Wani jirgin dako ya nutse a mashigar Hormuz bayan taka nakiya - IRGC
Rundunar sojin ruwa ta dakarun juyin juya halin Iran (IRGC) ta ce wani jirgin dakon kaya da ta bayyana a matsayin "mai laifi" ya taka nakiya a cikin Mashigin Hormuz.
A cewar sashen hulda da jama'a na rundunar ruwan ta IRGC, jirgin na kokarin bi ta wata hanya da ba a amince da ita ba kuma mai haɗari a Mashigin Hormuz lokacin da ya taka nakiyar.
Sanarwar ta ce bayan afkuwar lamarin, jirgin ya kama da wuta nan take.
Rundunar ta IRGC ta ƙara da cewa jirgin, wanda ke ɗauke da kwantena sama da 2,500, ya nutse da safiyar yau a kudancin ruwan Mashigin Hormuz sakamakon gobarar da ta tashi a cikinsa.
Sai dai sauran hukumomi da ke sa ido kan al'amuran tsaro a Mashigar ta Hormuz ba su fitar da wani bayani ba zuwa yanzu game da wannan lamarin, ko kuma yiwuwar asarar rayukan ma'aikatan jirgin.