, Anthony Barry, ya bayyana a matsayin wanda zai iya maye gurbin Pierre Sage, idan har ƙungiyar Crystal Palace ta kori kocin ɗan ƙasar Faransa. (Mirror)

Bayern Munich na ci gaba da sa ido kan kyaftin ɗin Arsenal, Martin Odegaard, yayin da ake fuskantar rashin tabbas game da sabon kwantiragin ɗan wasan tsakiyar na Norway mai shekara 27 a ƙungiyar ta Gunners. (Caughtoffside)

Ɗan wasan tsakiyar ƙasar Spain, Martin Zubimendi, mai shekara 27, a shirye yake ya nazarin barin Arsenal a lokacin kasuwar musayar ƴan wasa ta hunturu. (Team Talk)

Kungiyar Al-Hilal ta gasar Saudi Pro-League ba za ta bai wa ɗan wasan tsakiyar Manchester United da Portugal, Bruno Fernandes, mai shekara 32, damar barin Old Trafford ba, duk da cewa sun kusan ɗaukar sa a farkon kakar wasa ta bana. (Talksport)

Tottenham ba za ta amince da sayar da ɗan wasan tsakiya na ƙasar Sweden, Lucas Bergvall ba, duk da cewa Barcelona da Napoli na nuna sha'awar ɗaukar ɗan wasan mai shekara 20. (Football Insider)

Kocin Aston Villa, Unai Emery, yana cikin jerin mutane biyar da Manchester United ke duba yiwuwar ɗauka a matsayin wanda zai maye gurbin Michael Carrick; sai dai ana cewa tsarin gudanar da harkokin wasanni na yanzu a ƙungiyar bai dace da ɗan ƙasar Spain ɗin ba. (Daily Mail)

Ɗan wasan gaba na Minnesota United mai shekara 26, Kelvin Yeboah — wanda ɗan dan'uwan fitaccen ɗan wasan Leeds da Ghana, Tony Yeboah ne — ya na ɗaukar hankalin wasu ƙungiyoyin gasar Premier League. Everton da Crystal Palace da Sunderland duk suna neman ɗan wasan gaba a kasuwar saye da sayar da ƴan wasa. (Talksport)

Ƴan wasan Newcastle sun yi imanin cewa kasadar da ƙungiyar ta ɗauka wajen sayen ƴan wasa a lokacin bazara, shi ne babban dalilin matsalolin da suke fuskanta a kakar wasa ta bana. (Telegraph)