Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 15/10/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar Laraba 15 ga watan Oktoban 2026

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Shugaba Tinubu
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Ƴar Arewan da ke buga wa Najeriya ƙwallo
  • waya
  • Gwamna Adeleke na Accord
  • Jihohi masu talauci
  • Buba Galadima
  • Dattijuwa

Rahoto kai-tsaye

Aisha Aliyu Jaafar da Nabeela Mukhtar Uba

  1. Amurka ta ci amanar mu - Zelensky

    zelensky

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce yana jin Amurka ta ci amanarsa, bayan da Shugaba Donald Trump ya janye takunkumin da aka kakaɓa wa man dizal na Rasha, sannan ya sanar da tsagaita kai hare-hare kan cibiyoyin makamashi, wanda ya ce Rasha ta yi watsi da shi.

    Cikin wata hira da ya yi ta talabijin da ɗan jaridar Birtaniya Piers Morgan a lokacin ziyararsa a London, Zelensky ya ce alamu na nuna cewa Kyiv ta rasa goyon bayan Amurka na dogon lokaci a yaƙin da take yi da Rasha.

    Ya kuma nuna damuwa kan yiwuwar Amurka ta ƙara taƙaita bayanan sirri da take bai wa Ukraine, abin da Donald Trump ya musanta.

  2. Assalamu Alaikum

    Masu bibiyar shafin BBC Hausa, barkanmu da safiyar yau Alhamis.

    Kamar kullum, yau ma shafin zai kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar, da yankin Gabas ta Tsakiya da ma duniya bakiɗaya.

    Za kuma ku iya leƙa shafukanmu na sada zumunta kamar Fesbuk da X da Instagram da ma Youtube domin kallon bidiyo da tafka muhawara.

    Da fatan za ku kasance tare da mu.