Ƙungiyar Barcelona, na nazarin wasu sabbin hanyoyi biyu na samun karin kuɗi wajen gyaran filin wasanta na Camp Nou, ta hanyar karɓar bashi.
A ranar Asabar ɗin da ta gabata, mambobin ƙungiyar sun amince a wani babban taro da biyan ƙarin kuɗin Euro miliyan 510 ($580.02m) domin kammala ayyukan gyaran Camp Nou da kuma cike gibin kuɗin shiga.
Ƙungiyar ta Catalonia za ta raba wannan kuɗi zuwa sassa biyu daban-daban.
Wata majiya ta shaida wa Reuters ranar Alhamis cewa Euro miliyan 300 na farko za su kasance bashin kuɗin aiki ne, wanda za a tsara shi ta asusun securitisation da ke ɗaukar nauyin kuɗin gina filin.
Za a biya wannan bashin ne daga kuɗin shiga da Camp Nou zai samu nan gaba, musamman daga sabbin wuraren karɓar baƙi na VIP da ake ƙara faɗaɗa shi a filin, kuma wa'adin biyan bashin zai kai shekara 30..
Za a iya amfani da wannan kuɗin ne kawai wajen kammala ayyukan, kuma za a tabbatar da bashin ne da kuɗaɗen shiga daga filin wasa, ba tare da jinginar da kadarorin ƙungiyar ba. Majiyar ta ƙara da cewa tuni an gudanar da tattaunawa da masu saka jari, kuma Goldman Sachs ce ta kula da tattaunawar.
Goldman Sachs ta ƙi yin tsokaci kan batun, yayin da Barcelona ba ta mayar da martani ga buƙatar yin tsokaci ba.
A wani ɓangare kuma, ƙungiyar ta shirya karɓar bashin Euro miliyan 210, wanda za a tabbatar da shi ta kuɗin haƙƙin watsa shirye-shiryen talabijin da za ta samu nan gaba daga La Liga da gasar UEFA.
Za a fbiya bashin ne kan wa'adin da zai kasance shekara 10.
An ware wannan kuɗin ne musamman domin cike gibin wanda ake samu sakamakon jinkirin aikin filin, wanda ya shafi hasashen kuɗin shiga na Barcelona.
Za a raba bashin zuwa kashi biyu na Euro miliyan 105 kowanne. An riga an fitar da ɗaya daga cikin sassan a watan Yuli, yayin da ake sa ran fitar da na biyu kafin ƙarshen shekarar 2026.
Barcelona ta fara aikin gyaran Camp Nou a shekarar 2023, kuma tun da farko an shirya kammala aikin a shekarar 2026.
Sabon filin da aka gyara zai kasance da tsarin da zai rufe saman dukkan filin, yayin da a baya rufin yake rufe babban wurin zama ne kawai. Hakan zai kuma ƙara yawan kujerun filin zuwa 105,000.
A yayin babban taron Barcelona, mataimakin shugaban ƙungiyar, Ferran Olive, ya ce ba za a kammala aikin filin ba har sai kakar 2028-29.
A farkon rabin kakar 2027-28, Barcelona za ta buga wasanninta a filin Olympic na Montjuic yayin da ake kammala aikin rufin Camp Nou.
Olive ya ce ƙungiyar na tsara komawa Camp Nou a watan Janairun 2028, ko da yake akwai yiwuwar ta koma taka leda a filin tun kafin wannan lokaci.
Olive da shugaban Barcelona, Joan Laporta, sun danganta tashin kuɗin aiki da matsalolin samar da kayayyaki da jinkirin aikin da rikicin Ukraine da kuma sauye-sauyen tattalin arzikin duniya suka haifar.