Hukumomin Premier sun tabbatar da cewa an kama Man City da laifi
Manchester City ta kitsa “kwantaragin bogi” da kamfanonin da suka yi hulɗar kasuwanci da ita a wani yunƙuri na ɓoye hanyoyin samun kuɗaɗen shiga na sirri da suka zarce fam miliyan 830, a cewar hukumomin Gasar Premier ta ƙasar Ingila.
Gasar ta tabbatar cewa an samu Manchester City da laifi a dukkanin zarge-zargen da aka yi mata waɗanda suka shafi karya dokokin kashe kudi na gasar Premier tsakanin kakar wasa ta 2009-10 zuwa 2017-18.
Wani kwamitin bincike mai zaman kansa ya gano cewa a tsakanin lokacin, ƙungiyar ta ƙulla “yarjeniyoyi na bogi” da kuma “dogaro da yarjeniyoyi na bogi wajen kambama yawan kuɗin shiga da ta samu da kuma nuna ƙanƙancin kuɗin da take kashewa”.
Ƙungiyar na ci gaba da musanta aikata laifi, kuma tana da damar ɗaukaka ƙara daga nan zuwa ranar 2 ga watan Oktoba.
A makon da ya gabata ne rahotanni suka fito kan cewa an samu City da laifi dumu-dumu a tuhumar da ake mata ta karya dokokin kuɗi guda 115, sai a ranar Talatar nan ne hukumar da ke kula da gasar Premier ta wallafa wani ɓangare na rahoton.
Rahoton kwamitin ya ce zarge-zargen “sun haura 100 na karya ƙa’idodjin gasar Premier waɗanda aka kasafta su zuwa manyan gidaje huɗu.”
An bayyana cewa jerin kwantaragin bogin da ƙungiyar ta shirya sun kunshi kuɗin da ya kai fam miliyan 830.69.
City ta ce ta samu kuɗin tallace-tallace fam miliyan 360 daga kamfanonin da ta yi hulɗa da su a lokutan da ta lashe kofin Premier a kakar 2011-12 da 2013-14 da kuma 2017-18.
Sai dai fam miliyan 43 ne kacal na halak – sauran kuɗin sun fito ne daga waɗanda suka mallaki ƙungiyar, amma an lulluɓe hanyar da kuɗin suka shigo.