Jam'iyyar hamayya ta Demokrats a Amurka, wadda ta samu gagarumar rinjaye zaɓukan tsakiyar wa'adi da aka gudanar a ƙasar ta jaddada ƙudurin kawo ƙarshen yaƙin Iran.
Chuck Schumer, wanda shi ne shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawan ƙasar kafin gagagarumar nasarar da jamiyyarsa ta samu, wanda kuma a yanzu ake sa ran zai zama shugaban masu rinjaye, ya jaddada muhimmancin kawo ƙarshen yaƙin na Iran.
''Dole ne mu ɗauki matakan kawo ƙarshen yaƙin idan har muna son cika alƙawuran da muka ɗaukar wa Amurkawa kafin wannan zaɓe'', in ji shi.
A jawabin da ya yi bayan jam'iyyarsa ta Republican ta sha kaye a zaɓukan, Shugaba Trump ya amince cewa yaƙin Iran ne ya haddasawa jam'iyyarsa faɗuwa zaɓen.
Shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilan ƙasar, Hakeem Jeffries ya ce jam’iyyar Democrats za ta mayar da hankali wajen fafutukar samar da rayuwa mai sauƙi ga Amurkawa, da kuma tabbatar da gaskiya da adalci a ayyukan hukumomin gwamnati.
Sai dai a bayanne take cewa Jeffries da Schumer za su fuskanci ƙalubale wajan aiki tare da Shugaba Donald Trump, a dan haka sai sun nemi hanyar da za ta tabbatar cewa Mista Trump bai yi amfani da ikon shugaban ƙasa wajan ƙin amincewa da manufofinsu ba.