Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE , Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 7/11/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Asabar 7 ga watan Nuwamban 2026.

Rahoto kai-tsaye

Buhari Fagge, Haruna Kakangi

  1. An tsige shugaban Paraguay

    An tsige shugaban ƙasar Paraguay Santiago Pena sannan kuma an tsare shi a gida bayan durƙushewar wani banki ya haifar da matsalar da ta sanya sama da rabin al'ummar ƙasar sun kasa amfani da kuɗaɗensu na ajiya da ke cikin asusun banki.

    A jiya Juma'a ne aka kama Pena jim kaɗan bayan ƴan majalisar dokokin ƙasar sun tsige shi da gagarumin rinjaye, tare da goyon bayan ƴan jam'iyyarsa.

    Lamarin ya biyo bayan durƙushewar bankin Ueno Bank a farkon mako, wanda ke da alaƙa da kamfanonin da ake alaƙantawa da Peno.

    Ya yi yunƙurin ajiye mulki a ranar Alhamis. To sai dai a maimakon amincewa da ajiye mulkin nasa, sanatocin sun yanke shawarar tsige shi tare da tuhumar shi da saɓa ƙa'idar aiki, wanda hakan ke nufin an tuɓe masa kariyar da ake bai wa tsofaffin shugabannin ƙasar.

    Pena, wanda har a shekarar da ta gabata yake da hannun jari a kamfanin da ya mallaki bankin, ya musanta aikata ba-daidai ba.

    Tuhume-tuhumen da suka kai ga tsige Shugaba Pena sun yi zargin cewa ya nuna son rai wajen gudanar da ayyukan kula da kamfanoni, ya karkatar da kuɗaɗen fansho sannan yana da hannu wajen yin rufa-rufa game da wasu ayyukan babban bankin ƙasar.

  2. Barka da warhaka!

    Barka da shigowa shafin labaranmu BBC Hausa kai-tsaye, inda muke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da ƙasashe maƙwafta da kuma sauran sassan duniya.

    Kada ku manta ku je shafukanmun na Facebook, X, Instagram da YouTube domin yin tsokaci kan labaran da muke kawo muku da kuma kallon bidiyo masu ƙayatarwa.

    Ku shiga zurenmu na WhatsApp domin samun labarai da ɗumi-ɗumi sannan ku sauke manhajar BBC Hausa.