Ethiopia ta gargaɗi Eritrea kan goyon bayan ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai
Firaministan Habasha, Abiy Ahmed, ya yi gargaɗi Eritrea cewa za ta fuskanci mummunan sakamako idan ta ci gaba da goyon bayan ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai a Habasha. A wata hira da ya yi da gidan talabijin na gwamnati cikin harshen Tigrinya, ya ce Eritrea wata hanya da da maƙiyan Habasha ke amfani da ita.
Kalaman nasa na zuwa ne a lokacin da dangantakar Habasha da Eritrea ke ci gaba da tsami. Habasha na zargin Eritrea da tallafa wa ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai da kuma hannu a rikicin arewacin ƙasar, zarge-zargen da Eritrea ke musantawa.
A ranar 1 ga Oktoban 2026, Habasha ta sanar da rufe ofishin jakadancinta da ke Asmara tare da korar jami'an diflomasiyyar Eritrea 10.
Eritrea ta mayar da martani da irin wannan mataki, inda ta sanar da katse hulɗar diflomasiyya da Habasha. Hakan ya ƙara fito da girman rikicin da ke tsakanin ƙasashen biyu.
A hirarsa ta baya-bayan nan, Abiy Ahmed ya ce ƙasashen da ke mara wa Eritrea baya ba za su iya kare ta daga matakan da za su iya ɗauka ba.
Ya kuma zargi gwamnatin Eritrea da yin watsi da ci gaba da gina cibiyoyi, yana mai cewa hakan ne ya haddasa matsalolin tattalin arziki da ƙasar ke fuskanta.
Sai dai Eritrea ba ta yi martani kan waɗannan sabbin kalamai ba.