Da ba don ni ba da yanzu an shafe Isra'ila - Trump
Shugaban Amurka Donald Trump ya kare hare-haren sojin Amurka kan Iran a wata hira da gidan talabijin na CBS, yana mai cewa sai a nan gaba ne za a gane amfanin yaƙin.
Trump ya ƙara da cewa idan Iran ta mallaki makaman nukiliya a lokacin da yake kan mulki, hakan zai kasance baƙin tarihi a gare shi.
Shugaban ya kuma ce ba ya son ƙara tsanantar rikicin yaƙi da Iran.
A cikin hirar, an kuma tambayi Trump game da kuɗaɗen da Amurka ke kashewa wajen ɗaukar nauyin ayyukan sojinta a yankin.
Sai ya amsa da cewa ƙasashen da Amurka ke karewa ne ya kamata su biya duka kuɗaɗen yaƙin da Amurka ta kashe, yana mai cewa ƙasar ba za ta wanzu ba da Amurka ba ta taimaka mata ba.
Ya ce, "In da ba don mu ba, da tuni an jima da shafe Isra'ila. Ina so in gaya muku cewa da ba don Donald Trump ba, da an gama da Isra'ila, domin fiye da shekara guda da ta gabata muka tura jiragen saman yaƙi na zamani ƙirar B-2, waɗanda suka kai hari kan dukkan cibiyoyin nukiliyar Iran uku."