China ta sanya takunkumai kan ministocin Paraguay da Belize saboda alaƙarsu da Taiwan
China ta sanar da ƙaƙaba takunkumai kan ministocin ƙasashen Paraguay da Belize saboda alaƙar da gwamnatocinsu ke da ita da Taiwan.
Ma'aikatar harkokin wajen ƙasar da ke Beijing ta bayyana cewa an sanya takunkumi kan ministan sadarwa na Paraguay (Gustavo Villate) da ministan harkokin waje na Belize (Francis Fonseca) bisa dalilan kare yancin ƙasa da kuma tsaro.
Matakan sun hada da ƙwace kadarorinsu da ke China, da hana su bizar shiga ƙasar, da kuma hana kamfanoni ƙasar China gudanar da harkokin kasuwanci da su.
Beijing na kallon Taiwan, wadda ke bin tsarin mulkin dimokraɗiyya, a matsayin wani yankin da ke ƙarkashin ikonta.


















