Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya taya tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, murnar cika shekara 70 da haihuwa.
A wata sanarwa, Gwamna Yusuf ya bayyana wannan rana a matsayin wata muhimmiyar dama ta tunawa da rayuwar Kwankwaso, da jagorancinsa, da kuma gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa jihar Kano da Najeriya baki ɗaya.
Gwamnan ya yaba da rawar da Kwankwaso ya taka a ci gaban siyasar jihar Kano, yana mai cewa bikin cika shekarun na ba da damar waiwayen ayyukan hidimar jama'a da ya yi tsawon shekaru.
Ya ce Kwankwaso ya bayar da gudunmawa a fannoni daban-daban da suka haɗa da mulki, gina ababen more rayuwa da kuma ƙarfafa tsarin dimokuraɗiyya a jihar Kano.
A ranar Litinin 26 ga watan Janairun 2026 gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya koma jam'iyyar APC a hukumance, bayan sanar da ficewarsa daga NNPP a ranar Juma'a 23 ga watan Janairun 2026, ƙasa da shekara uku bayan cin zaɓen gwamnan Kano a cikinta.
Lamarin da ya haifar da tsamin dangantaka tsakanin makusantan biyu.
A wajen bikin komawarsa APC, gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce ya ɗauki matakin sauya sheƙar ne bisa la'akari da inda aka dosa a siyasar Najeriya da kuma buƙatar bin hanyar da za ta kawo ci gaba ga jama'ar Kano baki ɗaya.
Sai dai a wata hira da BBC,Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce yana da yaƙinin cewa sai gwamnan Kano Abba Kabir da muƙarrabansa sun yi da-na-sanin raba gari da tsarinsu.