Arsenal ta kusan tsawaita yarjejeniyar kociya Arteta, Mikel Arteta

Asalin hoton, Getty Images
Tuni dai Mikel Arteta ya zama kocin da ya fi kowa daɗewa a ƙwallon ƙasar Ingila
Ga magoya bayan Arsenal, ba za a iya samun sanarwar hukuma da wuri fiye da yadda suke so ba, musamman ganin cewa kwantiraginsa ta yanzu saura watanni tara kacal ta ƙare.
Tun bayan naɗa shi a matkin kociyan Gunnrs a watan Disamba a 2019, Arteta ya sauya Arsenal daga ƙungiyar da ta rasa matsayinta a gasar Zakarun Turai zuwa wadda ta lashe gasar Premier League a karon farko cikin shekara 22 a kakar wasan da ta gabata.
A yanzu Arsenal ita ce babbar wadda ake ganin za ta sake lashe kofin, sannan ana ganin tana cikin waɗanda suke da ƴan wasan da za su iya lashe gasar Zakarun Turai a karon farko a tarihinta a wannan kakar.
Tuni dai kociyan ya sauya fasalin taka ledar Arsenal tana da fitattun ƴan wasa tana taka leda mai ban sha'awa kuma. Kamar Arsene Wenger da ya gabace shi, Arteta ba tare da wata shakka ba shi ne mutum mafi tasiri a ƙungiyar, musamman idan aka yi la’akari da harkokin ƙwallon ƙafar da take bugawa a kowacce.
Tasirin Arteta ya bayyana a dukkan sassan ƙungiyar - kuma mafi muhimmanci a cikin ƴan wasan ƙungiyar. Babu wani abu da ya shafi ƙungiyar da ke faruwa ko ake tsarawa ba tare da amincewarsa ba.












