Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Alhamis 29/10/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Alhamis 29/10/2026

Rahoto kai-tsaye

Aisha Aliyu Jaafar da Aminu Kutama

  1. Tinubu zai gabatar da kasafin kuɗin 2027

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, zai gabatar wa majalisar dokokin ƙasar kasafin kuɗin 2027 kafin ƙarshen shekarar da muke ciki.

    Ƙaramar ministar kasafin kudin ƙasar, Dakta Doris Anite-Uzoka ce ta bayyana haka a wani taron manema labarai a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja, babban birnin ƙasar, jim kaɗan bayan kammala taron majalisar zartaswar ƙasar da Shugaba Tinubu ya jagoranta.

    “Mun fara aikin shirya kasafin kuɗin shekarar 2027, kuma manufarmu ita ce a gabatar da shi kafin ƙarshen shekara,” a cewar Mrs Anite-Uzoka.

    Wannan na zuwa ne makonni kaɗan bayan Ofishin Kasafi na Tarayya, a cikin wata takardar kira Kan kasafin kuɗaɗen ma’aikata mai ɗauke da kwanan watan 4 ga Satumbar 2026, wadda Darakta Janar na Ofishin Kasafin Kuɗi, Tanimu Yakubu, ya sanya wa hannu, ya umarci dukkan ma’aikatu, sassa da hukumomin gwamnati su gabatar da shawarwarinsu na kuɗaɗen ma’aikata na shekarar 2027, tare da dokokin da suka kafa su.

    Takardar ta wajabta wa ma’aikatu, sassa da hukumomin gwamnati su haɗa dokokin da suka kafa su da shawarwarin da suke gabatarwa, wani sabon sharaɗi da aka ƙirƙira bayan badaƙalar hukumomin bogi da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka Masu Alaƙa (ICPC) ta gano.

  2. Assalamu Alaikum

    Masu bibiyar shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar yau Alhamis.

    A yau ma za mu kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Kuna kuma iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa kamar a Fesbuk da X da Instagram, sannan ku ziyarci shafinmu na YouTube domin kallon bidiyo.