Iran ta ce ta kai hari kan sansanin sojin Amurka da ke Bahrain
Rundunar juyin juya halin Iran IRGC ta ce ta kai hare-hare kan sansanin sojin Amurka da ke Bahrai.
Cikin wata sanarwa da ta fitar a safiyar rundunar ta ce ta kai hari tare da lalata na'urar radar da sojojin Amurka ke amfani da ita wajen gano hare-hare tun da wuri a ƙasar Bahrain.
Rundunar ta ce harin martani ne ga wani harin sama da Amurka ta kai a yankin Sirik na Iran.
''Wannan babban gargaɗi ne ga abokan gaba da su dakatar da matakan tsokana da suke ɗauka a sararin samaniya, da kuma yunƙurinsu na jigilar man fetur ta mashigar ruwan Hormuz ba bisa ƙa'ida ba," in ji sanarwar.
"Idan aka sake samun keta iyakokin ƙasa da kuma hare-haren wuce gona da iri, rundunar sojin saman IRGC a shirye take domin fuskantar duk wani yaƙi ba tare da iyaka ba."
Kimanin sa'a guda kafin fitar da sanarwar, kafafen yaɗa labaran Iran sun rawaito cewa an kai wani harin sama a yankin Sirik.
Daga bisani, IRGC ta tabbatar da harin, inda ta ce hasumiyar sadarwa da ke yankin, kusa da gaɓar tekun Fasha (Persian Gulf), na daga cikin wuraren da aka kai wa harin.