Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE , Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Asabar 14/11/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Asabar 14/11/2026

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Bawage

  1. Gwamnatin Bauchi ta dakatar da sarkin Lame

    Gwamnatin jihar Bauchi ta dakatar da Sarkin Lame, Alhaji Yakubu Aliyu, kan zargin da ake yi masa da na karɓar haraji ba bisa ka'ida ba da kuma tsoma baki a harkokin filaye da kuma na haƙar ma’adanai.

    Wata sanarwa da mai bai wa gwamna Bala Muhammad shawara kan harkokin yaɗa labarai, Mukhtar Gidado, ya fitar ranar Asabar, ta ce dakatarwar ta fara aiki nan take kuma za ta ci gaba da kasancewa har zuwa lokacin da wani kwamitin bincike mai mutum 12 da aka kafa zai kammala aikinsa.

    Sanarwar ta ce an kafa kwamitin ne domin binciken sarkin kan zargin amfani da mukaminsa domin aikata ba daidai ba.

    A cewar gwamnatin, ta samu korafe-korafe da dama da kuma rahotanni daga shugabannin al’umma, masu ruwa da tsaki da kuma jami’an tsaro kan abubuwan da sarkin ke aikatawa.

    Gwamnatin ta ce korafe-korafen sun haifar da damuwa a Masarautar Lame tare da tayar da hankalin al'umma da kuma hana zaman lafiya.

    "Zarge-zargen da ake yi wa sarkin sun haɗa da saka baki a harkokin filaye, karɓar haraji ba bisa ka'ida ba da kuma katsalanda ga kamfanonin da ke haƙar ma'adinai," in ji sanarwar.

    Ta ƙara da cewa tun da farko Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Masarautun Gargajiya ta nemi Sarkin ya yi bayani kan zarge-zargen da ake yi masa, amma ya kasa kare kansa duk da cewa ya yi martani a rubuce.

    Daga bisani ne ta yanke shawarar kafa kwamitin bincike mai zaman kansa domin tabbatar da gaskiyar zarge-zargen da ake yi wa sarkin.

  2. An bai wa Remi Tinubu sarautar Jagaban Matan Zamfara

    Majalisar Sarakuna ta jihar Zamfara, ta naɗa uwargidan shugaban Najeriya, Oluremi Tinubu a matsayin Jagaban Matan Zamfara.

    An bai wa Remi sarautar ce ranar Juma'a 13 ga Nuwamba, yayin wata ziyara da ta kai jihar domin halartar gangamin mata na jam’iyyar APC na shiyyar Arewa maso Yamma, wanda aka gudanar a Gusau.

    Sanata Remi ta karɓi sarautar bayan ziyarar da ta kai wa sarakunan gargajiya a jihar.

    An yi bikin naɗin a gidan gwamnatin jihar Zamfara, a wani biki da dukkan sarakunan suka halarta.

    Mai ɗakin shugaban Najeriyar ta nuna farin ciki tare da godiya kan sarautar da aka ba ta.

  3. Sudan ta Kudu za ta gudanar da zaɓe karon farko a tarihinta

    Sudan ta Kudu ta ce za ta gudanar da zaɓen gama-gari na farko a tarihinta a watan Fabrairun shekara mai zuwa.

    Tun da farko an shirya gudanar da zaɓen a ƙarshen watan Disamba, amma hukumar zaɓen ƙasar ta ce ta sauya jadawalin.

    Sanawar na zuwa ne a daidai lokacin da Sudan ta Kudu ke shirin fara rajistar masu kaɗa ƙuri'a a faɗin ƙasar a cibiyoyi fiye da 3,000 a ranar Asabar.

    Hukumar zaɓen ba ta bayyana dalilin da ya sa aka ɗage zaɓen zuwa ranar 11 ga watan Fabrairu ba.

    An sha ɗage zaɓen sau da dama saboda saɓani tsakanin Shugaban ƙasar, Salva Kiir, da tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Riek Machar, kan yadda za a aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da ta kawo ƙarshen yaƙin basasa a shekarar 2018.

    Rikicin ya yi sanadin mutuwar mutum kusan rabin miliyan.

    Sudan ta Kudu ba ta taɓa gudanar da zaɓe ba tun bayan samun 'yancin kai a shekarar 2011.

  4. Tinubu ya nuna damuwa kan rikicin da ake samu wajen kamfe

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga 'yan siyasa da magoya bayansu da su guji tayar da rikici yayin gudanar da yaƙin neman zaɓe gabanin babban zaɓen 2027.

    Tinubu ya bayyana cewa ya kamata kamfen ɗin siyasa ya mayar da hankali kan muhimman batutuwan da za su inganta rayuwar al'umma da cigaban ƙasa.

    Tinubu ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma'a, inda ya ce bambancin jam'iyya ko manufar siyasa ba yana nufin cewa mutane su zama maƙiyan juna ba.

    Shugaban ya jaddada aniyarsa ta tabbatar da gudanar da zaɓe cikin lumana da adalci, tare da kira ga shugabannin siyasa da magoya bayansu su gudanar da harkokinsu cikin lumana.

    Ya kuma umarci hukumomin tsaro da su ɗauki matakin da ya dace kan duk wanda ya nemi ta da zaune-tsaye ko karya doka da oda.

    "Dole ne a kare dukkan jam'iyyun siyasa da 'yan takara daga wata barazana yayin gudanar da yaƙin neman zaɓe a ko'ina cikin Najeriya," in ji Tinubu.

    Ya ƙara da cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci duk wani rashin ɗa'a daga 'yan siyasa da magoya bayansu ba, inda ya umarci jami'an tsaro da su mataki mai tsauri kan ƴan bangar siyasa da ke son kawo fitina.

  5. Microsoft ya nemi afuwa kan katsewar ayyukan manhajojinsa

    Kamfanin Microsoft ya nemi afuwa kan katsewar ayyukan mahajojinsa a faɗin duniya.Kamfanin ya bayyana cewa hakan ya faru ne sakamakon aikin inganta tsarin na'urorin, ba wai kutse ne aka yi masa ba.

    A ƙasashe da dama, asibitci da kotuna da kuma harkokin sufuri duk sun shiga wani yanayi sakamakon matsalar, amma Microsoft ya ce al'amura sun fara daidaituwa a yanzu.

    Mutane sun fara bayar da rahoton samun matsala wajen amfani da mahajojin Microsoft tun daga ranar Alhamis.

    Ba a san adadin mutanen da abin ya shafa ba, amma kimanin mutum miliyan 430 ne ke amfani da manhajojin kamfanin, kuma an samu rahotannin matsaloli daga ƙasashe sama da 70.

  6. Jirage sun koma tashi a Amurka bayan sake buɗe sararin samaniyar ƙasar

    Wasu jiragen sama sun fara tashi a Amurka, bayan da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta kasa (FAA) ta sake buɗe sararin samaniyar ƙasar.

    An dakatar da zirga-zirgar jiragen sama na tsawon fiye da sa'o'i hudu — wanda shi ne lokaci mafi tsawo tun bayan hare-haren ta'addanci na ranar 11 ga watan Satumba a shekarar 2001.

    Sakataren Sufuri na Amurka, Sean Duffy, ya bayyana cewa zai dauki lokaci kafin a dawo da sufurin jiragen zuwa yadda aka saba.

    Ana shi ɓangaren, Sakataren Tsaron Cikin Gida, Markwayne Mullin, ya ce babu ko wata shaida da ke nuna cewa wani hari ne aka kawo wa ƙasar.

    Ya ce katsewar na'urorin sadarwa ne, kuma wani abu ne na daban ba hari irin na ranar 9 ga watan Satumba ba.

  7. Ɓudewa

    Masu bibiyar mu barkan mu da safiyar Asabar.

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa.

    Ku kasance da mu domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da kuma sauran sassan duniya.