An sauke Limamin masallacin unguwar Madina da ke cikin garin Bauchi daga muƙaminsa bayan da aka zarge shi da yaɗa manufofin sake zaɓar shugaban Najeriya Bola Tinubu a cikin wa'azinsa.
Rahotanni sun ce limamin mai suna Dahiru Abubakar na amfani da lokutan huɗuba bayan kammala sallolin farilla wajen bayyana ra'ayoyi da ake kallon suna goyon bayan sake zaɓen Shugaba Tinubu, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Da yake magana kan lamarin, Liman Dahiru Abubakar ya ce a wa'azinsa yana jan hankalin jama'a ne cewa Shugaba Tinubu ba shi ne silar wahalhalun tattalin arziki da matsalolin tsaro ba, yana mai cewa waɗannan ƙalubalen suna da alaƙa da abin da ya kira "alamomin ƙarshen zamani."
"Na kasance ina wa'azin mutane su daina ɗora alhakin matsalolin tsaro da ƙalubalen tattalin arziki a kan Shugaba Tinubu. Ina kuma ƙarfafa musu gwiwa su sake zaɓensa tare da ba shi wata dama a zaɓen 2027 domin ya ci gaba da manufofinsa," kamar yadda Daily Trust ta ambato sgi yana cewa.
Ya ci gaba da cewa wa'azinsa ya fi karkata ne kan tsoron Allah da kuma daina ɗora wa shugabanni laifin matsalolin tsaro, musamman Tinubu, domin Allah kaɗai ne zai iya kawo ƙarshen waɗannan matsaloli ta hanyar amsa addu'a.
"A wa'azina nakan mayar da hankali kan tsoron Allah da ayyukanmu na yau da kullum. Na kan kawo misalan matsalolin tsaro da ke faruwa a wasu ƙasashen Afirka kamar Sudan, Chadi da Mali, sannan in tambaya ko Tinubu ne ke da alhakin abin da ke faruwa a waɗannan ƙasashe."
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban kwamitin gudanarwar masallacin, Imam Abubakar Jibrin, ya ce matsalar kwamitin da limamin ba ta taƙaitu ga zargin yaɗa manufofin Tinubu kaɗai ba.
"Babbar matsalarmu da shi ita ce ba wai yaɗa manufofin Tinubu kawai yake yi ba, har ma da yadda yake tara mutane a gaban masallaci, kuma wani lokaci yakan shiga cikin masallacin ne da gangan domin tattauna harkokin siyasa."