Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 19/10/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran bubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 19/10/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Rabi'atu Kabir Runka

  1. Akalla mutum 15 sun mutu bayan motar sojoji ta taka nakiya a Borno

    Aƙalla mutane 15 ne suka mutu, ciki har da sojojin Najeriya 10 da mambobi biyar na rundunar sa-kai ta fararen hula (CJTF), bayan da wata motar sojoji ta taka nakiya a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

    Lamarin ya faru ne ranar Asabar yayin da sojojin wata bataliya da ke Gamboru ke sintiri a kan hanyar da ta haɗa Gamboru da Ngala kusa da iyakar Najeriya da Kamaru.

    Rahotanni sun nuna cewa nakiyar da motar ta taka ana zargin mayaƙan Boko Haram ne suka binne ta a kan hanyar. Fashewar ta kashe sojoji takwas nan take.

    Bayan fashewar, wasu mahara sun buɗe wuta kan wata mota ta biyu da ke cikin ayarin, inda suka kashe ƙarin sojoji biyu da kuma mambobi biyar na rundunar CJTF, wadda ke taimakawa sojoji a yaƙi da ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi.

    An kuma kai sojoji shida da suka jikkata zuwa Asibitin Sojoji na Maimalari da ke Maiduguri domin samun kulawar likitoci.

    Har zuwa lokacin da aka haɗa wannan rahoto, rundunar sojin Najeriya ba ta fitar da wata sanarwa mai alaka da bayanan harin ba.

    Babu kuma wata ƙungiya mai zaman kanta da ta tabbatar da adadin mamatan da aka ruwaito.

    Masana tsaro na ganin harin na nuna cewa ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP na ci gaba da kasancewa barazana a yankin duk da hare-haren da sojojin Najeriya ke kai musu.

    Tashin hankalin da ya fara a arewa maso gabashin Najeriya tun shekarar 2009 ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane tare da raba miliyoyin mutane da muhallansu a Najeriya da yankin Tafkin Chadi.

  2. Merz ya bukaci kamfanonin Jamus su rungumi fasahar AI

    Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz, ya yi kira ga kamfanonin ƙasar da su rungumi fasahar AI yayin wani taron masana'antu da aka gudanar a Berlin a ranar Litinin, wanda aka shirya domin jawo hankalin masu zuba jari, ciki har da wata yarjejeniya da ake sa ran za a kulla da kamfanin kera kwamfuta na Amurka, Nvidia.

    Yayin da yake jawabi tare da babban jami'in gudanarwa na Nvidia, Jensen Huang,yayin bude taron kolin, Merz ya jaddada muhimmancin AI wajen farfaɗo da tattalin arzikin Jamus da kuma sabunta harkokin masana'antunta.

    Jamus na fuskantar matsin lamba daga gasa ta duniya da ke kalubalantar manyan kamfanoninta na kera motoci, sinadarai da injiniyanci.

    Saboda haka, Merz na karkashin matsin lamba ya samar da ci gaban tattalin arziki a daidai lokacin da jam'iyyar masu ra'ayin tsattsauran ra'ayi ta dama, Alternative für Deutschland (AfD), ke samun karuwar goyon bayan jama'a.

    Gwamnatin Merz na kallon bunkasa amfani da fasahar AI a matsayin wata muhimmiyar hanya ta kara yawan aiki, habaka kirkire-kirkire da kuma karfafa matsayin Jamus a gasa da sauran manyan tattalin arzikin duniy

  3. Harin jirgin sama mara matuki ya kashe mutum 80 a Sudan

    Rahotanni daga yankin kudancin Sudan sun ce wani hari da jirgin sama mara matuki (drone) ya kai kusa da wata kasuwa ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 80.

    Wani ganau mai suna Ahmed Abakar Wasi ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa ya taimaka wajen binne gawarwaki 50 a garin Al-Dibab da ke jihar West Kordofan, ciki har da gawar ɗan'uwansa.

    A cewar rahoton da wakilin BBC a Nairobi, Richard Kagoe, ya bayar, mutanen da abin ya shafa sun halarci jana'iza ne kuma suna shirin shiga wata mota tsakanin garuruwan Al-Dibab da Al-Mujlad lokacin da harin ya auku.

    An kuma kai mutane da dama da suka jikkata zuwa wani gari da ke kusa domin samun kulawar likitoci, inda ma'aikatan lafiya suka ce wasu mutum 30 sun mutu daga baya sakamakon raunukan da suka samu.

    Rahotanni sun nuna cewa mata da yara na daga cikin mafi yawan waɗanda suka jikkata.

    Har yanzu babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da harin, amma idan aka tabbatar da adadin mamatan, zai kasance ɗaya daga cikin hare-haren da suka fi janyo asarar rayuka tun bayan fara yakin basasar Sudan.

    Yawancin yankunan West Kordofan na karkashin ikon rundunar sa-kai ta Rapid Support Forces (RSF), wadda ta zargi sojojin Sudan da kai harin.

    Lamarin na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan wasu hare-haren sama da aka kai kan wuraren da RSF ke iko da su a birnin Nyala da ke kudu maso yammacin Sudan.

  4. Kotu a Brazil ta bai wa Meta awa 24 ya samar daidaito tsakanin 'yan takarar shugaban ƙasa

    Kotun Koli mai kula da harkokin zaɓe ta Brazil ta bai wa kamfanin Meta awa 24 kacal domin ya tabbatar da cewa ya ɗauki matakan da suka dace wajen tabbatar da adalci da daidaito tsakanin 'yan takarar shugaban ƙasa biyu gabanin zaɓen da za a gudanar ranar Lahadi.

    Duka Shugaban ƙasa Lula da Silva da abokin hamayyarsa, Sanata Flavio Bolsonaro, sun shigar da ƙorafe-ƙorafe a kan Meta, suna zargin kamfanin da yin katsalandan ga kamfen ɗinsu na zaɓe.

    Lula da Silva ya zargi katafaren kamfanin fasahar na Amurka, wanda ya mallaki WhatsApp, Facebook da Instagram, da takaita da kuma hana wasu daga cikin saƙonninsa na kafofin sada zumunta isa ga jama'a.

    A gefe guda kuma, Flavio Bolsonaro ya yi iƙirarin cewa ayyukan yaƙin neman zaɓensa a kafafen sada zumunta sun fuskanci illa sakamakon matakan da aka ɗauka.

    Kamfanin Meta ya musanta aikata wani laifi, sai dai wasu ma'aikatan kamfanin sun ce an samu matsaloli da suka shafi asusun Lula a lokacin kamfen ɗinsa.

    Ministocin Kotun Koli ta Zaɓe sun bayyana cewa tuni sun bai wa Meta wa'adin cika wasu umarni, amma wa'adin ya wuce ba tare da kamfanin ya gabatar da gamsasshiyar hujja ba.

    Kotun ta yi gargadin cewa idan Meta ta kasa tabbatar da cikakken bin umarnin da aka gindaya mata, tarar yau da kullum da ake ci mata za ta ninka zuwa sama da dala dubu 60 a rana.

  5. An sanya dokar kulle a ƙananan hukumomi 145 a Valencia

    Gwamnatin yankin Valencia a gabashin Spain ta sanar da sanya dokar kulle a ƙananan hukumomi 145 bayan mummunar ambaliyar ruwa ta yi sanadin mutuwar akalla mutane biyu.

    A cewar rahoton wakiliyar harkokin duniya, Mimi Swaby, ruwan sama mai ƙarfi da guguwar Adam ta kawo ya yi barna a gabar tekun gabashin Spain, lamarin da ya tilasta wa mazauna yankin zama a cikin gidajensu.

    Bidiyoyin da aka wallafa sun nuna yadda kwararar ruwa mai ƙarfi ta riƙa kwashe motoci a tituna.

    Mahukunta sun buƙaci mutanen da ke jiran agaji da ceto da su yi haƙuri yayin da jami'an agajin gaggawa da sojoji ke ci gaba da aikin kwashe mutanen da suka makale a yankin Valencia.

    Firaministan Spain, Pedro Sánchez, ya bayyana lamarin a matsayin:

    "Yanayi mai matuƙar wahala."

    Ko da yake guguwar na raguwa, hukumomi sun shawarci mazauna yankin da su ci gaba da ɗaukar matakan kariya sosai saboda har yanzu akwai yiwuwar matakan ruwa a koguna su ci gaba da ƙaruwa.

    Haka kuma, an dakatar da karatu ga sama da ɗalibai 100,000 sakamakon matsanancin yanayin.

    Lamarin ya dawo da tunanin mummunar ambaliyar ruwa da ta auku a yankin Valencia a shekarar 2024, wadda ta yi sanadin mutuwar fiye da mutane 240, kuma ta kasance ɗaya daga cikin mafi munin bala'o'in yanayi a tarihin Spain.

  6. Masar ta ɗage muhawar neman tallafawa Saudiyya da soji

    An sake ɗage zaɓen da Majalisar Dokokin Masar za ta yi domin bai wa Shugaba Abdel Fattah al-Sisi ikon bayar da tallafin soja ga Saudi Arabia, inda aka mayar da shi zuwa ranar 26 ga Oktoba.

    An ɗage zaman ne domin ba wa dukkan 'yan majalisa damar gabatar da ra'ayoyinsu da yin muhawara kan batun kafin a kaɗa ƙuri'a.

    A ranar Asabar, Shugaba Abdel Fattah al-Sisi ya buƙaci 'yan majalisar da su amince da bai wa gwamnatin Masar damar tallafa wa Saudiyya idan ta nemi taimako wajen fuskantar hare-haren mayakan Houthi.

    Ya ce:

    "Na san cewa wannan mataki yana buƙatar amincewar majalisa, saboda haka na nemi a kira taron gaggawa domin a ba mu ikon ɗaukar mataki idan Saudiyya ta nemi hakan."

    Masar ta shiga kawancen sojin da Saudi Arabia ke jagoranta a yaƙin Yemen tun shekarar 2015. Sai dai rawar da ta taka ta fi karkata wajen kare hanyoyin jigilar kayayyaki ta Tekun Ja maimakon shiga kai tsaye a manyan hare-haren yaƙi.

    A gefe guda, wasu manyan jami'an Houthi sun gargadi Masar da kada ta shiga rikicinsu da Saudiyya. Sun yi iƙirarin cewa duk wani sa hannun Masar a yaƙin zai amfanar da Isra'ila ne a ƙarshe.

    Ko da yake ba su yi wata barazana kai tsaye ba, sun tuna da sa hannun sojin Masar a Yemen a shekarun 1960, wanda ya jawo asarar rayukan sojojin Masar da dama tare da tsadar yaƙi ga ƙasar.

  7. Kotun Koli ta Spain ta amince Carles Puigdemont ya koma ƙasar

    Kotun Koli ta Spain ta yanke hukuncin cewa tsohon shugaban yankin Catalonia, Carles Puigdemont, zai iya komawa ƙasar bayan kusan shekara goma da barinta sakamakon yunƙurin neman 'yancin kai da ya gaza a yankin.

    Mista Puigdemont ya fuskanci tuhume-tuhumen shari'a da suka shafi kuri'ar raba gardama kan 'yancin kai da aka gudanar ba tare da amincewar gwamnatin Spain ba.

    Tun bayan tserewarsa zuwa Belgium, ya ci gaba da nuna goyon baya ga ra'ayin ballewar Catalonia daga Spain, tare da sukar cibiyoyin dimokuraɗiyyar ƙasar da kakkausar murya.

    Wakilin BBC a Madrid ya ce idan Carles Puigdemont ya koma Spain, zai tarar da ƙasar ta canza sosai idan aka kwatanta da lokacin da ya tafi.

    Rahoton ya ce batun neman 'yancin kan Catalonia, wanda a da ya mamaye siyasar Spain, yanzu ya koma ƙaramin batu a siyasa yayin da ƙasar ke shirin gudanar da zaɓen gama gari na gaggawa.

    Masu sharhi na ganin cewa dawowar Puigdemont na iya zama wani muhimmin ci gaba a rikicin siyasar Catalonia, ko da yake tasirin batun ballewar yankin ya ragu sosai idan aka kwatanta da shekarun baya.

  8. Saudiyya ta soke halartar baki a taron zuba jari na "Davos of the Desert"

    Saudi Arabia ta yanke shawarar soke halartar baki da mahalarta a taronta na shekara-shekara kan zuba jari, wanda aka fi sani da "Davos of the Desert", kamar yadda majiyoyi hudu da suka san batun suka shaida wa Reuters.

    An ce an dauki matakin ne bayan munanan hare-haren da suka faru a makonnin baya-bayan nan da kuma tsanantar yaƙin ƙawancen da Saudiyya ke jagoranta da mayakan Houthi masu alaƙa da Iran.

    Jami'an Saudiyya ba su mayar da martani ga bukatar Reuters ta neman karin bayani ba.

    A cewar majiyoyin, taron Davos of the Desert, wanda aka shirya gudanarwa daga ranar 26 zuwa 29 ga Oktoba, yanzu zai gudana ne ta yanar gizo ko kuma a dage shi zuwa wani lokaci daban.

    Wannan shi ne karo na goma da ake shirya wannan babban taron zuba jari, wanda manyan mashahuran masu zuba jari da shugabannin harkokin kudi daga sassa daban-daban na duniya ke halarta.

    An samo sunan Davos of the Desert ne daga taron shekara-shekara na World Economic Forum da ake yi a birnin Davos na kasar Switzerland.

    Taron na daya daga cikin manyan hanyoyin da Saudiyya ke amfani da su wajen nuna shirye-shiryenta na jawo biliyoyin daloli na zuba jari domin aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki. Shirin ya hada da rage dogaro ga man fetur da kuma fadada zuba jari a bangarorin yawon bude ido, wasanni da fasaha.

    Bayan mayakan Houthi sun ayyana sararin samaniyar Saudiyya a matsayin yankin yaki tare da kai hare-haren makamai masu linzami kan filayen jiragen sama na kasar, an soke ko an dage ko kuma an mayar da wasu manyan tarukan siyasa, wasanni da nishadi zuwa yanar gizo.

  9. An sanya dokar hana fita da dare a wasu yankunan arewacin Faransa

    Babban jami’in gwamnatin yankin arewacin Faransa ya sanar da kakaba dokar hana fita da dare a wasu sassan biranen Lille, Douai, Denain da Wattignies.

    Waɗannan su ne matakan farko da aka sanar a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin Firaminista Sebastian Lecornu na kawo ƙarshen tashe-tashen hankula da sace-sacen dukiya da suka addabi Faransa tun daga ranar Asabar.

    Ana sa ran wasu ƙarin matakai makamantan haka za su biyo baya a sauran yankuna.

    Mista Lecornu ya ƙi ayyana dokar ta-baci a faɗin ƙasar a halin yanzu, amma ya ce gwamnati na iya ɗaukar wannan mataki idan lamarin ya zama dole.

    A gefe guda kuma, magajin garin gundumomi huɗu da ke tsakiyar Paris, waɗanda suka kasance wuraren da aka fi samun arangama tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zanga, ya yi kira da a tura sojoji domin dawo da doka da oda.

    A yau ma, ƙananan ƙungiyoyin masu zanga-zanga sun sake taruwa a dandalin Place de la République, wanda ya kasance ɗaya daga cikin wuraren da aka yi mummunar arangama a ranakun Asabar da Lahadi.

    Masu shirya zanga-zangar da aka gudanar a ranar Asabar domin nuna adawa da tsadar rayuwa sun kuma sanar da shirin sake gudanar da wata zanga-zangar a ƙarshen mako mai zuwa.

  10. Kotun Kenya ta samu shugaban ƙungiyar addini Paul Mackenzie da laifin kashe yara 190

    Wata kotu a ƙasar Kenya ta sami shugaban wata ƙungiyar addini mai tsattsauran ra'ayi, Paul Mackenzie, da wasu mutum 28 da ake zargi tare da shi da laifin kashe yara 190 da kuma mutum guda ɗaya babba.

    Wadannan kashe-kashen sun faru ne a dajin Shakahola, inda aka gano sama da gawarwaki 400 a cikin kaburbura na bai ɗaya.

    Bincike ya nuna cewa mafi yawan waɗanda suka mutu sun rasa rayukansu ne sakamakon yunwa mai tsanani bayan an umarce su da yin azumi, yayin da aka gano cewa wasu kuma an shake su har suka mutu.

    Kotun ta yi watsi da hujjar masu kare waɗanda ake tuhuma cewa mutanen sun mutu ne sakamakon azumin da suka yi da son ransu.

    An shirya yanke hukunci kan waɗanda aka samu da laifin a ranar 6 ga Nuwamba.

    Alƙalin kotun ya karanta hukuncin da ya kunshi kusan shafuka 1,000, lamarin da ya ɗauki kusan sa'o'i tara ana yi a gaban ɗakin kotu da ya cika da jama'a a birnin Mombasa da ke gabar tekun Kenya.

    Lamarin na Shakahola ya kasance ɗaya daga cikin manyan bala'o'in da suka shafi wata ƙungiyar addini a tarihin Kenya, kuma ya jawo hankalin duniya baki ɗaya saboda yawan mutanen da suka rasa rayukansu.

  11. 'Yan sandan tarzoma a Albania sun tarwatsa masu zanga-zangar adawa da gwamnati

    'Yan sandan tarzoma a Albania sun yi amfani da motocin fesa ruwa da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zangar adawa da gwamnati a harabar Ma’aikatar Ilimi da kuma Kotun Ƙoli ta Ƙara a babban birnin ƙasar, Tirana.

    Daga bisani, 'yan sanda sun sake fuskantar dandazon masu zanga-zanga, mafi yawansu ɗalibai ne, a wani babban wurin shakatawa da ke tsakiyar birnin, yayin da zanga-zangar ta shiga rana ta bakwai a jere.

    Masu zanga-zangar na neman Firaministan ƙasar, Edi Rama, ya yi murabus daga mukaminsa.

    Sai dai Mista Rama ya yi watsi da wannan buƙata, yana mai jaddada cewa ba zai sauka daga mulki ba.

    Ya kuma ce "Da zarar ƙasa ta fara tattaunawa da masu tayar da tarzoma da amfani da tashin hankali, to ƙasar ta faɗi."

    Wannan rikici na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun manyan zanga-zangar adawa da gwamnati a sassa daban-daban na Albania, inda masu zanga-zanga ke matsa lamba ga gwamnati kan batutuwan siyasa da tattalin arziki.

  12. Hari a Shabwa ya kashe mutum 50, ya jikkata 200 - AFP

    Fiye da mutum 50 ne suka mutu, yayin da akalla mutum 200 suka jikkata bayan makamai masu linzami na ballistic guda uku suka afka wa wani sansanin soji a lardin Shabwa na ƙasar Yemen, kamar yadda wasu majiyoyin soji biyu suka shaida wa AFP.

    Sa'a guda kafin wannan rahoto, kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa adadin waɗanda suka mutu ya kai mutum 18, yana mai ambaton majiyoyin gwamnati da na asibitoci guda hudu.

    A cewar waɗannan majiyoyin, mayakan Houthi ne suka kai harin kan sansanin Alam da ke lardin Shabwa.

    Mai magana da yawun rundunar sojin Yemen, Majid Nazili, ya wallafa a shafinsa na X cewa:

    "Mayakan Houthi sun kai hari kan wuraren tsaro a Shabwa da makamai masu linzami guda uku."

    Ya bayyana cewa harin ya afkawa cibiyar horas da jami'an tsaro da 'yan sanda.

    Wata majiyar soji ta gwamnatin Yemen a Shabwa ta kuma ce mayakan Houthi sun rufe hanyar da ke haɗa lardin Shabwa da lardin Bayda, wanda ke ƙarƙashin ikon Houthi, a ranar Lahadi.

    Tun da farko, mayakan Houthi sun harba makamai masu linzami guda biyar zuwa Fadar Al-Maashiq, wadda suka yi ikirarin cewa cibiyar gudanar da ayyukan rundunar kawancen da Saudi Arabia ke jagoranta ce.

    Wannan harin na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin Yemen ke ci gaba da tsananta, tare da ƙaruwa hare-hare tsakanin bangarorin da ke rikici a ƙasar.

  13. Qazvin ta ce ta kama mutane 39 da ke da alaƙa da zanga-zangar Janairu

    Hukumar Leken Asiri ta lardin Qazvin ta sanar da kama mutane 39 bisa zargin lalata dukiyoyin jama'a, ƙona gidaje da kuma wawashe gine-ginen gwamnati a lokacin zanga-zangar da ta faru a watan Janairun shekarar da ta gabata.

    A cikin sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce an gano tare da kama mutanen ne a matsayin "ƙungiyoyi takwas masu tsari."

    Sanarwar ta zargi waɗanda aka kama da lalata da ƙona gidajen jama'a, ƙona manyan shaguna a faɗin birane, lalata bankuna, ƙona motocin gwamnati da na masu zaman kansu, wawashe shagunan jama'a, kwashe kayayyaki daga ofisoshin gwamnati da kantuna.

    A cewar sanarwar, mutane 10 daga cikin waɗanda ake zargin sun yi arangama da jami'an tsaro yayin da suke ƙoƙarin banka wa gidan mai da ke titin Shahid Babaei wuta, lamarin da ya yi sanadin mutuwar wasu daga cikinsu.

    Hukumar leken asirin ta Qazvin ta kuma ce an gano makamai tare da barasa a hannun wasu daga cikin waɗanda aka kama yayin samamen da aka kai.

    A ranar Asabar da ta gabata, Hukumar Leken Asiri ta lardin Ilam ita ma ta sanar da kama mutane 11 a gundumar Malekshahi kan irin waɗannan zarge-zarge.

    Gwamnatin Iran na siffanta waɗannan zanga-zangar a matsayin wani yunƙurin "juyin mulki". A watannin baya-bayan nan kuma, ta zartar da hukuncin kisa kan wasu mutane da aka samu da laifi dangane da wannan zanga-zanga.

  14. 'Rasha ba za ta yi watsi da haɗin gwiwa da Iran ba'

    Bayan jawabin Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araqchi, Ministan Harkokin Wajen Rasha, Sergei Lavrov, ya ce yana goyon bayan batutuwan da takwaransa na Iran ya gabatar, yana mai bayyana tattaunawar da suka yi a matsayin mai amfani kuma mai armashi.

    Mista Lavrov ya jaddada cewa haɗin gwiwar dabarun siyasa da tattalin arziki tsakanin Iran da Rasha na ci gaba da ƙaruwa.

    Ya kuma ce Rasha ta miƙa tayin taimakon abinci da kayan agajin lafiya ga Iran, tare da bayyana cewa shugaban Iran, Masoud Pezhikian, zai halarci taron ƙasashen masu samar da iskar gas da za a gudanar a Moscow.

    Ministan harkokin wajen na Rasha ya ƙara da cewa ƙasarsa tana da cikakken ƙuduri wajen aiwatar da yarjejeniyar haɗin gwiwar dabarun da ke tsakanin ƙasashen biyu.

    A cewarsa "Moscow ba za ta taɓa yin watsi da haɗin gwiwarta da Iran ba."

    Kalaman Lavrov na nuna ci gaba da ƙarfafa dangantakar da ke tsakanin Rasha da Iran, musamman a fannonin siyasa, makamashi, kasuwanci da haɗin gwiwar dabarun tsaro.

  15. Ma'aikatar Harkokin Wajen Jamus ta gayyaci jakadan Iran

    Ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta sanar da cewa ta gayyaci jakadan Iran domin neman ƙarin bayani kan wani batu da ya shafi tsaro.

    Matakin ya biyo bayan hukuncin da wata kotu ta yanke kan wasu maza biyu da aka samu da laifin shirya makircin kashe shugaban wata ƙungiyar Yahudawa a Jamus.

    A cewar kotun, ɗaya daga cikin mutanen biyu ya aikata laifin ne bisa umarnin hukumar leƙen asirin Iran.

    Bayan an bayyana tuhume-tuhumen da ake yi wa mutanen biyu, ofishin jakadancin Iran da ke Berlin ya fitar da sanarwa inda ya ƙi amincewa da zarge-zargen.

    Sanarwar ta ce "Yi wa Iran manyan zarge-zarge bisa ga umarnin maƙiyan Iran, tare da maimaita zarge-zargen da ba su da hujja da kuma ra'ayoyin son zuciya, ba ya haifar da komai face rage amincewa da mutuncin hukumomin shari'ar ɓangaren da ke yin zargin."

    Iran ta musanta duk wata alaƙa da shirin kisan da ake magana a kai, tana mai cewa zarge-zargen ba su da tushe balle makama kuma suna dogara ne da bayanan da ba su da tabbas. Jamus kuwa na ci gaba da bin lamarin ta hanyoyin diflomasiyya da na shari'a.

  16. An daƙile harin da aka kai kan cibiyoyin iskar gas na Qatar

    Mashawarcin Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya ce babbar hanyar dakile hare-hare ita ce tabbatar da cewa idan aka kai hari kan tashoshin wutar lantarki da masana'antun sinadarai na Iran, to Iran ma za ta kai hari kan irin waɗannan cibiyoyi a ƙasashe tara.

    Ya kuma kare harin da aka kai kan cibiyar samar da iskar gas da ke Ras Laffan a Qatar yayin yaƙin kwanaki 40, yana mai cewa harin ya “jefa duniya gaba ɗaya cikin matsala.”

    Qatar ta nuna matuƙar rashin jin daɗinta tare da yin kakkausar suka ga harin.

    A cewarsa, bayan harin da aka kai kan cibiyoyin makamashin Iran a South Pars, Iran ta mayar da martani ta hanyar kai hari kan wata babbar cibiyar fitar da iskar gas ta Qatar.

    Baya ga haifar da tashin farashi, harin ya kuma tayar da damuwa game da wadatar makamashi a duniya.

    A wani ɓangare na jawabinsa, Mista Mokhbar ya ce “Wasu na ganin cewa ya kamata a yi watsi da mashigar ruwa ta Hormuz domin a kare sauran sassan ƙasar.”

    Wannan kalami na nuni da muhimmancin Mashigar Hormuz, wadda take ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin jigilar mai da iskar gas a duniya, kuma duk wata barazana ga mashigar na iya yin tasiri mai girma ga kasuwannin makamashi na duniya.

  17. Matawalle ya dawo da ƴanmajalisar Zamfara 8 da suka bar APC

    Ƴanmajalisar dokokin jihar Zamfara takwas da suka fice daga APC a kwanakin bayan sun sake komawa jam'iyyar bayan ganawarsu da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

    Tsohon gwamnan Zamfara kuma Ministan Tsaro na Ƙasa, Bello Matawalle ne ya jagoranci tawagar ’yan majalisar zuwa ganawar, kamar yadda sanarwar da mai magana da yawun shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya wallafa a shafukansa na sada zumunta.

    A yayin ganawar, ƴan majalisar sun sake tabbatar da goyon bayansu ga Shugaba Tinubu tare da alƙawarin ci gaba da kasancewa a cikin APC, abin da suka ce na nuna ƙudirinsu na ganin jam’iyyar ta ci gaba.

    A kwanakin baya ne wata sabuwar rigima ta ɓalle, inda lamarin ya kai ga cewa wasu ƴan majalisar dokokin jihar takwas suka sanar da sauya sheka daga jam'iyyar.

    Yan majalisar sun bayyana matakin nasu ne a zaman majalisar dokokin jihar da aka gudanar a birnin Gusau, inda aka karanta wasiƙun murabus ɗinsu a hukumance.

    Wannan ba shi ne karon farko da ake fama da taƙaddamar siyasa a jihar.

    A zaɓen shekara ta 2019 wani rikicin siyasa mai muni ya turnuƙe jam'iyya mai mulki, lamarin da ya sa kotu ta rushe dukkanin zaɓaɓɓun ƴansiyasa a jihar bayan zaɓe, tare da miƙa dukkanin muƙaman ga jam'iyyar adawa.

  18. Tsohon gwamnan jihar Delta ya rasu

    Tsohon gwamnan jihar Delta, Emmanuel Uduaghan ya rasu yana da shekara 71.

    Uduaghan, wanda ya yi gwamnan jihar daga 2007 zuwa 2015, ya rasu ne yau Litinin, kamar yadda iyalansa suka bayyana.

    Toju Anire Uduaghan ne ya sanar da rasuwar tsohon gwamnan cikin wata sanarwa da ya fitar a madadin sauran iyalai.

    Iyalan sun ce rasuwar tasa rashi ne babba saboda mutum ne da ya hidimtawa al'umma a Delta da ma Najeriya.

    "Cikin alhini muke sanar da rasuwar mahaifinmu, ɗan'uwanmu, kuma kawunmu, Dakta Chief Emmanuel Eweta Uduaghan, tsohon gwamnan jihar Delta, wanda ya rasu ranar Litinin 19 ga Oktoban 2026," kamar yadda sanarwar ta bayyana.

    Iyalan mamacin sun ce mutuwar Uduaghan ta bar babban giɓi a rayuwarsu inda kuma suka bayyana shi a matsayin mutumin da tasirinsa ya zarce iya danginsa na kusa.

    Kafin zama gwamna, Uduaghan ya taɓa riƙe muƙamin kwamishinan lafiya na jihar Delta daga 1999 zuwa 2003.

    Daga baya kuma ya kasance sakataren gwamnatin jihar Delta daga 2003 zuwa 2007 inda daga nan kuma ya zama gwamna a 2007.

    Ya yi wa'adi biyu a matsayin gwamna kafin ya bar ofis a 2015.

  19. Amurka ta gargaɗi ƴanƙasarta mazauna Gabas ta Tsakiya

    Ofisoshin jakadancin Amurka da ke ƙasashen Gabas ta Tsakiya da dama sun yi kira ga ƴan ƙasar su ƙara taka-tsantsan, suna mai nuni da abin da suka bayyana a matsayin "rincaɓewar yanayin tsaro" da kuma cikas ga tafiye-tafiye.

    Sanarwar tsaron da aka fitar daga ofisoshin jakadancin Amurka da ke ƙasashen yankin Tekun Fasha, da Isra'ila da Iraki da Labanon da Jordan, ta ce:

    "Amurkawan da ke Gabas ta Tsakiya a halin yanzu su ƙara taka-tsantsan saboda rikicewar yanayin tsaro a yankin."

    "A yi la'akari da yiwuwar soke jirage, rufe sararin samaniya ga zirga-zirgar jiragen sama, da kuma samun tangarɗa ga tafiye-tafiye."

    Gargaɗin ya ce akwai yiwuwar rikicin ya yi saurin bazuwa zuwa wasu sassan yankin.

    Haka kuma an shawarci 'yan ƙasar Amurka su riƙa bibiyar bayanan jirage tare da tanadar wasu hanyoyin tafiya na madadi idan wani yanayin gaggawa ya taso.

    Sanarwar ta kuma yi nuni da hare-haren da mayaƙan Houthi na Yemen suka kai kan Saudiyya.

    Filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa na Riyadh na ci gaba da kasancewa a rufe bayan da mutane 18 suka mutu sakamakon hare-haren da Houthi suka kai.

    An sake jaddada wa 'yan ƙasar Amurka muhimmancin ci gaba da sa ido kan bayanan zirga-zirgar jirage da kuma shirya wasu tsare-tsaren madadin idan wata matsala ta taso.

    A gefe guda, a jiya mayaƙan Houthi sun yi barazanar cewa za su kammala abin da suka fara nan ba da jimawa ba, lamarin da ya fuskanci kakkausar martani da barazanar ramuwar gayya daga Iran.

  20. Faransa ta ba magaddai ikon sanya dokar hana fita

    Ministan Tsaron Faransa, Sébastien Lecornu,ya ce firaministan kasar ya bai wa shugabannin ƙananan hukumomi ikon ƙaƙaba dokar hana fita na wani lokaci a wasu sassan ƙasar domin kare rayuka da dukiyoyi.

    ya ce ministan shari'a zai yi bayani daga baya kan matakan da gwamnati ke ɗauka domin hana sake barkewar tashin hankali.

    Ya ce wani gagarumin samame na bincike zai fara a yau a birnin Paris, inda masu bincike 200 za su nazarci bidiyon rikice-rikicen da suka faru a ƙarshen mako.

    Lecornu ya ce ana sa ran wannan bincike zai taimaka wajen gano waɗanda suka haddasa tashin hankalin da kuma ɗaukar matakan doka a kansu.

    Ya kuma ce firaministan kasar ya bai wa shugabannin ƙananan hukumomi ikon kakaba dokar hana fita na wani lokaci a wasu sassan ƙasar domin kare rayuka da dukiyoyi.