Hotunan Afrika na mako: Daga ranar 5 zuwa ranar 11 ga watan Nuwambar 2021

An wallafa

Zababbun hotunan Afrika da ma 'yan Afrika a wasu nahihoyin na wannan mako.

Short presentational grey line
Wani masunci mai suna Osman Abdulahi dauke da babban kifi da ya kamo a wani kogin da ke Mogadishu, babban birnin Somalia ranar Juma'a.
Bayanan hoto, Wani masunci mai suna Osman Abdulahi dauke da babban kifi da ya kamo a wani kogin da ke Mogadishu, babban birnin Somalia ranar Juma'a.
Ranar Laraba mutane sun yi layi a kan titunan Cotonou, babban birnin Benin, a yayin da aka komawa da kasar wasu kayayykin tarihi da aka sace shekaru 130 da suka wuce lokacin mulkin mallakar Faransa.
Bayanan hoto, Ranar Laraba mutane sun yi layi a kan titunan Cotonou, babban birnin Benin, a yayin da aka komawa da kasar wasu kayayykin tarihi da aka sace shekaru 130 da suka wuce lokacin mulkin mallakar Faransa.
Washegari a Senegal, mambobin kungiyar Morudai ta mabiya addinin Musulunci, sun yi bikin tunawa da mutuwar mutumin da ya kafa kungiyar Amadou Bamba.
Bayanan hoto, Washegari a Senegal, mambobin kungiyar Morudai ta mabiya addinin Musulunci, sun yi bikin tunawa da mutuwar mutumin da ya kafa kungiyar Amadou Bamba.
'Yar Najeriya mai zane-zane Alduphina Imuede a tsaye a kusa da wadansu zane-zane da ta yi a wajen bikin nunin zane-zane na shekara mai taken Art X da aka yi a birnin Lagos ranar Juma'a...
Bayanan hoto, 'Yar Najeriya mai zane-zane Alduphina Imuede a tsaye a kusa da wadansu zane-zane da ta yi a wajen bikin nunin zane-zane na shekara mai taken Art X da aka yi a birnin Lagos ranar Juma'a...
An art enthusiast speaks to Delphine Lopes of Galerie Cecile Fakhoury.
Bayanan hoto, An sake bude babban taro kan zane-zane na Afirka ta Yamma, bayan da aka gudanar da shi ta intanet a shekarar da ta wuce saboda annobar korona...
Ayoola Gbolahan, an artist represented by Kanbi projects, poses for a picture in front of his artwork.
Bayanan hoto, Mai zayyana Ayoola Gbolahan shi ma ya nuna kayan da ya zana a wurin taron nan Najeriya.
Dan damben nan Kamaru Usman, wanda ake wa lakabi da "the Nigerian Nightmare", yana shiri inda daga bisani ya kare kambunsa a fafatawar da suka yi da Colby Covington a birnin New York City ranar Asabar.
Bayanan hoto, Dan damben nan Kamaru Usman, wanda ake wa lakabi da "the Nigerian Nightmare", yana shiri inda daga bisani ya kare kambunsa a fafatawar da suka yi da Colby Covington a birnin New York City ranar Asabar.
Bayan mutuwar Abdul Razzaq Lachhab sakamakon shakar barkonon-tsohuwar da 'yan sanda suka watsa masa lokacin zanga-zanga kan kwashe shara a Tunisia, masu zanga-zangar kyamar rikici sun rika kwalaye masu dauke da sunansa ranar Asabar.
Bayanan hoto, Bayan mutuwar Abdul Razzaq Lachhab sakamakon shakar barkonon-tsohuwar da 'yan sanda suka watsa masa lokacin zanga-zanga kan kwashe shara a Tunisia, masu zanga-zangar kyamar rikici sun rika kwalaye masu dauke da sunansa ranar Asabar.
A kwanakin baya-bayan nan kusan mutum 5,000 suka tsere suka tsallaka iyaka zuwa Uganda bayan hare-haren da 'yan tawayen da ke Chanzu da Runyonyi, suke kai musu a gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo.
Bayanan hoto, A kwanakin baya-bayan nan kusan mutum 5,000 suka tsere suka tsallaka iyaka zuwa Uganda bayan hare-haren da 'yan tawayen da ke Chanzu da Runyonyi, suke kai musu a gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo.
Dan tseren Kenya Albert Korir ya yi nasara a gasar tsere da aka gudanar a birnin New York City ranar Lahadi, bayan da ya zo matsayi na biyu a shekarar 2019.
Bayanan hoto, Dan tseren Kenya Albert Korir ya yi nasara a gasar tsere da aka gudanar a birnin New York City ranar Lahadi, bayan da ya zo matsayi na biyu a shekarar 2019.
Masu tallan kabeji suna yin bacci a yayin da suke jiran kwastomomi a kasuwar kayan marmari da ke Addis Ababa, babban birnin Ethiopia, ranar Juma'a.
Bayanan hoto, Masu tallan kabeji suna yin bacci a yayin da suke jiran kwastomomi a kasuwar kayan marmari da ke Addis Ababa, babban birnin Ethiopia, ranar Juma'a.
A green monkey reaches for a banana.
Bayanan hoto, Lokacin cin abincin wannan birin da ke Tsibirin Santiago da ke Cape Verde, ya yi a ranar Asabar.
Ranar Talata, Kevin Ochieng Onyango ya lashe gasar Hotuna kan Muhalli ta 2021 a bangaren Sauyin Yanayi saboda hoton da ya dauka mai take The Last Breath. "Wani yaro ya shaki iska daga tsirrai a yayin da gugwa take hadawa a bayansa, a wata alama ta sauyin da ke tafe," a cewar mai daukar hoton.
Bayanan hoto, Ranar Talata, Kevin Ochieng Onyango ya lashe gasar Hotuna kan Muhalli ta 2021 a bangaren Sauyin Yanayi saboda hoton da ya dauka mai take The Last Breath. "Wani yaro ya shaki iska daga tsirrai a yayin da gugwa take hadawa a bayansa, a wata alama ta sauyin da ke tafe," a cewar mai daukar hoton.
1px transparent line
A woman selling children gift toys waits for buyers.
Bayanan hoto, Ana sayar da katunan da ake bai wa yara kyautarsu a wurin bajekoli da aka gudanar a Lagos ranar Juma'a.
Jacques Blaauw of South Africa plays his tee shot on the 8th hole.
Bayanan hoto, 'Yar kwallon golf ta Afrika Ta Kudu Jacques Blaauw ta kammala zagayenta a gasar Rolex Challenge Tour Grand Final da aka yi a Sifaniya ranar Lahadi.

Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka.