Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE , Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Lahadi 01/11/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Lahadi 1/11/2026

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed

  1. Gwaji ya nuna cewa ba a samu sababbin waɗanda suka kamu da Ebola a Najeriya

    Hukumar kula da cututtuka masu yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta ce gwaje-gwajen ɗakin gwaji da aka gudanar kan samfurorin mutum biyu da ake zargin sun kamu da cutar Ebola a jihar Adamawa sun nuna sakamakon da ke tabbatar da cewa babu wanda ya kamu da cutar a jihar.

    Sanarwar da hukumar ta fitar a daren Asabar ta biyo bayan wani gargaɗi da ta bayar tun farko game da gano wasu mutane biyu da ake zargin suna ɗauke da cutar a Yola, babban birnin jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya.

    Babban daraktan NCDC, Dkta Jide Idris, ya ce hukumomin lafiya na jihar sun samu rahoto a ranar Juma’a bayan gano wasu mutane biyu da ke nuna alamomin da suka yi kama da na Ebola. Wannan ya sa aka killace su tare da fara daukar matakan da suka dace.

    “An tattara samfurori domin gudanar da gwaje-gwajen ɗakin gwaji don gano haƙiƙanin cutar da ke damun su. Abin farin ciki, sakamakon gwaje-gwajen sau biyu da aka yi ya nuna cewa ba su ɗauke da cutar Ebola,” in ji Dokta Jide.

    A halin yanzu, hukumomi na kira ga jama’a da su guji yaɗa jita-jita ko hasashe marasa tushe game da yaɗuwar cutar.

  2. Tattaunawa da Iran na tafiya da kyau, amma ba su da amana - Trump

    Donald Trump ya ce: "Tattaunawar da ake yi da Iran na tafiya da kyau a wannan lokaci, amma babbar matsalar ita ce ba su da cikakkiyar amana. Sukan ƙulla yarjejeniya, sannan daga baya cikin sauƙi su saɓa alƙawuransu ko kuma su janye daga abin da suka amince da shi."

    Kalaman Mista Trump na zuwa ne a daidai lokacin da jami’an Iran suka sha zargin gwamnatinsa da karya alƙawuran da ta ɗauka tare da kai wa Iran hare-hare a yayin da ake ci gaba da tattaunawa.

    Da yake magana da manema labarai a wurin shaƙatawarsa da ke Florida, Trump ya ce: "Mun lalata cibiyoyinsu na makamashin nukiliya. Har yanzu akwai wuri guda ko biyu da ya rage a kula da su, amma za mu iya yin hakan cikin mintuna 10."

    Ya kuma yi magana kan cibiyar Mount Klang, yana cewa: "Wataƙila ya kamata mu dubi wannan wurin ma; za mu iya kammala komai cikin gaggawa."

    Tun da farko, Sakataren Harkokin Wajen Amurka ya ce har yanzu Donald Trump bai yanke hukuncin ko zai kaddamar da harin soja kan Iran ba.

    A gefe guda kuma, jami’an Iran sun yi gargadi a ranar Asabar cewa za su mayar da martani mai tsanani idan Amurka ta kai musu hari.

  3. Farawa

    Masu bibiyar shafin BBC Hausa kai-tsaye, Assalamu alaikum. A yau ma, kamar kullum, za mu kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Kuna kuma iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa kamar a Fesbuk da X da Instagram, sannan ku ziyarci shafinmu na YouTube domin kallon bidiyo.